Isra'ila na jimamin zagayowar ranar kai harin Hamas
Isra'ila ta cika shekaru biyu da zagayowar hare-haren da Hamas ta kai, lamarin da ya janyo mutuwar fararen hula da sojoji sama da dubu 1200.
Abun da kuma ya janyo soma yakin Gaza.
Ana gudanar da tarukan tunawa da ranar a wurare daban-daban a ƙasar, ciki har da wurin bikin nan na Nova, inda aka kashe aƙalla mutane 400.
Ana kuma yin irin wannan taro a dandalin Telaviv, da ke babban birnin na Isra'ilar wanda aka sauya wa suna zuwa dandalin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Ana tunawa da zagayowar ranar ne yayin da kuma a Masar, ake tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da za ta kai ga ceto waɗanda suka rage a hannun Hamas.
Shugaba Trump ya yaba da irin abubuwan da aka cimma a ranar farko ta tattaunawar, yayin da sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ke jaddada buƙatar amfani da wannan dama don kawo ƙarshen zubar da jini a Gaza.