Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/05/2025

Taƙaitattu

  • Aƙalla mutum 50 aka kashe a wani sabon harin Isra'ila a Gaza
  • An kashe mayaƙan Boko Haram biyar bayan daƙile harinsu a Borno
  • Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin 'ƙauyawa' a jihar Kano
  • Za a samar da ƙarin kayan aiki don daƙile ƴan ta da ƙayar-baya - Janar Chris Musa
  • ISWAP ta kashe manoma 23 a jihar Borno
  • Ya kamata a gaggauta komawa kai agaji Gaza - MDD
  • Ko duniya za ta fuskanci tsadar abinci mafi muni a shekaru masu zuwa?

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo muku ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya nuna mana.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Kamfanin Orano na Faransa mai haƙo Uranium zai sayar da sashensa na Nijar

    Kamfanin Orano na Faransa mai haƙo ma'adinin Uranium ya fara yunƙurin sayar da sashensa na Nijar wanda gwamnatin sojin ƙasar ta ƙwace.

    Duk da cewa kamfanin ya maka jamhuriyar Nijar a kotu, ya ce duk da haka a shirye yake ya tattauna da duk wanda ke da sha'awar mallakar wajen haƙo ma'adinin da ke Nijar.

    Tuni kamfanoni daga sabuwar ƙawar Nijar, Rasha da China da wasu ƙasashen suka fara bayyana sha'awarsu ta mallakar kamfanin.

    Wannan na cikin alamomin da ke nuna tsamin dangantaka da ke tsakanin ƙasashen biyu na ƙara faɗaɗa ne duk da cewa ba a Nijar ɗin ba ce kaɗai aka samu haka, domin kamfanoni da dama suna fuskantar ƙalubalen ci gaba da aiki a wasu ƙasashen Afirka.

  3. Trump zai gana da shugabannin Rasha da Ukraine ta wayar tarho

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi waya da Shugaban Rasha, Vladimir Putin a ranar Litinin, sannan ya kuma kira Shugaban Ukraine, Zelensky da shugabannin ƙasashen ƙungiyar NATO daga baya.

    Trump zai yi kiran ne a ƙoƙarin da yake yi na shigewa gaba domin kawo ƙarshen yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.

    Tun farko, wakilan ƙasashen biyu sun gana a ranar Juma'a da ta gabata, wanda shi ne karo na farko tun farkon ɓarkewar yaƙin shekara uku da suka gabata, duk da cewa Rasha ba ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Amurka ta tsara.

    Sai dai duk da haka, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce lallai akwai buƙatar kowane ɓangare ya mayar da kubensa domin a samu zaman lafiya.

  4. Hamas ta ce ta fara tattaunawa da Isra'ila domin sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta

    Hamas ta tabbatar da cewa ta fara tattaunawa da Isra'ila domin tsara sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila take cigaba da kutsawa ƙasar, inda ta ce tana da burin ƙwace sassan Gaza ne.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce Isra'ila ta kashe sama da mutum 250 daga ranar Alhamis da ta gabata.

    Isra'ila na cigaba da luguden ne duk da matsin lamba da take fuskanta kan ta cire takunkumin mako goma da ta saka na hana shigar da kayan agaji Gaza, inda har Amurka ta nuna rashin jin daɗinta. Sannan Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce hanin a daidai lokacin da ake cigaba da ɓarin wuta yunƙurin kisan ƙare dangi ne.

  5. Hanyoyi uku na inganta lafiyar ƙwaƙwalwa a lokacin aikin Hajji

    Zuwa aikin Hajji wata dama ce babba ga Musulmi, kuma ibada ce da ke buƙatar cikakkiyyar lafiyar ƙwaƙwalwa.

    A kan samu wasu matsaloli da suke da alaƙa da lafiyar ƙwaƙwalwa a lokacin gudanar da ibadar.

    Wannan ya sa BBC ta gana da ƙwararren likita, wanda ya zayyana wasu hanyoyi uku da mahajjata za su iya inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu.

  6. 'Kuɗin cizo sun hana mu kwana a gidajenmu'

    A Harare, babban birnin ƙasar Zimbabwe, hukumomi na fafutikar ganin sun yaƙi ƙananan ƙwarin nan masu shan jinin ɗan'adam, wato kuɗin cizo.

    Mazauna unguwar Mbare da ke babban birnin sun shaida wa shirin BBC na Focus on Africa Podcast cewa sun gaji da rayuwar ƙawanya da kuɗaɗen cizo suka musu.

    "Yanzu ba ma iya bacci a gidajenmu, da zarar yamma ta yi za ka ji yara na ta ihu saboda kuɗin cizo sun addabe su, ba mu iya ziyaratar ƴan'uwanmu haka nan su ma ba su iya ziyartar mu, duk saboda kuɗin cizo," in ji wata mata da ke zaune a unguwar.

  7. Burkina Faso da Senegal za su ƙulla alaƙar tsaro

    Shugaban gwamnatin mulkin soji na ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traore ya gana da Firaministan Senegal, Ousmane Sonko domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa domin yaƙi da rashin tsaro da sauran abubuwan da suka shafi ƙasashen biyu.

    An gudanar da tattaunawar ce a ranar 16 ga watan Mayu a babban birnin Burkina Faso, Ouagadougou, kamar yadda kafar Burkina24 mai zaman kanta a ƙasar ta ruwaito.

    "Na zo ne domin nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa Traore da gwamnatinsa da ma mutanen ƙasar a ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ta'addanci da aka ƙaƙaba musu, sannan mu duba hanyoyin da za mu ƙulla alaƙa da haɗin gwiwar taimakon juna," in ji Sonko bayan tattaunawar.

    Firaministan ya ce rashin tsaron ba zai tsaya a Burkina Faso da Mali da Nijar kaɗai bam "babu ƙasar da za ta tsira idan ta'addancin ya cigaba da faɗaɗa a yankin Afirka ta Yamma," in ji shi.

  8. Ghana ta kama baƙin haure 2,000 a ƙoƙarinta na yaƙi da bara a ƙasar

    Hukumomi a ƙasar Ghana sun sanar da kama baƙin haure aƙalla guda 2,000 a ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ta ce tana yi domin yaƙi da barace-barace a titunan ƙasar, musamman a babban birnin ƙasar, Accra, kamar yadda kafar Joy Online mai zaman kanta a ƙasar ta ruwaito.

    "Yanzu haka suna tsare ana tantance su," in ji hukumar kula da baƙin haure ta ƙasar.

    Ta ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kama akwai ƙananan yara guda 1,332, waɗanda hukumar ta ce za a ba su kula ta musamman domin kare haƙƙinsu.

    Ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Muntaka Mubarak ya ce sun gudanar da kamen ne "domin yaƙi da barace-barace a titunan ƙasar," in ji shi, wanda ya ƙara da cewa har da baƙin haure.

    Ya ce yawancin waɗanda aka kama ɗin sun shigo Ghana ta ɓarauniyar hanya ce, "kuma suna barazana ga zaman lafiyar ƙasar."

    Ya ce yawancin waɗanda aka kama ɗin ƴan ƙasashen Togo da Burkina Faso da Najeriya ne.

  9. Abin da ake yaɗawa kan makomata a siyasa karya ce - Kwankwaso

    Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi watsi da rahotanni da ke alaƙanta cewa yana daf da komawa wata jam'iyya, da kuma batun cewa zai shiga haɗaka da wasu jam'iyyu, lamarin da ya ce ƙanzon kurege ne kawai domin ba da yawunsa ba.

    Wata sanarwa da a wallafa a shafina na X, ɗan takarar shugaban ƙasa karashin jam'iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, ya ce raɗe-raɗen ba su da tushi balle makama kuma labaran ƙarya ne kawai na siyasa.

    "Na daina yin tsokaci kan lamuran siyasa da ke faruwa a Najeriya... kuma zan ci gaba da yin haka har zuwa wani lokaci," in ji Rabiu Kwankwaso.

    Don haka ne, ya buƙaci al'umma da su amince da sakonni da suka fito daga shafukansa da kuma majiyoyi da aka yarda da su kaɗai ba daga wasu wurare na daban ba.

  10. Yadda ƙuɗin cizo suka hana mutane sakat a Zimbabwe

    A Harare, babban birnin ƙasar Zimbabwe, hukumomi na fafutikar ganin sun yaƙi ƙananan ƙwarin nan masu shan jinin ɗan'adam, wato kuɗin cizo.

    Mazauna unguwar Mbare da ke babban birnin sun shaida wa shirin BBC na Focus on Africa Podcast cewa sun gaji da rayuwar ƙawanya da kuɗaɗen cizo suka musu.

    "Yanzu ba ma iya bacci a gidajenmu, da zarar yamma ta yi za ka ji yara na ta ihu saboda kuɗin cizo sun addabe su, ba mu iya ziyaratar ƴan'uwanmu haka nan su ma ba su iya ziyartar mu, duk saboda kuɗin cizo," in ji wata mata da ke zaune a unguwar.

    Wannan dai ba shi ne karon farko da unguwar ta yi fama da annobar kuɗin cizo ba, kasancewar an samu irin hakan a shekarar da ta gabata – 2024, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

  11. Aƙalla mutum 50 aka kashe a wani sabon harin Isra'ila a Gaza

    Aƙalla mutum 50 ne aka ruwaito mutuwarsu a wasu sabbin hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai Gaza - wani abu da ke alamta kaddamar da sabon farmaki.

    Isra'ilar ta ce tana da zimmar ganin ta karya lagon ƙungiyar Hamas da kuma kuɓutar da sauran ƴan ƙasar da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    Hukumomin lafiya da kuma tsaro karkashin ikon Hamas sun ce hare-haren na Isra'ila sun hallaka mutum sama da 250 tun ranar Alhamis.

  12. An kashe mayaƙan Boko Haram biyar bayan daƙile harinsu a Borno

    Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile wani harin Boko Haram a ƙauyen Warambe na karamar hukumar Gwoza na jihar Borno, inda suka hallaka mayaƙa biyar.

    Warambe ɗaya ne daga cikin ƙauyukan da ke ɗauke da mutanen da aka sake mayarwa yankin, inda ƴan ta da ƙayar baya suka sha yin yunkurin afka wa ƙauyen.

    Shugaban maharban yankin, wanda ya tabbatarwa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, ya ce mayaƙan ƙungiyar sun yi wa ƙauyen tsinke ne da misalin karfe shida na yammacin ranar Juma'a.

    "Sai dai sun gamu da jami'an mu inda aka yi artabu har ta kai ga biyar daga cikin ƴan ƙungiyar suka kwanta dama. Mun ƙwato makamai da harsasai waɗanda ke yanzu haka ke karkashin ikon sojoji," in ji shi.

  13. Hukumar tace fina-finai ta haramta bikin 'ranar ƙauyawa' a jihar Kano

    Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da haramta bukukuwan 'ranar ƙauyawa' da ake yi a faɗin jihar, a wani mataki na ƙarfafa kyawawan ɗabi'u tsakanin al'umma da kuma bin doka.

    Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin yayin wani taron manema labarai a yau Asabar, inda ya ce an kuma dakatar da dukkan wuraren gudanar da bukukuwan wato 'event centers' har sai abin da hali ya yi.

    El-Mustapha ya ce wannan mataki da suka ɗauka wani ɓangare ne da hukumar ke yi na ƙarfafa ɗabi'u masu kyau tsakanin al'umma.

    "Wannan mataki da muka ɗauka yana cikin tsarin dokar hukumar mu wanda majalisar jiha ta yi wa garambawul da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu," in ji El-Mustapha.

    Ya ƙara da cewa dokokin sun bai wa hukumar tace finai-finai ta jihar Kano damar kula da kuma sa ido kan ayyukan da DJ (waɗanda ke saka waƙoƙi a bukukuwa) ke yi da kuma dukkan wuraren bukukuwa a faɗin jihar Kano.

    "Daga yau duk wanda ya shirya biki da sunan ranar ƙauyawa ya aikata laifi," in ji El-Mustapha.

    Ya kuma yi kira ga shugabannin al'umma da jami'an tsaro, ciki har da Hisbah da ƴan bijilanti da su haɗa-kai da hukumar domin tabbatar da cewa an bi wannan mataki na haramta bukukuwan ƙauyawa sau da kafa.

  14. Real Madrid ta tabbatar da ɗaukar Huijsen daga Bournemouth

    Real Madrid ta sanar da sayen ɗan wasan baya na ƙungiyar Bournemouth Dea Huijsen kan kuɗi fam miliyan 50.

    Ɗan wasan mai shekara 20 ya saka hannu kan kwantiragin shekara biyar, inda zai fara yi wa Madrid wasa a gasar Club World Cup da aka sake fasali.

    Dukkan ƙungiyoyin sun tabbatar da cinikin - inda Madrid ta ce ɗan wasan zai kammala komawa ƙungiyar a hukumance ranar 1 ga watan Yuni.

    Za su buga wasa na farko a gasar da Al Hilal ta Saudiyya ranar 18 ga watan Yuni.

    Huijsen dai na cikin matasan ƴan wasa da suka hasaka a Premier League a kakar wasa ta bana.

  15. ISWAP ta kashe manoma 23 a jihar Borno

    Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe wasu manoma 23 da kuma masunta a wani hari da ta kai ƙauyen Malam Karanti kusa da Baga a karamar hukumar Kukawa na jihar Borno.

    Majiyoyi sun ce mayaƙan sun tara manoman da kuma masunta ne wuri ɗaya, inda suka kashe manoman wake 23.

    An hana mazauna garin ɗaukar gawawwakin ƴan uwansu da aka kashe, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

    "Mun yi ƙoƙarin zuwa don ɗaukar gawawwakin waɗanda aka kashe tare da jami'an tsaro, sai dai mayaƙan sun hana mu yin haka. Iyalai da dama na jiran gawawwakin ƴan uwansu," in ji wani ɗan garin.

    Ƙauyen Malam Karanti matattara ne na mayaƙan ISWAP, wuri kuma da fararen hula ke noma da kamun kifi duk da irin barazanar da suke fuskanta.

  16. Tsohon shugaban Koriya ta Kudu Yoon Yeol ya ce zai bar jam'iyyarsa ta PPP

    Tsohon shugaban Koriya ta Kudu da aka kunyata, Yoon Suk Yeol, ya ce zai bar jam'iyyarsa ta PPP kafin zaɓen da aka shirya yi domin maye gurbinsa, sakamakon tsigeshi a watan da ya gabata.

    Jam'iyyarsa ta fuskanci matsin lamba kan ta kori Mista Yoon, wanda ke fuskantar tuhuma kan manyan laifuka, bayan yunkurinsa na kafa dokar sojin da ba ta yi nasara ba a Disamban bara.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Yoon ya ce zaɓen na watan gobe, wata dama ce na kawo karshen tsarin kama karya da ɗabbaka dimokradiya mai sassauci a Koriya ta Kudu.

  17. Za a samar da ƙarin kayan aiki don daƙile ƴan ta da ƙayar-baya - Janar Chris Musa

    Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa sojoji na aiki tukuru domin shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a baya-bayan nan.

    Ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin samar da ƙarin kayan aiki - musamman na sama domin ƙarfafa yaƙi da ƴan ta da ƙayar baya da ake yi.

    Janar Musa ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaban Najeriyar ya yi da manyan hafsoshin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a.

    Babban hafsan ya ƙara da cewa tuni aka sayo kayan yaƙin domin daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka zafafa kai hare-hare a ƴan watannin nan, musammman a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    "Shugaban ƙasa ya ba da umarnin abu na gaba da za a yi, da kuma haɗa-kai da sauran ƙasashe da muke makwabtaka da su saboda yanayin wurarensu ne ke ƙara rura wutar wannan lamari a ƙasar mu" in ji Janar Musa.

    Ya ce an ƙara ƙarfafa rundunoni tare da sayan makamai domin ganin an magance wannan matsalar da aka daɗe ana fama da ita.

    "Shugaban ƙasa na kuma duba yiwuwar tattaunawa da gwamnoni domin samun goyon bayansu ta hanyar tabbatar da cewa al'umma sun mori ribar dimokraɗiyya da kuma kakkaɓe ayyukan ƴan ta'adda," in ji shi.

    Babban hafsan tsaron ya alaƙanta ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya da ƙara ƙaimi da ƴan ta'dda da kuma masu ikirarin jihadi ke yi a faɗin yankin Sahel, inda ya ce abin da ya sa ƙasar ke cikin matsin lamba shi ne rashin kyawun yanayin iyakokinta.

  18. Ya kamata a gaggauta komawa kai agaji Gaza - MDD

    Shugaban hukumar agaji a Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce bai kamata a ɓata lokaci kan amincewa da kudirin da Amurka na nuna goyon-bayanta na kai kayan agaji Gaza.

    Tom Fletcher ya ce MDD na da tsarin shigar da ɗaruruwan motocin agaji da za su taimakawa Falasɗinawa da ke kange, waɗanda ƙungiyoyin ke cewa kusan rabin miliyan na al'ummar na cikin yunwa.

    "Dole mu kawo karshen wannan haukan a yanzu, saboda MDD na buƙatar tabbaci cikin gagggawa na kai ɗauki ga fararen-hula a Gaza," in ji shi.

    Sama da makonni goma kenan da Isra'ila ta hana kai agaji Gaza, bayan ta zargi Hamas da wawushe kayan agajin.

  19. Mutum tara sun mutu a harin Rasha a birnin Sumy na Ukraine

    Hukumomi a Ukraine sun ce wani jirgin Rasha mara matuki ya kai hari kan wata motar bas da ke ɗauke da fararen-hula a yankin Sumy, inda ya hallaka mutun tara.

    Akwai kuma wasu huɗu da suka jikkata.

    Harin na zuwa ne kwana guda bayan tattaunawar ƙeƙe da ƙeƙe da wakilan Rasha da Ukraine suka gudanar a birnin Santanbul na Turkiyya.

    Ƴansandan Ukraine sun kwatanta harin kan motar bas da cewa "babban laifin yaƙi ne".

    Rasha ba ta yi martani kai-tsaye ba, sai dai ta ce ta far wa wani "shingen soji" a birnin Sumy.

    A cikin wata sanarwa ƴansandan sun ce: "Sojojin Rasha sun sake kai hari kan fararen hula, abin da ya saɓa wa ƴancin ɗan'adam da kuma kaucewa dokokin ƙasa da ƙasa."

  20. Isra'ila ta fara kai sabbin hare-hare don ƙwace iko a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun ce sun soma kai sabbin hare-haren ƙwace ikon wasu yankuna a Gaza.

    Wakilin BBC ya ce Isra'ila a kai hare-hare a wurare da dama babu kakkautawa, sannan suna shirya sojoji da za su shiga Gaza domin tarwatsa Hamas da kuma sakin sauran mutanensu da ake garkuwa da su.

    Hukumomin lafiya a Gaza sun ce hare-haren da Isra'ila ke kai wa sun yi ajalin mutane sama da 250 a safiyar ranar Alhamis.

    Shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, Volker Turk ya ce hare-haren da ake kai wa haɗe da datse kai kayan agaji Gaza, ba su da maraba da yunkurin shafe al'umma daga doron ƙasa.