Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 09/04/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Wace ce marigayiya Saratu Daso da aka gaza maye gurbinta?, Daso ta cika shekara guda da rasuwa cif-cif

    A game da irin giɓin da ta bari a masana'antar Kannywood, fitaccen mai shiryan fina-finai a Kannywood, Alhaji Naziru Auwal, wanda aka fi sani da Ɗan Hajiya ya ce giɓi ne babba wanda da wahala a iya mayewa.

    Ya ce, "Hajiya Daso mutum ce wadda take taka rawa ta musamman a fim wanda ba kowa ba ne yake iya takawa. Idan ka duba kusan fim ɗinta na ƙarshe shi ne fim ɗina mai suna Umarni. Mun yi zango na farko da ita ne sai Allah ya yi mata rasuwa."

    Ya ce duk da cewa a lokuta da dama idan aka samu irin haka ana musanya jarumi ne, "amma na yi iya dubawar da zan iya, amma har ga Allah ban samu abin da nake so ba, sai dai kawai kwatantawa, haka kawai na haƙura na kashe fitowar. Don haka gaskiya ta bar mana babban giɓi, fatanmu shi ne Allah ya mata rahama," in ji shi.

    Dangane da ayyukan jinƙai ma, har yanzu ba a iya maye gurbinta ba.

    "A wannan azumin yara suka zo suka sa me ni kan batun kayan Sallah, sai na ce musu ai dama Daso ce ke ba ku yanzu kuma ba ta nan. Ni kuma ba ni da ƙarfin yin abin da take yi." In ji Zinaru Muhammad Giɗaɗo, ƙanwa ga marigayiya Daso.

  2. Likitoci 16,000 sun fice daga Najeriya cikin shekara shida - Pate

    Likitoci 16,000 sun fice daga Najeriya cikin shekara biyar ko shida, in ji Ministan Lafiya Muhammad Pate.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito ministan na magana yayin wani taron ƙara wa juna sani na ƙungiyar likitoci ta Association of Medical Councils of Africa (AMCOA) ranar Talata, yana mai cewa hakan ya jawo wa ƙasar asarar biliyoyin naira.

    Ya ce ƙiyasin kuɗin da ake kashewa wajen bai wa likita ɗaya horo a Najeriya ya zarta dala 21,000, inda ya nuna damuwa game da yadda Najeriya ke asarar irin waɗannan kuɗaɗe.

    "Wannan lamari ba wai magana ce kawai ta mutanen da ke ficewa ba, hakan na nufin asara," in ji ministan.

    "Yana shafar ɓangaren kula da lafiyarmu sosai, inda yankunan ƙauyukanmu suka fi shiga haɗari."

    Ya ƙara da cewa yanzu yawan mutanen da likita ɗaya ke gani a Najeriya ya ƙaru zuwa miliyan 3.9, wanda ya zarta adadin da hukumar lafiya ta duniya ta ƙiyasta sosai.

  3. Al-Shabab ta yi iƙirarin kashe sojojin Somalia 53

    Ƙungiyar Al-Shabab mai iƙirarin jihadi ta ce ta kashe sojojin Somalia 53 tare da raunata wasu 87 yayin fafatawa tsakaninsu a yankin Hiiraan na tsakiyar ƙasar.

    Shafin Calamada na ƙungiyar ya ce dakarunsu sun daƙile hare-haren dakarun gwamnati da dama, waɗanda ke samun taimakon sojojin Amurka ta sama.

    Ta kuma wallafa sunayen wasu jami'an soji da ta yi iƙirarin kashewa a ɓarin wutar. Daga ciki akwai na rundunar Danab da suka samu horo daga sojin Amurka, da kuma na hukumar tsaron ƙasa.

    Gwamnati ta ce ta ƙwace ƙauyen Aborey da ke yankin bayan yaƙin da dakarunta suka tafka da mayaƙan.

    Al-Shabab da dakarun gwamnatin Somalia sun yi ta fafatawa a ƙoƙarin kama iko da garin na Aborey tun daga 7 ga watan Afrilu, lokacin da mayaƙan suka ce sun ƙwace shi.

  4. Amurka ta damu kan kayanta da Najeriya ta hana shigarwa ƙasar

    Amurka ta nuna damuwa kan wasu kayayyakin kasuwancinta 25 da Najeriya ta hana shiga da su ƙasar, tana mai cewa hakan na daƙile riba.

    Hukumar kula da harkokin kasuwanci na Amurka ne ya bayyana hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa.

    Sanarwar na zuwa ne bayan Shugaba DOnald Trump ya ƙaƙaba wa kayayyakin ƙasashen duniya 60 ƙarin haraji, ciki har da na kashi 14 cikin 100 da ya saka wa Najeriya.

    Hukumar USTR ta ce cikin kayan da Najeriya ta hana shiga da su ƙasarta sun shafi noma, da magunguna, da ababen sha, da naman alade, da kayan kiwon kaji.

    Masana tattalin arziki na cewa Najeriya ta yi hakan ne saboda ta haɓaka kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida a shekarar 2016.

  5. Harajin Trump kan ƙasashen duniya ya fara aiki

    Sabon harajin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaƙba wa ƙasashen duniya fara aiki.

    Matakin wanda ya shafi ƙasashe 60 za su biya karin haraji kan kayan da suke shigarwa Amurka daga yau Laraba.

    Cikin waɗanda matakin ya shafa har da gagarumin karin da Trump ya yi wa China na kashi 104 cikin 100.

    China ta soki Donald Trump a matsayin "mai tursasawa" inda kuma ta ce ba za ta janye matakin harajinta na ramuwa kan Amurka ba.

    Wakilin BBC ya ce harajin kashi 104 kan China shi ne mafi girma a tarihi.

    Matakin na Trump ya tagayyara kasuwar hannayen jari ta duniya, inda aka yi hasarar biliyoyin dala saboda halin da masu zuba jari suka shiga na rashin tabbas.

  6. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin halin da duniya ke ciki a yau, inda za mu kawo rahotonni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.