Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/07/2024.

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/07/2024.

Taƙaitattu

  • Manyan kamfanoni na fama da ɗaukewar intanet a sassan duniya
  • Mutum ɗaya ya mutu a harin da aka kai wa Isra'ila ta sama

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Su wane ne suka lakaɗa wa Danbilki Kwamanda duka a bidiyo?

    Wani bidiyon da ya ɓulla a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu mutane ke dukan ɗan siyasar mai yawan magana a kafofin yaɗa labarai da bulala bayan sun ɗaure hannunsa da ankwa.

    An ji mutanen da ba a ganin su a bidiyon na tuhumar sa kan dalilin da ya sa "yake zagin" gwamnan Kaduna Uba Sani, yayin da shi kuma yake musanta zargin.

    BBC Hausa ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a Abuja ranar Laraba da dare.

  2. Labarai da dumi-dumi, Ɗaukewar intanet ta jefa asibitocin Birtaniya cikin rikici

    Da alama wannan matsala ta fara ta'azzara a fannin lafiya na Birtaniya.

    Akwai rahotonni daban-daban cewa ma'aikatan hukumar lafiya ta NHS sun kasa samun damar shiga manhajar kwamfutarsu ta EMIS Web, wadda ke bai wa likitoci damar sama wa marasa lafiya gurbin ganin likita, da adana bayanansu.

    Asibitin Grimethorpe Surgery ya wallafa a shafinsa na X cewa an samu "babbar matsala", yana mai cewa "ya kasa" shiga manhajarsa.

    Daga baya asibitin ya ce: "Muna sane da cewa har yanzu mutane ba su iya shiga manhajar EMIS Web."

    Shi ma asibitin Church Lane Surgery ya ce "manhajojinmu ba su aiki tun ƙarfe 7:00 na safiyar yau [Juma'a]".

  3. Matsalar ɗaukewar intanet ta shafi duka filayen jirgin sama a Sifaniya

    Matsalar ɗaukewar intanet a sassan duniya ta tsananta a wasu yankuna.

    Hukumar da ke kula da filayen jirgin sama a Sifaniya ta sanar da "matsalar kwamfuta" a duka filayen jirgin sama na ƙasar, kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Kamfanin zirga-zirgar jirgin sama mafi girma a Turai, Ryanair, ya gargaɗi fasinjoji game da matsalar da aka samu, inda ya ce hakan zai iya shafar "dukkan jiragen da ke shirin tashi," kodayake dai bai fayyace abin da ya faru ba.

  4. Labarai da dumi-dumi, Manyan kamfanoni na fama da ɗaukewar intanet a sassan duniya

    Kamfanoni da hukumomin gwamnati a faɗin duniya na fama da matsala ta rashin layin intanet.

    An dakatar da tashin jirage a wasu birane kamar Sydney na Australia, wasu gidajen jarida da na talabijin sun dakatar da aiki.

    Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na United Airlines ya sanar da dakatar da aiki.

    Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani kan wannan batu.

  5. Mutum ɗaya ya mutu a harin da aka kai wa Isra'ila ta sama

    Sojojin Isra'ila sun ce suna bincike kan wani hari da aka kai da jirgi maras matuƙi da safiyar yau Juma'a a birnin Tel Aviv.

    Hukumar agajin gaggawa ta ƙasar ta ce harin ya kashe mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.

    Rundunar sojin ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna fashewar ta faru ne sakamakon faɗowar wani makami daga sararin samaniya.

    Wakiliyar BBC ta ce 'yan ƙungiyar Houthi ta Yemen sun ɗauki alhakin kai harin, inda suka wallafa a shafukan sada zumunta cewa za su saki bayanan yadda suka kai harin a Tel Aviv.

  6. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Juma'a.

    Ku biyo mu domin karanta abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar, har ma da maƙwabtansu.