Ana zargin tsoffin shugabannin sojin Birtaniya da ɓoye shaidar aikata laifukan yaƙin a Afghanistan
Ana zargin tsoffin shugabannin rundunar sojin Birtaniya ta musamman biyu da ɓoye shaidar aikata laifukan yaƙi.
An gabatar da zargin ne a gaban wata kotun sauraron ƙararraki da suka shafi zarge-zargen haramtaccen kisan da rundunar ta musamman ta yi a Afghanistan.
Wani rahoto da shirin BBC na Panorama ya yi akan zargin aikata laifukan yaƙi a Afghanistan ya janyo wannan tuhuma.
Wani babban jami'i wanda ba a bayyana sunansa ba na ɗaya daga cikin manyan jami'an rundunar kuma ya shaida wa kotun cewa ya yi matukar shiga damuwa akan abin da ya ce zargin kisan babu gaira babu dalili da aka yi wa mutanen da basu ji basu gani ba ciki har da yara.
Ya ce tsoffin shugabannin rundunar sun san da zarge zargen amma basu yi komai akai ba.