Birtaniya da China sun amince da daƙile ƙaruwar tashin hankali a duniya
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce shi da takwaransa na Japan Sanae Takaichi sun amince da buƙatar mayar da martani game da ƙaruwar tashe-tashen hankula a duniya.
Yayin da ya kai ziyara Japan, Sir Keir ya ce alaƙar da ke tsakanin ƙasashen ita ce mafi ƙarfi da ta kasance cikin shekaru da dama.
Ƙasashen Japan da Biritaniya, na daga cikin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya.
A baya-ban nan sun ƙara haɗa kai don bunƙasa tattalin arziki da tsaro bayan ziyarar kwanaki uku da firaministan Birtaniya ya kai China.
















