Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Lahadi 16 ga watan Fabarairun 2025,

    Muna fatan gobe Litinin kamar kullum idan Allah Ya kai mu lafiya, za ku sake kasancewa da mu.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku yi muhawara

  2. 'Yantakarar zaɓen shugabancin gwamnatin Jamus na muhawara

    Ana gudanar da muhawarar farko da za a yaɗa a gidan talabijin a Jamus tsakanin manyan ƴan takara huɗu da za su fafata a zaɓen shugaban gwamnatin ƙasar da zai gudana nan da mako ɗaya.

    Ɗan takarar Jam'iyyar Social Democratic, Olaf Scholz, wanda shi ke kan karagar mulki zai fuskanci ƴan takara daga jam'iyyar CDU masu ra'ayin mazan jiya, da AfD mai tsattsauran ra'ayi da kuma jam'iyyar Greens.

    Wannna shi ne karon farko da AFD za ta fito da ɗan takara amma sauran jam'iyyu sun ce ba za su yi aiki tare da ita ba.

    Shugaban Jam'iyyar CDU Friedrich Merz shi ne ke kan gaba a ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a, kuma ana masa ganin mai tsattsaurar ra'ayi kan batun baƙin-haure da ke tururuwa zuwa ƙasar ta Jamus.

  3. An samu gawar sufeton 'yansanda a otal a jihar Ogun

    An samu gawar wani sufeton 'yansanda mai suna Haruna Mohammed a wani ɗaki da ke rukunin gidaje na Anthony Uzum Estate, a garin Oyeyemi, Akute, da ke ƙaramar hukumar Ifo a jihar Ogun, ta kudu maso yammacin Najeriya.

    Bayanai sun nuna cewa ɗansandan wanda yana aiki ne a caji ofis na Ishashi da ke jihar Lagos, ya je otal ɗin, Super G Royal a rukunin gidajen tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na dare, jiya Asabar.

    A lokacin da shugabar otal ɗin, Deborah Adejobi, ke kewayawa ne kamar yadda rahotanni suka ce ta ga ƙofar ɗakin ba a kulle ba da misalin 8:52 na safe, kuma tana duba ciki sai ta ga gawar mutumin, amma kuma matar da yake ɗakin tare da ita ba ta nan.

    Bayanin da 'yansanda suka tattara ya nuna cewa matar da ta tsere wadda yanzu ake nemanta, tun da farko a wannan rana da misalin ƙarfe 6:00 na safe ta je zauren da karɓar baƙi na Otal ɗin inda ta buƙaci a ba ta ruwan sha.

    Yanzu an adana gawar sufeton 'yansandan a ɗakin ajiye gawawwaki na Life Channel Mortuary da ke Olambe.

    Mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar ta Ogun Omolola Odutola, wadda ta tabbatar da labarin ta ce da farko ba a ga wata alama ta waye mutumin ba sai da aka duba jakarsa aka ga kayansa na ɗansanda, sannan bayan bincike aka tabbatar da waye.

    Jami'ar ta ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar tasa.

  4. 'Yansanda sun kashe masu satar mutane da ceto wanda aka sace a jihar Kebbi

    Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta ce ta yi nasarar kashe masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, har huɗu, waɗanda suka sace wani dattijo, Umar Bawa, mai shekara 60 a ƙauyen Gobiraje na ƙaramar hukumar Suru.

    A wata sanarwa da kakakin 'yansandan CSPNafiu Abubkar ya fitar, ya ce haɗakar jami'an tsaro ce ta bi sawun 'yanbindigar zuwa dajin Tudunfari da ke Dakin-Gari inda suka yi musayar wuta.

    Ya ce jami'an tsaron sun yi nasarar hallaka ɓarayi huɗu da kama ɗaya sannan kuma an samu kuɗin fansa naira miliyan uku da aka bai wa ɓarayin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa alokacin farmakin sun kuma yi sa'ar ƙwato makamai da dama, tare da ceto dattijon da ɓarayin suka sace, ba tare da wata illa ba.

  5. Gwamnatin Amurka na cigiyar ma'aikatan da ta sallama na nukiliya su koma aiki

    Gwmnatin Amurka na ƙoƙarin sake ɗauko hayar ma'aikatan kare cibiyoyin nukiliya da ta sallama haka kawai ranar Alhamis, bayan da aka shiga nuna damuwa cewa sallamarsu ka iya haifar da matsala ga tsaron ƙasar.

    Ma'aikatan na daga cikin ɗaruruwan jami'an ma'aikatar makamashi da gwamnatin Trump ta sallama a ƙudurinsa na rage ma'aikatan tarayya, shirin da ya fara aiwatarwa tun daga ranarsa ta farko da ya kama mulki a wannan wa'adin na biyu.

    Ma'aikatar ida ke da alhakin tsarawa da ginawa da kuma sanya ido a kan makaman nukiliyar Amurka.

    Kafofin yaɗa labarai na Amurka sun bayar da rahoton cewa an sallami ma'aikatan ɓangaren kula da nukiliyar sama da 300.

    Sai dai kakakin ma'aikatar ya musanta yawan da cewa waɗanda aka sallama ba su kai 50 ba.

    Ganin irin haɗarin da sallamar ma'aikatan ke da bisa la'akari da aikinsu na kula da tashoshin nukiliyar, tuni gwamnatin Trump ta bayar da umarnin soke korar tasu.

    Sai dai kuma ma'aikatar tasu ba ta da hanyar yadda za a iya tuntuɓar ma'aikatan saboda yanayin sirrin aikinsu, illa dai ta sanya sanarwa a kafafen yaɗa labarai ta sanar da su su koma bakin aiki.

    A makon da ya gabata kusan ma'aikatan tarayya 10,000 gwamnatin Trump ta sallama daga hukumomi daban--daban kamar yadda bayanai suka nuna.

    Wannan kuma kari ne a kan aƙalla ma'aikata 75,000 da suka amince da tayin da Fadar Gwamnatin Amurka ta yi musu na barin aiki don kansu.

  6. Matasa sun ƙona ofishin 'yansanda a jihar Ondo saboda mutuwar wani matashi

    Wasu matasa da suka fusata sun ƙona wani caji ofis na 'yansanda a garin Ifon na ƙaramar hukumar Ose da ke jihar Ondo.

    Wannan ya faru ne sakamakon mutuwar wani matashi, wanda aka yi zargin cewa 'yansanda sun gana mishi azaba a lokacin da suke tsare da shi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a jiya Asabar, amma har zuwa yau Lahadi ba a samu cikakken bayani kan lamarin ba.

    Jaridar ta ce ta samu bayanai daga garin da ke da iyaka da jihar Edo cewa mutuwar matashin ta harzuƙa abokan yaron da sauran jama'ar garin suka shiga zanga-zangar da ta kai ga ƙona ofishin 'yansandan.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka bada bayani kan lamarin ya ce lamarin ya faru ne a dalilin bikin Ranar Masoya ta Duniya da aka yi, ranar Juma'a.

    mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar Funmilayo Odunlami-Omisanya ta tabbatar da aukuwar lamarin ta kuma ce kwamishinan 'yansandan jihar na kan hanyarsa ta zuwa garin domin kwantar da hankali.

  7. Pakistan ta ayyana dokar taɓaci kan fari a Rawalpindi

    An ayyana dokarta ɓaci kan fari a birnin Rawalpindi na ƙasar Pakistan sakamakon rashin ruwan sama a yankin.

    Jami'ai a yankin sun ce ruwan sha da ake da shi a birnin ba zai wuce kwanaki 45 ba.

    Sun ƙara da cewa idan ba a samu ruwan sha a cikin watannin Fabrairu da Maris ba - waɗanda galibi lokacin rani ne a yankin - to al'ummar Rawalpindi miliyan biyu za su shiga matsanancin yanayi.

    Tuni dai hukumomin suka buƙaci mazauna birnin su adana ruwan sha - da za su yi amfani da shi yayin da yanayin ke ƙara munana.

    Masana kimiyya sun ce Pakistan na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fuskanci mummunar illar sauyin yanayi, inda ƙasar ta fuskanci mummunar ambali da kuma fari.

  8. An kashe wani limamin masallaci mai neman maza a Afirka ta Kudu

    Ana ci gaba da jimamin kisan da aka yi wa wani limamin masallaci na farko da ya bayyana kansa a matsayin mai neman maza.

    An harbe Muhsin Hendricks, babban malamain musulunci a Afirka ta Kudu a wani kwantan ɓauna da aka yi masa ranar Asabar.

    ƴan gwagwarmaya sun ce lamarin ka iya zama laifin ƙyama.

    Malamin mai shekara 59 - da ke jagorantar wani masallaci a birnin Capetown - ya jima da bayayan cewa shi ɗan luwaɗi ne.

  9. Dole a 'kawar da Hamas' idan ana son zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya - Amurka

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce dole ne a ''kawar'' da ƙungiyar Hamas, yana mai cewa wanzuwarta a matsayin gwamnati a Gabas ta Tsakiya zai kawo cikas ga zaman lafiya.

    Mista Rubio na magana ne a Birnin Kudus yayin wata ziyara da ya kai ƙasar inda ya gana da Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu.

    A lokacin ziyarar tasa zuwa yankin, Mista Rubio bai gana da shugabannin Falasɗinawa ba.

    A nasa ɓangare, Netanyahu ya yaba wa shawarar Trump na sake tsugunar da Falasɗinawa zuwa wasu wurare.

  10. Isra'ila ba ta taɓa samun babban amini a fadar White House irin Trump ba - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana takwararnsa na Amurka, Donald Trump a matsayin babban abokin da Isra'ila ba ta taɓa samun kamarsa ba a fadar White House.

    Yayin da yake jawabi bayan ganawarsa da sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, da ya kai ziyara ƙasar, Mista Netanyahu ya ce ƙasashen biyu na da matsayi iri guda a kan Gaza.

    Netanyahu ya yi gargaɗi kan abin da ya kira ''fara balbalin bala'i'' idan ba a saki duka Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su ba kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

    A baya-bayan nan ne dai shugaban Amurkan ya bayar da shawarar kwashe duk ilahirin mutanen Gaza domin mayar da su wasu ƙasashen, inda ya ce yankin zai koma ƙarƙashin ikon Amurka, bisa kulawar Isra'ila, wani abu da Isra'ilar ta yi maraba da shi.

    Shawarar dai ta fuskanci suka daga ƙasashen Larabawa da dama.

  11. Tinubu ya yaba wa El-Rufai saboda 'gina dimokraɗiyya' a Najeriya

    Shugaban anjeriya Bola Tinubu ya yaba wa tsohon gamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai kan gudunmowar da ya bayar a fannin dimoƙraɗiyyar ƙasar.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, domin taya El-Rufai munar cika shekara 65 a duniya, Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan na Kaduna da jagora, manazarci kuma ɗan siyasa.

    ''Irin gudunmowar da ya bayar wajen hidimta wa ƙasa da zama abin koyi ga ƴan baya, babban abin yabawa ne'', a cewar sanarwar.

    Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa rawar da El-Rufai ya taka wajen kafuwar jam'iyyar APC, da kuma irin gudunmowar da ya bayar wajen nasarorin jam'iyyar a zaɓukan ƙasar uku da suka gabata, 2015 da 2019 da kuam 2023.

    A shekarar 2015 ne aka zaɓi Mallam Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna, inda ya yi wa'adin mulki biyu.

    Bayan rantsar da Shugaba Tinubu a 2023 ya sanya sunan El-Rufai cikin jerin mutanen da yake son bai wa muƙaman ministoci, sai dai tsohon gwamnan bai tallake tantancewar majalisar dattawan ƙasar ba, lamarin da ya sa bai samu muƙamin ba.

    Daga nan ne kuma dangantaka ta fara tsami tsakaninsa da Tinubu, inda a baya-bayan ya riƙa fitowa fili yana sukar manufofin gwamnatin.

  12. Jirgi na uku ya kawo Indiyawan da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa'ida ba

    Wani ƙarin jirgi ɗauke da Indiyawan da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba na kan hanyarsa ta mayar da su birnin Amritsar na jihar Punjab.

    Rahotonni sun ce jirgin nan ɗauke da kusan mutum 150.

    A jiya Asabar ne wani jirgin ɗauke da ƴanciranin Indiyawa fiye da 100 - da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba - ya mayar da su ƙasar.

    A farkon wannan wata ne aka mayar da jirgin farko na Indiyawan da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa'ida ba, bayan shugaban ƙasar, Donald Trump ya sanya hannu da dokar mayar da baƙin haure ƙasashensu.

    Gwamnatin Amurka na fifita matakin mayar da baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba zuwa ƙasashensu.

    An yi ƙiyasin cewa akwai dubban Indiyawan da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa'ida ba.

  13. An zaɓin ɗan Najeriya a matsayin babban kwamishinan hukumar tsaro ta AU

    An zaɓi ɗan Najeriya, Bankole Adeoye a matsayin babban kwamishin hukumar tsaro ta tarayyar Afirka, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar.

    Ministar harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar - wanda ke halartar taron ne ya tabbatar da hakan cikin zantarwasa da BBC.

    Haka kuma ministan ya ce Najeriya ta samu shiga majalisar tsaro ta ƙungiyar Tarayyar Afirkan.

    Mista Tuggar ya ce hakan zai taimaki ƙasar a ƙoƙarin da take yi na yaƙi da matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita.

  14. Ƴantawayen M23 sun kutsa babban birnin lardin Kivu ta Arewa

    Ƴantawayen M23 sun danna cikin Bukavu, babban birnin lardin Kivu ta Arewa a gabashin DR Congo. Mayaƙan sun shiga birnin ne da asubahin ranar Lahadi riƙe da manyan makamai, inda wasu mazauna birnin ke jinjina musu.

    Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ƴantawayen ke ɗaukar hotuna a dandalin tunawa da samun ƴanci da ke tsakiyar birnin.

    Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da suka shiga yankin Bukavu.

    Ƙungiyar ta ce ta shiga birnin ne domin ƴanto shi, sannan ta yi kira ga sojojin Congo da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai masu ƙawance da sojojin a birnin su miƙa wuya.

    To sai gwamnatin Congo ta dage cewa har yanzu Bukavu na ƙarƙashin ikonta.

    Ƴantawayen na ƙabilar Tutsi da ke samun goyon bayan Rwanda sun ƙwace yankuna masu yawa a hare-haren baya-bayan nan da suka ƙaddamar.

    Lamarin da ke ƙara haifar da fargaɓar bazuwar yaƙin zuwa makwabtan ƙasashe.

    Tarayyar Afirka ta yi kiran gaggauta kawo ƙarshen yaƙin.

  15. Harin Isra'ila ya kashe ƴansandan Falasɗinawa biyu a kudancin Gaza

    Rahotonni daga Gaza na cewa wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kudancin yankin ya kashe aƙalla jami'an ƴansandan Falasdinawa biyu.

    Ƙungiyar Hamas ta bayyana harin da saɓa wa yarjejeniyar tsagita wuta.

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Hamas ta ce harin ya kuma ji wa wani ɗansandar munanan raunuka.

    Ta ƙara da cewa an aike da ƴansandan uku ne domin kula da shigar da kayan agaji zuwa gabashin Rafah.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan wasu masu ɗauke da makamai da suka tunkari ynkin da sojojinta suke.

  16. Majalisar Wakilan Najeriya ta mayar da martani kan zarge-zargen Gambaryan

    Majalisar Wakilan Najeriya ta ce iƙirarin cin hanci - da jami'in kamfanin Binance, Tigran Gambaryan ya ce wasu jami'ai a ƙasar sun buƙata daga gare shi - ba komai ba ne illa ɓata wa hukumomin ƙasar suna.

    Mista Gambaryan, ya yi zargin cewa wasu ƴan majalisar wakilan ƙasar sun nemi ya ba su cin hancin dala miliyan 150 a lokacin da aka samu wata kiki-kaka tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Binance, lamarin da ya sa hukumomin Najeriya suka tsare Mista Gambaryan.

    Cikin wata sanarwar da majalisar wakilan ta fitar, ta hannun mai magana da yawunta, Hon. Akin Rotimi,ta ce ''an yi zarge-zargen - waɗanda a shekarar da ta gabata ma an yi ta yawo da su - an yi ne domin ɓata wa wasu ƴan majalisar suna ba wai majalisar gaba ɗaya ba''.

    “Majalisa na kira ga ƴan ƙasa su yi watsi da zarge-zargen marasa tabbas da aka ƙirƙira da nufin ɓata wa hukomomi da wasu jami'an ƙasar suna'', kamar yadad sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Majalisar ta kuma wanke ƴanmajalisaun da Mista Gambaryan ya ambata cikin zarge-zargen nasa.

    “Ƴan majalisunj da aka ambata cikin zargin, sun tabbatar da jagorancin majalisa cewa babu wani abu makamancin zargin da ya auku tsakaninsu da mista Gambaryan, kamar yadda ya yi zargin''.

    Kan haka ne sanarwar ta ce ƴan majalisun za su ɗauki matakin shari'a kan Mista Gambaryan.

    ''Ɗaya daga ciki ma tuni ya shigar da ƙara kotu domin wanke kansa, yayin da aka ƙarfafa wa sauran biyun gwiwa su ma su yi hakan,'' in ji sanarwar.

    A kwanakin baya ne aka gurfanar da Gambaryan- ɗan Amurka - a kotun Najeriya bisa zargin laifukan kuɗi.

    To sai dai hukumomin Najeriya sun sake shi ne bayan shiga tsakani da gwamnatin Amurka ta yi.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a baya-bayan nan, Gambaryan ya yi ikirarin cewa kama shi da gwamnatin Najeriya ta yi ba bisa ƙa'ida ba ya sa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya kauce wa ganawar da ya shirya yi da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 (UNGA).

    Ya kuma zargi mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu kan lamarin, sannan ya ce gwamnatin Amurka ta rage yawan wakilan Najeriya da suka halarci taron na MDD.

    Tuni dai gwamnatin ƙasar ta mayar masa ta martani kan zarge-zargen, tana mai cewa ba su da tushe balle makama, tana mai bayyana su da tsantar ƙarya da ya shirya kuma da gangan.

  17. Adadin mutanen da suka mutu a turmutsitsin tashar jirgin Indiya ya kai 18

    Adadin mutanen da suka mutu a tattake mutanen da aka yi a tashar jirgin ƙasa ta birnin Delhi na Indiya ya kai 18.

    Ƴansanda sun fara gudanar da bincike, inda za su duba hotuna da bidiyon kyamarorin tsaro na CCTV domin gano ainahin abin da ya faru.

    Wani mutum da abin ya auku a kan idonsa ya ce mutanen sun cika a tashar ne bayan da aka soke tashin wasu jirage biyu.

    Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Asabar, lokacin da masu ibada suka taru domin hawa jirgin ƙasa zuwa Prayagraj a Uttar Pradesh, inda mabiya addinin Hindu ke gudanar da bikin ibada na Kumbh Mela.

  18. Shugabannin Turai na shirin gudanar da taron gaggawa kan Ukraine

    Tarayyar Turai ta gayyaci shugabannin ƙasasshen nahiyar zuwa birnin Paris a gobe Litinin, domin taron gaggawa kan yaƙin Ukraine.

    Hakan tamkar wani martani ne kan yadda Amurka ta ƙi sanya ƙasashen yankin cikin tattaunawar kawo ƙarshen yakin.

    Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer - wanda shi ma zai halarci taron na Faransa - ya kira shi da irin sa na farko cikin shekaru masu yawa.

    Mista Starmer na son ganin ya yi amfani da muƙaminsa wajen daidaita Turai da Amurka, domin zama tsintsiya guda kan kawo ƙarshen yaƙin na Ukraine.

    A ƙarshen watan nan ne ake sa ran zai kai wa shugaba Trump ziyara a birnin Washington.

  19. Mutum 48 sun mutu bayan ruftawar mahaƙar ma'adinai a Mali

    Aƙalla mutum 48 ne suka mutu sakamakon ruftawar wata mahaƙar ma'adinai da ake haƙa ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar Mal.

    Yawancin waɗanda suka mutu mata ne goye da 'ya'yansu a baya.

    Lamarin ya faru ne a kusa da yammacin Kenieba da ke yankin Keyes - yankin da ke cike da wuraren haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

    Akwai rahotonnin da ke cewa wasu ƴan ƙasar China ne ke jagorantar haƙar ma'adinan ba bisa ƙa'ida ba.

    Bisa yarjewar gwamnatin Mali, Beijing ta zuba maƙudan kuɗi domin inganta masana'antun haƙar ma'adinai a ƙasar.

    Sai dai sakomakon rashin dokokin da ke tafiyar da harkar, gwamnatin Mali ta fito da wani tsari, inda ta buƙaci duka kamfanonin ƙasashen waje su ba ta hannun jari a kamfanonin nasu.

    Ruftawar mahaƙar ma'adinai ba baƙon al'amari ba ne a Mali, ko a shekarar da ta gabata ma kusan mutum 70 ne suka mutu a wannan yankin sakamkon ruftawar wata mahaƙa.

    Haka ma a watan da ya gabata, mutum 10 sun mutu da dama suka jikkata, a wata mahakar.

  20. Maraba lale

    Masu bin wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Sannunmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku ci gaba da bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta domin tafkqa muhawara kan labaran da muke wallafawa.