Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/07/2024.

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/07/2024.

Taƙaitattu

  • Manyan kamfanoni na fama da ɗaukewar intanet a sassan duniya
  • Mutum ɗaya ya mutu a harin da aka kai wa Isra'ila ta sama

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Shugaban Kenya ya sake naɗa wasu ministocinsa shida da ya kora a makonnin baya

    Shugaban Kenya, William Ruto ya sake naɗa mutum shida daga cikin ministocin da ya kora makonnin da suka gabata.

    Mista Ruto ya sanar da sunayen mutum 11 cikin ƙunshin sabbin ministocin nasa, wato kimanin rabin adadin da kundin tsarin mulki ya sahale masa.

    Shugaban na Kenya ya ce har yanzu yana ci gaba da tuntuɓa kafa kafa abin da ya kira ''gwamnatin da ta ƙunshi kowa'' a ƙasar.

    Daga cikin ministocin da ya sake naɗawa akwai Kithure Kindiki, wanda ya sake komawa kan muƙamin da ya bari a baya na ministan cikin gida.

    An yi ta kiraye-kirayen ya sauka daga muƙaminsa sakamakon rawar da ya taka kan yadda 'yansanda suka murƙushe zanga-zangar adawa da ƙarin kuɗin haraji da aka gudanar a makonnin baya-bayan nan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40.

    An zargi 'yansanda da kamawa tare da muzgunawa masu zanga-zangar.

    A farkon wannan wata ne shugaban ya gana da jagoran adawar ƙasar Raila Odinga inda ya bayyana aniyarsa ta kafa kwamiti mai mambobi 150 domin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

  2. Gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220

    Gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 bayan sakamakon binciken da ƙasar ta gudanar wanda ya gano musayar bayanai da kamfanin ke yi ta kafofinsa na WhatsApp da Facebook sun saɓa wa dokar ƙasar.

    Binciken wanda hukumar kare haƙƙin masu sayayya ta ƙasar ta gudanar ya zargi kamfanin Meta da yin amfani da ɗaukar bayanan mutane ciki har da na sirrinsu ba tare amincewarsu ba da kuma mamayar kasuwanci.

    Hukumar ta kuma bukaci kamfanin ya biya ƙarin dala 35,000 na kuɗaɗen da ta kashe wajen gudanar da binciken.

    Gwamnatin Najeriya ta ba kamfanin wa'adin wata biyu ya biya kuɗaɗen na tara. Babu wani martani da ya fito daga kamfanin kawo yanzu.

  3. Gwamnati ta ba masu haƙar ma'adinai wa'adi su fice kudancin Kivu

    Mahukunta a lardin da ke da arzikin ma'adinai a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun bayar da umarnin dakatar da dukkan ayyukan hakar ma'adinai.

    Gwamnan kudancin Kivu, ya ce an ba wa dukkan kamfanoni da mutanen da ke wajen wa'adin sa'oi 72 su daina hakar ma'adinai.

    Ya ce an dauki matakin ne saboda rikicin da masu hakar ma'adinai ke haifarwa.

    Shekaru da dama, kungiyoyin masu dauke da makamai ke fada a kan kwace ikon wajen da ake hakar abubuwan da suka shafi zinare da makamantansu har ma da abin da ake amfani da shi wajen yin wayoyin salula.

  4. 'Sun kashe min ɗana' - Yadda iyaye ke jimamin yaran da suka mutu a ruftawar makarantar Jos

  5. Masu zanga-zanga sun fasa gidan yari a Bangladesh

    Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a Bangladesh sun ɓalle wani gidan yarin brnin Narsingdi, inda ɗaruruwan fursunoni suka gudu.

    Rahotanni sun ce ɗaruruwan masu zanga-zangar da suka abka gidan yarin, ya sa jami'an tsaro sun gaza tabbatar da tsaronsa yayin da kuma suka abka wa hedikwatar ƴansanda a yankin.

    Bangladesh na ci gaba da fuskantar zanga-zanga a faɗin ƙasar, mutum sama da ashirin aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Juma'a.

    Masu zanga-zangar na son sai firaminista da ta fi daɗewa kan karagar mulki Sheikh Hasina ta yi murabus da kuma tabbatar da sabbin sauye-sauye a ƙasar.

  6. Kotun Duniya ta bayyana matsayarta kan mamayar Isra'ila a yankunan Falasdinawa

    Babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mamayar Isra'ila a yankunan Falasdinawa ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    Kotun ta duniya ta yi umarni ga Isra'ila ta gaggauta dakatar da ayyukanta na mamayar yankunan Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Kudu, ayyukan da ta kira "haramtattu."

    A martaninsa, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana matakin na kotu a matsayin "ƙarya."

    Duk da cewa wannan matsayar ta kotun ICJ ba doka ba ce, amma tana da tasiri sosai a siyasance. Karon farko kenan da kotun ta bayyana matsayarta game da halaccin mamayar Isra'ila a yankunan Falasdinawa tsawon shekara 57.

    Kotun ta ICJ da ke da shalkwata a Hague kasar Netherlands, tun a bara take nazari kan batun bisa umarnin babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

  7. Gwamnatin Jigawa ta samar da rumbun ajiyar bayanan masu ƙaramin ƙarfi

    Hukumomi a jihar Jigawa sun ce sun samar da rumbun alƙaluman mutane masu ƙaramin ƙarfi da tsofaffi da kuma marayu a wani mataki na tallafa musu.

    Gwamnatin ta ce ta yi aikin tattara bayanan tsafaffi tare da haɗin gwiwar ‘yan ƙungiyoyi har 93,112, sai kuma marayu 65,607.

    Kwamishiniyar ma’aikatar harkokin mata Hajiya Hadiza Abdulwahab ta shaida wa BBC cewa sun tattaro waɗannan bayanan ne daga mazaɓun jihar 287 cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar.

    ''Mun tattaro bayanan ne daga ƙauyuƙa 9,000 da ke faɗin jihar'', in ji kwamishinar.

    Ta ƙara da cewa daga cikin tsofaffi marasa ƙarfi a jihar 93,112, mutum 56,802, mata kuma 36,230, marayu kuma muna da 65,607, kamar yadda kwamishinar ta yi bayani.

    Kwamishiniyar ta ce a yanzu za a fara tallafa wa tsofaffin marasa galihu da kuɗi naira 10,000 a kowane wata.

  8. Dubban ɗalibai a Bangladesh sun yi arangama da jami'an tsaro

    Ɗalibai a ƙasar Bangladesh sun sake fitowa kan titunan birnin Dhaka inda suka ƙi bin umarnin haramta zanga-zanga.

    Zanga-zangar da suka fara kafin yau ɗin ta jawo mutuwar mutum aƙalla 25 ranar Alhamis.

    An tsara yin jana'iza a wurare na musamman da zimmar yin jawabai na tunawa da mutanen da aka kashe.

    An sake kashe mutum biyu a yau Juma'a wanda ya sa jimillar mutanen da aka kashe tun bayan fara boren zuwa 33. Sai dai abu ne mai wuya a iya tantance haƙiƙanin mutanen da aka kashe saboda katsewar layukan sadarwa.

    Dubban 'yan ƙasar na zanga-zanga ne saboda matakin gwamnati na rarraba gurbin aiki ga iyalan dakarun sojin ƙasar da suka yi yaƙin neman 'yancin kan ƙasar a shekarar 1971.

  9. Ana zargin jami'an Ukraine 30 da sace kuɗin makamai

    Kimanin jamai'an Ukraine 30 ne ke fuskantar zargin karkatar da fiye da dala miliyan uku da aka ware domin saya wa sojojin ƙasar makamai.

    Ana gudanar da binciken ne a rundunar sojin ƙasar da masana'antu da wasu sassan ƙasar da dama.

    Masu shigar da ƙara sun ce suna zargin an karkatar da kuɗin ne a lokacin saya wa rundunar sojin ƙasar makamashin iskar gas da kayayyakin amfanin gida da sauran abubuwa.

  10. Kalli yadda katsewar intanet ta gigita dubban fasinjoji a sassan duniya

    Jiragen ɗaukar fasinja kimanin 110,000 da aka tsara tashinsa a faɗin duniya a yau Juma'a.

    Yayin rubuta wannan labari misalin ƙarfe 12:00 agogon Birtaniya, an soke tashin jirage 1390, kamar yadda kamfanin Cirium mai kula da zirga-zirgar jirage ya wallafa.

    Ga jadawalin kasashen da lamarin ya fi shafa

    • Amuka:jirage 512
    • Jamus:92
    • Indiya:56
    • Italiya:45
    • Canada:2
  11. ICPC za ta binciki ɓacewar ƙunzugun yara 13,350 a asibitin Kebbi

    Hukumar yaƙi da almundahana ta ICPC a Najeriya ta ce za ta binciki batun ɓacewar ƙunzugun yara da aka fi sani da Famfas kimanin 13,350 a ƙaramin asibitin shan magani da ke Sambawa a jihar Kebbi.

    Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin taron da hukumar da shirya a Abuja.

    Ya ce hukumar za ta yi bincike domin gurfanar da waɗanda ke da hannu a ɓacewar famfas ɗin.

    Shugaban hukumar ya ce al'ummar Sambawan ne suka kai wa hukumar ƙorafin ɓacewar famfas ɗin da aka tanada domin tallafa wa masu juna biyu da jaririn da ake haifa a asibitin.

    “Bincikenmu na farko ya nuna mana cewa yawan ƙunzugun da suka ɓace a asibitin ya kai 13,350, to amma binciken hukumar lafiya a matakin farko ta jihar Kebbi ya nuna adadin 3,466 ne'', in ji Adamu.

    Ya ce akai mutum biyu mace da na miji da ke aiki da ƙaramin asibitin na Sambawa da ake zargi da hannu a ɓacewar tarin ƙunzugun.

  12. Katsewar intanet ta tilasta wa direbobin tasi karɓar kuɗi-hannu a Landan

    Masau tasi a birnin Landan na fama wajen karɓar kuɗin mota da katin banki na kamfanin Visa daga fasinjojinsu.

    Direba Tony Vieira ya ce lamarin ya sa yanzu kwastomominsa sai dai su biya kuɗi hannu.

    Lamarin zai iya "haiafar da gagarumar matsala", in ji shi, yana mai cewa ana zuwa wurin da mutane ba su da kuɗin da za su biya.

    Wani direban tasin mai suna Tommy Johnson ya ce ya kasa shiga manhajarsa a yau gaba ɗaya, yayin da ya saba karɓar kuɗin ta hanyar kati.

    Sai dai ya yi sa'ar samun fasinjojin da ke da kuɗin a hannu. "Amma fa akwai mutanen da na ƙi ɗauka saboda matsalar."

  13. Rasha ta yanke wa ɗan jaridar Amurka hukuncin shekara 16 kan zargin leƙen asiri

    Wata kotu a Rasha ta yanke wa ɗan jaridar Amurka hukuncin ɗaurin shekara 16 a wani gidan yari mai cike da matakan tsaro, saboda laifin leƙen asiri, bayan an saurari ƙarar cikins sirri, wadda jaridar da yake yi wa aiki ta bayyana da ''abin kunya''

    A watan Maris ɗin da ya gabata ne jami'an tsaro suka kama ɗan jaridar mai aiki da jaridar Wall Street Journal (WSJ), a lokacin da yake aika rahoto a birnin Yekaterinburg, mai nisan kilomita 1,600 daga gabashin birnin Moscow.

    Masu shigar da ƙara sun zarge shi da aiki da hukumar leƙen asirin Amurka ta CIA, zargin da Mista Gershkovich da jaridar WSJ da Amurkan suka musanta.

    Wannan ne dai karon farko da aka yanke wa ɗan jaridar Amurka hukunci a Rasha tun bayan yaƙin cacar baka da aka ƙare fiye da shekara 30 da suka gabata.

    Amurka ta zargi Rasha da riƙe shi domin yin musayar fursunoninta da ke tsare a gidajen yarin ƙasashen waje.

  14. NDLEA ta kama kwalaben kodin fiye da 1,200,000

    Jami'an hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta najeriya sun kama kwalaben kodin miliyan 1,229,400 a cikin wasu kwatenoni bakwai a tashar jiragen ruwa ta Onne da ke birnin Fatakwal.

    Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce an yi ƙiyasin kuɗin kodin din ya kai fiye da naira biliyan 9.8.

    Kamen na zuwa ne ƙasa da mako uku da jami'an hukumar suka kama wasu kwalaben kodin fiye da miliyan guda a birnin na Fatakwal.

    Kamen na daga cikin jerin samamen da jami'an hukumar ke ƙaddamarwa kan tasoshin ruwan ƙasar, da nufin kakkaɓe safarar ƙwaya a tasoshin ruwan ƙasar.

    Hukumar ta ce bincikenta ya gano cewa an shigar da ƙwalaben daga ƙasar Indiya.

  15. Kusan jirage 1,400 ne aka soke tashinsu a faɗin duniya saboda da katsewar intanet

    Akwai jiragen ɗaukar fasinja kimanin 110,000 da aka tsara tashinsa a faɗin duniya a yau Juma'a.

    Yayin rubuta wannan labari misalin ƙarfe 12:00 agogon Birtaniya, an soke tashin jirage 1390, kamar yadda kamfanin Cirium mai kula da zirga-zirgar jirage ya wallafa.

    Ga jadawalin kasashen da lamarin ya fi shafa

    • Amuka: jirage 512
    • Jamus:92
    • Indiya:56
    • Italiya:45
    • Canada:2
  16. Kamfanin American Airlines ya fara dawo da harkokinsa.

    Kamfanin jirgen sama na American Airlines ya ce ya samu damar maido da harkokinsa bayan tsaikon da aka samu sakamakon katsewar intanet.

    Kamfanin na Amurka ya ce harkoki sun dawo da misalin ƙarfe 05:00 na asuba agogon ƙasar.

    "Muna neman afuwar kwastomominmu saboda jinkirin da aka samu,” kamar yadda kamfanin ya wallafa cikin sanarwar da ya fitar.

    Katsewar intanet ɗin dai ta haifar ta tsaiko, inda al'amura da dama suka tsaya sakamakon matsalar da ta kunno kai da asubahi ranar Juma'a.

  17. Katsewar intanet ta jawo soke tashin jirage sama da 1,000

    An soke tashin jirage sama da 1,000 a faɗin duniya zuwa yanzu saboda katsewar layukan intanet a wasu sassan duniya, kamar yadda shafin kamfanin sufurin jiragen sama na Cirium ya ruwaito.

    Wannan adadi da ya kai 1,078 a yanzu, zai ci gaba da ƙaruwa yayin da matsalar ke ƙara ta'azzara.

    Kamfanin ya ce yau Juma'a ya kamata ta zama rana mafi hada-hadar jiragen da za su tashi daga Birtnaiya a wannan shekarar, inda aka tsara aƙalla jirgi 3,200 za su tashi - mafi yawan adadi na kullum ke nan tun daga watan Oktoban 2019.

  18. Dalilin da ya sa muka amince da N70,000 mafi ƙanƙantar albashi - NLC

    Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya ce sun amince da naira 70,000 ne a matsayin mafi ƙanƙantar albashi saboda wasu alƙawura na daban da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi musu.

    Da suke magana ranar Alhamis jim kaɗan bayan ganawarsu da shugaban a Abuja, shugabannin ƙwadagon sun tabbatar da cewa sun karɓi tayin gwamnatin ne saboda ta ce za ta dinga sake duba albashin duk shekara uku maimakon biyar.

    "Abin da aka sanar game da ƙarin mafi ƙanƙantar albashi shi ne N70,000, amma abin jin daɗi a kan haka shi ne ba za mu dinga jira har sai shekara biyar ba kafin a sake duba shi," in ji Mista Ajaero. "Wannan ɗaya ne daga cikin dalilin da ya sa muka amince da shi."

    Ya ƙara da cewa sun yi wa shugaban ƙasar batun zanga-zangar ma'aikatan jami'o'i na Najeriya ƙarƙashin ƙungiyoyin SSANU da NASU da ke neman a biya su albashin watanni da gwamnati ta riƙe musu.

    "Wani abin kuma shi ne batun SSANU da NASU, da sauransu, musamman ma abin da kwamashinan 'yansandan Abuja ya yi musu. Mun faɗa wa shugaban ƙasa kuma mun nemi a kawo ƙarshen matsalar, inda ya nemi hukumomin da abin ya shafa su tsara yadda za a biya ma'aikatan," a cewarsa.

  19. Ƴan Boko Haram 263 sun miƙa wuya - Rundunar MNJTF

    Rundunar Sojojin Haɗin Gwiwwa mai Yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi ta ce mayaƙan ƙungiyar tare da iyalansa kusan 263 ne suka miƙa wuya ga sojojinta da ke aiki a yankin tafkin Chadi.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce 'yan ƙungiyar sun fara rububin miƙa wuyar ne daga ranar 11 ga wtan Yulin, lokacin da wasu mutum biyar suka miƙa wuya ga sojoji a garin Wulgo da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

    A ranar ne kuma, wasu 'yan ƙungiyar 19 suka miƙa wuya a wani ƙauye da ke yankin Arewa Mai Nisa a Jamhuriyar Kamaru.

    Cikin waɗanda suka miƙa wuyar akwai mata da ƙananan yara da kuma matasa, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

    Sojojin sun ce a ranar 15 ga watan na Yuli wasu ƙarin mutum 102, da suka haɗa da matasa 20 da mata 40 da ƙananan yara 42 ne suka miƙa wuya da yankin arewa mai nisan.

    Binciken farko ya gano cewa waɗanda suka miƙa wuyan 'yan Najeriya da Kamaru ne, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske, tana mai cewa an miƙa 'yan Najeriyar daga cikinsu hannun sojojin rundunar Operation HADIN KAI, domin ɗaukar mataki na gaba.

  20. United Airlines ya ce matsalar na'ura ta kamfanin Crowdstrike ce ta jawo ɗaukewar intanet

    Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na United Airlines, wanda shi ne mafi girma a duniya ta yawan fasinjoji, ya faɗa wa BBC cewa ya dakatar da duka jiragensa na fasinja daga tashi, kuma yana kan tattaunawa da waɗanda suke sararin samaniya.

    Sai dai ya ce matsalar ɗaukewar intanet da aka samu ta faru ne "saboda matsalar na'ura da kamfanin Crowdstrike ya samu da ke shafar kamfanoni da dama".

    Kamfanin ya ce yana aiki tare da kamfanin Crowdstrike mai samar da tsaron intanet domin shawo kan matsalar matsalar nan take.

    Kamfanin kan ɗebi fasinja 578,000 a kullum a adadi na tsakatsaki.