Har yanzu ba a saki dukiyoyinmu da aka riƙe ba - Shugaban Babban Bankin Iran
Shugaban Babban Bankin Iran, Abdolnaser Hemmati, ya ce kawo yanzu ba a saki ko ɗaya daga cikin kuɗaɗe da kadarorin Iran da aka rike musu ba, kamar yadda aka tanada a yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.
A wata hira da gidan talabijin, Hemmati ya bayyana rahotannin cewa an mayar wa Iran wasu kuɗaɗe da zinare a matsayin jita-jita.
Ya ce har yanzu babu wata kadara ko kuɗin Iran da aka saki bisa yarjejeniyar.
A ƙarƙashin sashe na 11 na yarjejeniyar, Amurka ta yi alƙawarin bai wa Iran cikakkiyar damar amfani da kadarorinta da aka riƙe, tare da bayar da lasisin da ake buƙata domin mayar da kuɗin zuwa asusun da Babban Bankin Iran ya amince da su.
Sai dai wani jami’in Amurka ya ce sakin wasu daga cikin kadarorin zai dogara ne kan cika alkawarin da Iran ta ɗauka, ciki har da bayar da haɗin kai kan batun shirinta na nukiliya.