Chelsea za ta biya fam miliyan 83 kan ɗan wasan Barca, ƙungiyoyin Saudiyya na harin Diaz

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan Ingila da Manchester United, Marcus Rashford, mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Aston Villa, na da ƙwarin gwiwar cimma fatansa na komawa Barcelona nan ba da jimawa ba, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.

Atletico Madrid na son dan wasan Faransa da Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekara 27, wanda aka yi wa farashin fam miliyan 42, in ji majiyar Fichajes.

Manchester City na son maye gurbin Kevin de Bruyne da dan wasan tsakiyar Belgium mai taka leda a Atalanta, Charles de Ketelaere, a cewar mujallar TBR Football.

Chelsea za ta amince da biyan fam miliyan 83 kan ɗan wasan bayan Faransa da ke taka leda a Barcelona Jules Kounde, sai dai kulub din na Sifaniya ba ya son sayar da ɗan wasan mai shekara 26, kuma yana shirin bai wa ɗan wasan sabon kwantiragi kamar yadda jaridar Diario Sport ta ambato.

Ajax na fatan ɗaukar ɗan wasan Ghana da Brighton, Tariq Lamptey, mai shekara 23, suna kuma son ɗauko mai tsaron gida Joel Veltman, mai shekara 33 idan kwantiraginsa ya kare a lokacin bazara a cewar jaridar Mirror.

Arsenal na tuntuɓar Atalanta kan yiwuwar ɗauko ɗan wasa, Mateo Retegui, sai dai Gunners kan iya fuskantar cikas kan ɗan Italiyan, mai shekara 25, in ji majiyar CaughtOffside.

Liverpool na son ɗan wasan Netherland da Tottenham, Micky Van de Van mai shekara 23, a wannan bazarar, cewar mujallar wasanni ta Football Insider.

Daga Saudiyya kuma Al-Nassr da Al-Hilal na son dan wasan gaban Colombia mai taka leda a Liverpool, Luis Diaz, mai shekara 28, sai dai hankalin dan wasan na kan Barcelona, kamar yadda majiyar Todofichajes ta ruwaito.

Manchester United na shirin rage kuɗin da take kashewa, a wani ɓangare na tanadin kuɗin ritayar 'yan wasa da ma'aikata a cewar jaridan Guardian.