Jami'ai a birnin Los Angeles sun ce mummunar gobarar daji ta lalata sama da gidaje dubu 10 da wasu gine-gine suka a jihar Californian.
Kawo yanzu adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu ya kai 7, ana kuma ci gaba da neman wasu.
Brad Sherman ɗan majalisa ne mai wakiltar Carlifornia, ya bayyana halin da ake ciki, inda ya ce wannan ce gobara mafi muni a tarihin Amurka.
Ya ce babu wanda ya taɓa tsammanin lamarin zai kai haka ga kuma iska mai ƙarfin da ake fama da ita na ƙara rura wutar.
Ƙiyasin ɓarnar da wutar dajin ta yi ya
tashi sosai zuwa aƙalla dala miliyan 135.
An tura jami’an tsaro na ƙasa 400 a yankin
domin taimaka wa ƴansanda aikin, bayan da aka samu rahotanni sata ko kwashe
kayan jama’a.
Da yake magana a wani taron manema
labarai , babban jami’in ƴansanda na birnin na Los Angeles, Jim McDonnell, ya
ce abin da suka mayar da hankali yanzu a kansa shi ne kare aikata miyagun
laifuka.
Ya ce, "kare gidaje da harkokin kasuwanci a
wuraren da aka kwashe jama’a da inda babu tsaro sosai shi ne abin da muka bayar
da fifiko a kai yanzu, domin tabbatar da ganin cewa babu wanda ya yi amfani da
damar mawuyacin halin da ake ciki. Ko kaɗan
ba za a lamunta wawashe kayan jama’a ba ko wawason kaya ko ribatar
wannan bala’i."