Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Birtaniya da China sun amince da daƙile ƙaruwar tashin hankali a duniya

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce shi da takwaransa na Japan Sanae Takaichi sun amince da buƙatar mayar da martani game da ƙaruwar tashe-tashen hankula a duniya.

    Yayin da ya kai ziyara Japan, Sir Keir ya ce alaƙar da ke tsakanin ƙasashen ita ce mafi ƙarfi da ta kasance cikin shekaru da dama.

    Ƙasashen Japan da Biritaniya, na daga cikin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.

    A baya-ban nan sun ƙara haɗa kai don bunƙasa tattalin arziki da tsaro bayan ziyarar kwanaki uku da firaministan Birtaniya ya kai China.

  2. Shettima ya karɓi gwamnan Taraba a APC

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shetiima ya wakilci Shugaban ƙasar Bola Tinubu wajen karɓar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas da magoya bayansa zuwa jam'iyyar APC a hukumance.

    An gudana da bikin karɓar gwamnan ranar Asabar a birnin Jalingo fadar gwamnatin jihar.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron, mataimakin shugaban ƙasar ya ce jihar Taraba da ɗaya daga cikin jihohi mafiya muhimmanci a fanni samar da abinci da makamashi da kuma tsaro ga Najeriya.

    Shettima ya ce Shugaba Tinubu na sanar wa gwamnan cewa yana da matsayi ba iya a cikin jam'iyyar APC ba, har fannin ciyar da jihar gaba.

    “Abin da ya bambanta jam'iyarmu da saura shi ne mu, mun yi imanin ƙasarmu za ta ci gaba da wanzuwa ne idan muka fahimci ƙarfinmu da yadda za mu taimaka, kuma mun tabbata jihar Taraba na ɗaya daga cikin ƙarfin ƙasarmu'', in ji mataimakin shugaban ƙasar.

    ''Jiha ce da ke ciyar da ƙasarmu, sannan take da makamashin da ƙasarmu ke buƙata, kuma take ciyar da ƙarsarmu gaba'', in ji shi.

    A ƙarshen shekarar da ta gabata ne gwamnan na Taraba ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC bayan ficewa daga PDP tare da duka kwamishinoninsa.

  3. Qatar da Masar sun yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a Gaza

    Ƙasashen Qatar da Masar sun yi Allah wadai kan abin da suka kira saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta yi ta hanyar ƙaddamar da hare-hare ta sama tare da kashe aƙalla mutum 30 a yankin Falasɗinawa.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin sada zumunta, Qatar ta ce hare-haren na da hatsarin sake tayar da rikicin.

    Hukumar tsaron fararen hula a Gaza - da Hamas ke jagoranta - ta ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu na zaune a wani sansanin ƴangudun hijira da ke kudancin Khan Younis, sannan aka kashe wasu biyar a wani gida a Birnin Gaza.

    Hukumar ta ce an kashe mutum 12 a cibiyar ƴansandan Hamas.

    Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan kwamandojin Hamas da gine-ginen ƙungiyar da na ƙungiyar Islamic Jihad da suka saɓa wa yarjejeniyar.

    Yarjejeniyar zaman lafiyar da Amurka ta gabatar ta kuma fara aiki a watan Oktoban da ya gabata, ta shiga zagaye na biyu tun bayan da aka mayar da mutum na ƙarshe da ake garkuwa da shi a Gaza zuwa Isra'ila.

  4. Amurka ta shirya sayar wa Saudiyya da Isra'ila manyan makamai

    Amurka ta amince da yarjejeniyar sayar da makamai na biliyoyin daloli ga Isra'ila da Saudiyya, a daidai lokacin da ake takun saƙa tsakaninta da Iran.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Isra'ila za ta sayi jirage masu saukar ungulu nau'in Apache guda 30 da motocin yaƙi masu sulke waɗanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan huɗu.

    Har ila yau, ta amince da sayar wa Saudiyya makamai masu linzami nau'in Patriot sama da 700 kan kuɗi dala biliyan tara.

    Ana dai zaman ɗar ɗar a yankin Gabas ta Tsakiya inda Amurka ta jibge dakaru masu yawa da kayan yaƙi a tekun da ke kusa da Iran.

  5. Matan da aka ci zarafinsu a badaƙalar Epstein sun koka kan fitar da sunayensu

    Matan da Jeffrey Epstein ya riƙa kawalcinsu don haɗa su da manyan maza, sun koka dangane da bayana sunayensu da aka yi cikin sabbin bayanan da aka fitar ranar Juma'a.

    Matan sun ce matakin zai sake jefa su cikin tashin hankali da tsangwama yayin da aka ci gaba da ɓoye sunayen mazan da suka ci zarafinsu.

    Lauyar da ke akiltan matan fiye da 20, Gloria Allred ta ce duk da an ja layi kan wasu sunayen, amma za a iya karanta su.

    A ranar Juma'a ne ma'aikatar shari'ar Amurka ta wallafa bayanan da suka ƙunshi shafuka miliyan uku da bidiyoyi da hotuna na badaƙalar.

  6. Amurka ta fara yunƙurin daidaita alakarta da ƙasashen Sahel

    Ofishin kula da harkokin Afirka na Amurka ya ce babban jami'insa Nick Checker na kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Mali domin ƙoƙarin daidaita alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    A cikin abin da ya bayyana a matsayin sanarwar sasantawa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ofishin ya bayyana sha'awar Washington na magance 'rashin fahimta' da aka samu a baya da niyyar inganta dagantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "Amurka na fatan tattaunawa kan matakai na gaba don inganta haɗin gwiwar Amurka da Mali da kuma tuntuɓar wasu gwamnatocin yankin, ciki har da Burkina Faso da Nijar, kan samun daidaito a batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki."

    Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ɓaraka a dangantakar da ke tsakanin ƙasashen yankin Sahel da ƙawayensu na yammacin duniya, musamman bayan wasu juyin mulkin da aka yi a ƙasashen.

    Dangantakar ta ƙara tsami ne a lokacin da gwamnatocin mulkin sojan ƙasashen suka umurci sojojin ƙasashen yammacin duniya da suka hada da sojojin Amurka da na Faransa da su fice daga yankin Sahel duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yaƙi da ta'addanci a yankin.

    Tuni dai suka ƙula alaƙa ta ƙut da ƙut da Rasha domin neman agajin soji da tsaro, lamarin da ya haifar da jibge sojojin haya da kuma kayan yaƙin rasha a yankin.

  7. An samu rahotonnin fashewa a kudancin Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce mutum guda ya mutu yayin da wasu suka jikkata bayan wata fashewa ta auku a wani gini da birnin Bandar Abbas mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin ƙasar.

    Ba a dai bayyana dalilin fashewar ba, amma wasu saƙonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta a ƙasar sun ce an kai hari ne kan kwamandan sojin ruwa na rundunar dakarun juyin juya halin ƙasar.

    Kodayake wata majiya a kamfanin dillancin labaran ƙasar ta musanta iƙirarin.

    Bidiyon da aka ɗauka a wurin fashewar ya nuna yadda aƙalla hawa biyu na ginin ya yi matuƙar lalacewa.

    A wani labarin na daban kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ta ce mutum huɗu ne suka mutu a wata fashewar a birnin Ahvaz.

    Sai dai wata majiyar hukumomin ƙasar ta ce duka fashewar biyu sun faru sakamakon fashewar tukunyar gas.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Amurka, kan zargin kashe masu zanga-zanga, Inda rahotonni ke ambato Trump na duba yiwuwar ɗaukar matakai kai Iran har da kai hari ƙasar.

  8. Ƴan aware sun kai hare-hare a wasu yankunan Pakistan

    An samu rahotannin wasu jerin hare-haren haɗin gwiwa na ƴan aware a lardin Balochistan na ƙasar Pakistan.

    An ji tashin bama-bamai da ƙarar harbe-harbe a garuruwa da dama da suka haɗa da Quetta inda aka rufe muhimman gine-ginen gwamnati.

    Gwamnatin lardin ta ce ta yi nasarar daƙile hare-haren - amma aƙalla jami'an tsaro goma ne suka rasa rayukansu - yayin da wasu rahotanni ke nuna cewa adadin ya zarta haka.

    An kafa dokar ta baci a yankunan da hare-haren suka shafa.

    Ƙungiyar ƴan aware ta Balochistan Liberation ta dauki alhakin kai hare-haren.

  9. Wata mahaukaciyar guguwa ta dumfari ƙasar Madagascar

    Hukumar kula da yanayi ta ƙasar Madagascar ta fitar da sanarwar gargaɗi a yankunan da ke arewa maso yammacin ƙasar da ke cikin haɗari daga wata guguwa mai ƙarfin gaske.

    Ta ce guguwar mai suna Fytia, tana gudun da ya kai kilomita 150 a cikin sa'a guda.

    Hukumar ta yi gargadin samun ruwan sama mai ƙarfi da zai haifar da ambaliya da zaftarewar ƙasa da kuma toshe hanyoyi.

    Madagascar dai na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma ta na fuskantar barazana daga bala'o'i da ke da alaƙa da yanayi.

  10. Hare-haren isra'ila sun kashe aƙalla mutum 19 a Gaza

    Akalla Falasdinawa 19 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a cewar ma’aikatan lafiya da jami’an ma’aikatar lafiya.

    Ma'aikatar da ke aiki a ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas ta ce mutane da dama kuma sun jikkata.

    Mazauna Gaza sun bayyana waɗannan hare-hare a matsayin mafi muni tun bayan da Donald Trump ya sanar da zango na biyu na tsagaita wuta.

    An kai hari kan rukunin gidaje da ofishin ƴan sanda na Hamas a birnin Gaza , kuma cikin waɗanda suka mutu har da fursunoni da jami'an ƴan sanda da ƙananan yara.

    An kuma samu rahoton cewa an kashe wasu mutane bakwai ƴan gida ɗaya a kudancin yankin a lokacin da wani jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan tantin da suke fakewa a ciki.

    Wani mutum ya ce ji ya ke kamar yaƙi ya sake dawowa zirin Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazarin rahotannin amma ba ta tabbatar da cewa ta kai wani hari ba.

  11. Sojojin Najeriya sun kashe manyan mayaƙan ISWAP

    Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Haɗin Kai da ke aiki a yankin arewa maso gabshin Najeriya, sun sanar da nasarar kai wasu munanan hare-hare kan ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke addabar yankin.

    A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar, ya ce bayanan sirri sun tabbatar da kashe wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP mai suna Julaibib a yankin Gujba.

    A cewarsa, an yi nasarar kashe shugaban mayaƙan na ISWAP ne bayan wanii artabu da aka yi tsakanin mayaƙan da dakarun soji a kusa da garin Kimba da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, a ranar 30 ga watan Janairu.

    "Wannan ci gaba mai mahimmanci ya kasance babban illa ga tsarin ƙungiyar ISWAP a yankin," in ji sanarwar.

    Laftanar kanar Uba ya kuma sanar da cewa rundunar ta yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga uku bayan wani harin kwanton ɓauna da aka kai tsakanin Ngazalgana da Lamusheri a jihar Borno.

    Ya bayyana cewa, wannan farmakin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne da aka samu kan kai kawo da ƙungiyoyi masu tayar ƙayar baya ke yi a yankin.

    A cewarsa aikin wani bangare ne na ci gaba da ƙoƙarin hana mayakan samun walwala da kuma daƙile ƙarfin gudanar da ayyukansu a duk faɗin yankin.

  12. Ana ci gaba da Zanga-zangar adawa da hukumar ICE a manyan biranen Amurka

    Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Minneapolis a wani ɓangare na zanga-zangar adawa da ayyukan hukumar shige da fice da kwastam (ICE) bayan kisan gillar da jami'an gwamnatin tarayya suka yi wa wasu Amurkawa biyu.

    An kuma gudanar da zanga-zangar a biranen Amurka, ciki har da New York da Los Angeles da Chicago da Washington DC, inda masu shirya zanga-zangar ke kira ga Amurkawa da su kasance a gida kada su fita zuwa wuraren aiki ko makaranta.

    Kisan Renee Good da Alex Pretti ya haifar da zanga-zangar cikin gida tare da haifar da koke-koke a faɗin ƙasar, kuma ya haifar da suka daga ƴan majalisar dokoki daga jam'iyoyin ƙasar biyu biyu.

    Tun da farko a ranar Juma'a, ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ƙaddamar da binciken kan mutuwar Pretti.

  13. Kotu ta yi watsi da ƙarar wasu da aka yankewa hukuncin kisa a jihar Kwara

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke garin Ilorin a jihar Kwara ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa wasu mutane biyar da aka samu da laifin fashi da makami a wani banki a garin Offa a shekarar 2018.

    Daraktan sashen shigar da ƙara na jihar, Mohammed Akande, ya bayyana cewa duka alƙalai uku na kotun sun amince da hukuncin da babbar kotu ta yanke na kisa ta hanyar rataya.

    Wani jami’in kotun ya kuma ce kotun ta yi watsi da duka hujjojin waɗanda aka yankewa hukuncin suka shigar kuma ta ba da umarnin a mayar da su gidan yari cikin gaggawa.

    Ko da yake waɗanda aka yanke wa hukuncin suna da ƴancin tunkarar kotun ƙoli, jami’in ya ce hujjojin da aka gabatar a kotun ɗaukaka kara ba su da gamsarwa kuma da wuya sau yi nasara ba idan aka maimaita su a kotun ƙoli.

    Hukuncin dai ya samo asali ne daga wani fashin banki a watan Afrilun 2018 a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara, inda aka kai hari kan bankunan kasuwanci guda biyar.

    Aƙalla mutane 32 ne aka kashe, ciki har da ƴan sanda tara, biyu daga cikinsu mata ne, lamarin da ya sa ya kasance ɗaya daga cikin fashin banki mafi muni a tarihin Najeriya. .

  14. An tuhumi tsohon ma'aikacin CNN da shiga zanga-zangar adawa da ICE a Minnesota

    Tsohon mai gabatar da shirye-shiryen CNN Don Lemon ya bayyana a gaban alƙali bayan da aka kama shi da laifin shiga cocin Minnesota da ɗaukar hoton masu zanga-zangar adawa da hukumar shige da fice ta Amurka (ICE) a yayin da suka tarwatsa wata hidima a cocin.

    An saki Lemon bayan da ya bayyana a gaban kotu Ya shaida wa manema labarai a waje cewa an kama shi ne da laifin yaɗa labarai, ya ƙara da cewa: "Ba za a rufe mun baki ba."

    Hukumar tsaron cikin gida (DHS) ta ce an tuhume shi da laifin "haɗa baki don tauye haƙƙi" da "ketare dokar FACE", ta hanyar yin katsalandan ga ƴancin faɗin albarkacin baki.

    Lemon ya shiga Cocin Cities da ke St Paul a ranar 18 ga watan Janairu tare da masu zanga-zangar da suka ce ɗaya daga cikin fastocin jami’in tsaro ne na hukumar shige da fice.

  15. Gwamnatin Venezuela za ta yi wa fursunonin siyasa afuwa

    Shugabar riƙon ƙwarya ta Venezuela, Delcy Rodríguez, ta ce gwamnatinta za ta gabatar da wata doka ta afuwa ga ɗaruruwan fursunonin siyasa.

    Ta ce za a aika da daftarin dokar ga Majalisar Dokoki ta ƙasa mako mai zuwa.

    Wakilin BBC yan riuwaito cewa ƙudurin zai nemi a rufe fitaccen gidan yarin nan na El Helicoide, da ke birnin Caracas, wanda ake kallo a matsayin wani wuri da ake gudanar da ayyukan da su ka take haƙƙin ɗan'adam.

    Wannan matakin ya zo ne makonni huɗu bayan da sojojin Amurka suka kama Shugaba Nicolas Maduro, suka kuma buƙaci gwamnatin ta gabatar da sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki.

    Tuni aka riga aka saki ɗaruruwan fursunoni.

    Amurka ta ce an ƴantar da dukkan fursunonin Amurka da aka sani ana tsare da su a Venezuela.

  16. Aƙalla mutum 200 sun mutu a wurin haƙar ma'adinai a Congo

    An ruwaito cewa sama da mutane 200 ne suka mutu sakamakon ruftawar wasu wuraren hakar ma'adanai a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

    Kakakin gwamnan lardin Arewacin Kivu da 'yan tawaye suka nada, ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da masu hakar ma'adinai, da yara da mata.

    Ya ce, an ceto wasu daga cikinsu.

    Wurin yana samar da kusan kashi 15 cikin 100 na ma'adanin coltan na duniya, wanda yake da matuƙar muhimmanci ga samar da wayoyin hannu da sauran kayan lantarki.

    Yana ƙarƙashin ikon ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 tun shekarar 2024.

    Mutane sama da miliyan ɗaya da rabi ne ke aiki a irin waɗannan wurare da ba a amince da su ba, inda haɗurra irin waɗannan suka zamo ruwan dare.

  17. Bayanan da aka fitar kan Jeffrey Epstein sun tayar da ƙura a Amurka

    Wata ƙungiya ta waɗanda laifukan da attajirin nan na Amurka Jeffery Epstein da aka kama da ayyukan lalata suka shafa, sun soki ma'aikatar shari'ar ƙasar, bayan fitar da ƙarin takardu miliyan uku da suka shafi abubuwan da ya aikata.

    Mataimakin babban lauyan gwamnati, Todd Blanche, ya ce sun cire sunayen mutanen ne don kare su, in ban da waɗanda watakila suka taimaka masa wajen yin abubuwan da ya aikata, kamar Ghislaine Maxwell.

    Amma a cikin wata sanarwa, waɗanda abun ya shafa sun ce ana yayata sunayensu, wani abu da ke sake tuna musu irin cin zarafin da suka fuskanta a baya.

    Epstein shahararren attajiri ne da ya yi abota da manyan masu faɗa a ji a duniya, ciki har da shugabannin ƙasashe da ƴan kasuwa, kuma ya rika yi masu kawalci da sunan lalata sa'ad da yake raye.

  18. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.