'Yansanda sun kama shugaban babbar jam'iyyar adawa a Tanzania
Asalin hoton, AFP
Babbar jam'iyyar adawa a Tanzania ta ce 'yansanda sun kama shugabanta, Tundu Lissu, bayan ya halarci wani gangamin da aka gudanar a kudancin kasar.
Kungiyoyin kare hakki dan adam sun zargi gwamnatin shugaba Samia Suluhu Hassan, da matsawa 'yan adawa gabannin babban zaben dake tafe a watan Oktoba mai zuwa.
A makonnin baya-bayannan Mista Lissu, na yawaita gudanar da taron gangamin siyasa a sassan Tanzania da kuma neman kawo sauyi a harkokin zaben kasar.
A shekarar 2017 ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka yi kokarin hallaka shi.
Babu wanda zai iya maye gurbin Daso a Kannywood - Falalu Ɗorayi
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Yayin da tauraruwar Kannywood, Saratu Daso ke cika shekara ɗaya da rasuwa, furodusa a Kannywood, Falalu Dorayi ya bayyana wa BBC irin giɓin da ta bari da kuma kyakkyawar mu’amalarta da abokan aiki a lokacin daukar fim.
Faransa na shirin amincewa da yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa mai ƴanci
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasɗinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa.
Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York.
Kasashe 147 kawo yanzu ne suka amince da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai ƴanci.
Sifaniya da Ireland da Norway su ne na baya-bayan nan da suka nuna amincewarsu a watan Mayun bara.
An dakatar da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Zamfara saboda bullar cutar gubar dalma
Asalin hoton, OTHERS
Gwamnatin Najeriya, ta umarci masu hakar ma’adanai a jihar Zamfara ba bisa ka’ida ba, da su dakatar da ayyukansu kuma su fice su bar wuraren da suke hakar ma’adanan.
Wannan na zuwa ne bayan tabbacin da aka samu na barkewar cutar gubar dalma a cikin karamar hukumar mulki ta Bungudu.
Ministan tama da karafa na kasar Dele Alake, shi ne ya sanar da hakan to amma ya ce za a koma ci gaba da hakar ma'adinan da zarar an kammala tantance abin da ya janyo barkewar cutar ta gubar dalma.
Masu hakar ma'adinai a kasar sun ce basu tsammaci daukar matakin ba sai kawai suka ji shi kwatsam, to amma duk da haka za su bi umarnin da aka ba su domin su suna hakar ma'adinai nai bisa ka'ida.
Alhaji Sa'adu Adamu mai zinare, shi ne mataimakin shugaban kungiyar masu hakar ma'adinai a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, su babban abin da ke basu mamaki shi ne inda aka samu barkewar cutar sam ba a hakar ma'adinai a wajen.
Ya ce,"Mu abin da muke fata shi ne a gudanar da bincike a kan yadda aka yi a samu bullar cutar domin su inda suke sana'arsu ba a samu bullar wata cuta ba.
Jihar Zamfara ta yi fice wajen hakar ma'adinai kasancewar tana da dumbin arzikin ma’adanai a kasar musamman zinare.
Amurka ta dakatar da harajin da ta lafta wa ƙasashen duniya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Amurka, Donald Trump
A wani mataki na ba-zata, shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da haraje-harajen da ya lafta kan kayayyakin da ke shiga ƙasar daga ƙasashen duniya, sai dai ban da kayan da ke shiga ƙasar daga China.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai za a ƙara wanda aka lafta kan kayan China zuwa kashi 125%.
Donald Trump ya kuma zargi China da nuna rashin girmamawa da kuma zaluntar Amurka.
Kafin haka, China ta sanar da ƙara haraji kan kayan Amurka da ake shiga da su China zuwa kashi 84% - inda Chinar ta zargi Amurka da amfani da dabarar "zare idanu" kan ƙasashen duniya.
Ecowas ta buƙaci Mali da Algeria su mayar da wuƙa cikin kube
Asalin hoton, Assimi Goita
Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Mali, Assimi Goita
Hukumar Ƙungiyar cigaban ƙasashen yammacin Afirka, Ecowas ta nuna damuwa kan rashin jituwar da ta ɓalle tsakanin ƙasar Mali da maƙwafciyarta Algeria, lamarin da ya kai ga ƙasashen biyu janye jakadunsu daga juna.
A cikin wata sanarwa da ta fitar yau a Abuja, Ecowas ta ce "Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin ƙasar Mali da kuma Algeria, kamar yadda za a iya gani a jerin sanarwar da dukkanin ɓangarorin biyu suka fitar.
A madadin ƙasashen da ke da wakilci a cikinta, Ecowas na nuna matuƙar damuwarta kan lamarin. Tana kuma kira ga Mali da Algeria da su yayyafa wa wutar lamarin ruwa, su buɗe hanyoyin tattaunawa sannan su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya na yanki da nahiya wajen warware saɓanin ra'ayin da ke tsakaninsu."
A makon da ya gabata ne Algeria ta kaɓo wani jirgi maras matuƙi mallakin sojojin ƙasar Mali, wanda ta ce ya karya dokokin kan iyakar ƙasarta.
Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Algeria kiranye, haka nan ma ƙasashen ƙumgiyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar ɗaukar irin wannan mataki.
Lamarin da ya sanya ita ma Algeria ta yi wa jakadunta da ke Mali da Jamhuriyar Nijar kiranye, sannan ta ce za ta jinkirta tura jakadanta zuwa Burkina Faso, wadda ita ma mamba ce a ƙungiyar ta AES.
Hakan nan ƙasar ta Algeria ta fitar da sanarwa ɗauke da kausasan kalamai, sannan ta yi fatali da zargin da Mali ke mata kan cewa tana ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci a yankin Sahel.
An nada shugabannin kananan hukumomi a jihar Ribas
Asalin hoton, Ibok-Ete Ekwe Ibas
Bayanan hoto, Ibok-Ete Ekwe Ibas
Gwamnan rikonkwarya na jihar Ribas, Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya nada shugabannin kananan hukumomi
23 na jihar, duk da umarnin da wata babbar kotun tarayya ta bayar na hana shi
yin hakan.
Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 7 ga watan Afrilu, 2025, wani
bangare ne na gwagwarmayar neman mulki tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da
‘yan majalisar dokoki masu biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike.
To
sai dai al’ummar jihar na neman a bayyana musu yadda za a tafiyar da kasafin
kudin jihar bisa la’akari da cewa babu ‘yan majalisar dokokin jihar domin
tantancewa.
Wadannan nade-nade da kantoman ya yi sun janyo zarge-zargen cewa ya yi watsi da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.
Rahotanni sun ce al'ummar jihar na nan na nuna rashin jin dadinsu a game da abubuwan da ke faruwa a harkar tafiyar da gwamnatin jihar.
Gwamnatin nrikon kwaryar nan dai na nan na kakkabe dukkan wasu abubuwa da tsari na dimokradiyya a jihar.
A ranar 18 ga watan Maris din 2025, ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Yakin kasuwancin da aka shiga a duniya sun kassara kasuwannin hannayen jari
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Jirgin dakon kaya
Yaƙin kasuwancin da aka shiga a duniya kan haraje-haraje sun sake kassara kasuwanni hanayen jari a duniya.
Kasuwanni Turai da na Asiya sun shiga yanayi na halin ha'ula'i.
Masu sharhi na ganin ma su zuba jari na bukatar karin kuɗaɗe, ko kuma suna ganin kamar zuba kudadensu a kamfanonin Amurka na da hadari.
China na daga cikin manyan kasashen duniya da ke bin gwamnatin Amurka bashi, kuma ana ganin cewa ta na daga cikin na gaba-gaba wajen sayar da takardun lamuni.
Karuwar bashi da ake bin gwamnatin Amurka zai iya yin illa ga bangaren ba da bashin gidaje da kudin ruwa.
Mutum 113 sun mutu a gidan rawa a jamhuriyar Dominican
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, .
Hukumomi a jamhuriyar Dominican sun sanar da cewa akalla mutum 113 ne suka mutu wasu sama da 150 suka jikkata, lokacin da wani gidan casu ya rufta a birnin Santo Domingo.
Gwamnan yankin kuma tsohon dan wasan Baseball Octavio Dotel, na daga cikin wadanda suka mutu.
Dotel, ya rasu a kan hanyar zuwa asibiti bayan an yi nasarar ciro shi daga baraguzam da suka danne mutane.
Lamarin dai ya faru ne a wani wajen bikin wakoki da aka yi.
Rahotanni sun ce mawakin da ya yi waka a wajen na daga cikin wadanda suka mutu.
Sama da jami'an aikin ceto 400 na ta fadi tashi domin zakulo wadanda suka tsira da ransu.
Ana dai fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu.
Sama da mutum miliyan bakwai na cikin matsananciyar yunwa a Sudan ta Kudu
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, .
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan bakwai na cikin matsananciyar yunwa a Sudan ta Kudu tare da gargadin yadda matsalolin tsaro ke haifar da cikas wajen ayyukan agaji.
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce yankunan da aka fi fuskantar fari sun hada da jihohin da ke arewa maso gabashi, inda ake gwabza yaki tsakanin sojoji Sudan da dakarun da ke biyayya ga mataimakin shugaban kasa, Riek Machar.
Sannan wasu yankuna na kasar kuma na fama da 'yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwararowa daga makwabciyar kasar Sudan da ke fama da yaki, lamarin da ya kai ga an samu barkewar kwalara.
Ƙasashen Turai sun lafta wa Amurka haraji
Asalin hoton, FULTON COUNTY SHERIFF'S OFFICE
Bayanan hoto, Donald Trump
Kasashen kungiyar tarayyar Turai sun kada kuri'ar amincewa da laftawa Amurka haraji.
Kasashen za su sanyawa Amurkawa harajin kashi 25 cikin 100 a kan kayayyakin da ta ke shigarwa kasashensu daga watan Afrilu.
Rahotanni sun ce kayayyakin da Amurkan ke shigarwa da su da za a sanyawa harajin sun hadar da kayan amfanin gona kamar alkama da na kiwon kaji da motoci da makamantansu.
Wannan shi ne martanin kasashen a kan harajin da Amurkan ta sanyawa kasashen kungiyar ta EU.
Za a ci gaba da sayar wa matatun mai ɗanyen mai da naira
Asalin hoton, NNPCL/X
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da sayar wa matatun mai ɗanyen mai da kuɗin naira.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin kuɗi ta tarayya ta fitar a shafinta na X ranar Laraba.
Ma'aikatar ta ce tsarin, wanda majalisar zartaswa ta fara amincewa da shi, wani daɗaɗɗen yunkuri ne da aka ɗauki tsawon lokaci ana tsara shi.
A cewar ma'aikatar, masu ruwa da tsaki sun nuna goyon bayansu da kuma tabbatar da ganin tsarin na sayar da ɗanyen mai ga matatu a naira ya tafi daidai.
Tsarin wanda ya buƙaci cinikayyar ɗanyen mai a kuɗin naira, an yi shi ne da zimmar ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar da inganta tace mai a ƙasar da kuma daidaita ƙudin ƙasashen waje ta hanyar rage buƙatar dala a cinikayyar ɗanyen mai.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa wannan tsari zai kuma janyo hankalin masu zuba jari a ɓangaren tace ɗanyen mai.
Jami'an lafiya a Gaza sun ce hare-haren Isra'ila sun kashe mutum aƙalla 29
Asalin hoton, Reuters
Jami'an lafiya a zirrin Gaza sun ce aƙalla mutane 29 aka kashe a hare-haren Isra'ila a gabashin birnin.
Gommai sun jikkata inda suke samun kulawa a asibiti, akwai kuma waɗanda ɓaraguzan gine-ginen suka binne.
Shaidu sun ce gini mai hawa huɗu ya ruguje sakamakon harin makami mai linzami a anguwar Shejaiya mai yawan al'umma.
A cewar sojojin Isra'ila, suna kai hare-haren ne kan Hamas, kuma suna ɗaukan matakai don ganin ba a cutar da fararen-hula ba.
Gwamnonin PDP 11 sun shigar da ƙara don kalubalantar dakatar da Fubara
Asalin hoton, Getty Images
Wasu gwamnoni 11 karkashin jam'iyyar PDP, sun shigar da ƙara gaban kotun koli inda suke kalubalantar dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.
Ƙarar da gwamnonin suka shigar ranar Talata, na kuma kalubalantar ayyana dokar ta-baci da aka yi a jihar.
Gwamnonin jihohi da suka shigar da ƙarar sun haɗa da Adamawa da Enugu da Osun da Oyo da Bauchi da Akwa Ibom da Plateau da Delta da Taraba da Zamfara da kuma Bayelsa.
A ƙarar da suka shigar, gwamnonin na kuma son kotun kolin ta ayyana cewa ko shugaban ƙasa na da ikon dakatar da zaɓaɓɓen gwamna na jiha.
Sun kuma buƙaci kotun ta yanke hukuncin cewa ko yadda shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar ta Ribas bai saɓa wa kundin tsarin mulki na 1999 ba.
Hare-haren dakarun RSF sun hallaka mutum 11 a Sudan
Asalin hoton, RSF
Hare-hare da jirage marasa matuka da mayaƙan RSF suka kai a sassa daban-daban na Sudan, sun yi ajalin rayukan mutane 11 ciki har da ƙananan yara.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka lalata gidaje a El Obeid, birnin jihar Kordofan ta Arewa.
An kashe mutum biyar ƴan gida ɗaya - sannan mayaƙan na RSF sun kuma lalata katafaren madatsan ruwa mafi girma da ke samar da lantarki a ƙasar.
Motar bas ta ƙwace, ta hallaka mutum biyar a Yobe
Asalin hoton, Getty Images
Wata motar bas ƙirar Toyota Hiace mai lamba KTG 283 XA ta ƙwace tare afka wa cikin kasuwar Damagum a jihar Yobe, inda ta hallaka wata mai juna biyu tare da wasu mutum huɗu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta jihar, Livinus Yilzoom, ya ce hatsarin ya kuma jikkata mutum 19.
"Lamarin ya afku ne da yammaci lokacin da ake shirin rufe kasuwar. Mutane biyar ɗin da suka mutu ba su cikin motar bas ɗin, suna ƙoƙarin tsallake titi motar ta afka musu," in ji Livinus.
Ya ce dreban motar ya yi ƙoƙarin kauce wa mutanen, amma sai motar ta ƙwace masa sannan ya afka musu.
Ya ƙara da cewa tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata da kuma gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa babban asibitin Damagum.
Ya ce bincikensu ya gano cewa gudu fiye da ƙima na cikin abubuwan da suka janyo afkuwar hatsarin.
Labarai da dumi-dumi, China ta lafta wa kayan Amurka harajin 84%
Ma'aikatar Kuɗi ta China ta sanar da kashi 84 cikin 100 a matsayin ƙarin haraji kan kayan Amurka da ake shigarwa ƙasar.
Ma'aikatar ta ce ƙarin zai fara aiki daga ƙarfe 5:00 na asubahin Alhamis agogon Najeriya.
An kwaso 'yan Najeriya 144 da suka maƙale a Libya zuwa gida
Asalin hoton, Nema
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta karɓi 'yan ƙasar 144 da suka maƙale a Libya ranar Talata bayan isar su.
Mutanen sun sauka ne da misalin ƙarfe 5:15 na yamma a filin jirgi na Murtala Muhamed da ke Legas.
Cikin mutanen da aka kwaso akwai maza 89, mata 35, yara 17, da jarirai uku, inda ƙungiyar kula da 'yan gudun hijira ta International Organization for Migration (IOM) ta agaza musu.
An kai su sansanin 'yan gudun hijira na Igando bayan kammala tantance su, in ji hukumar Nema.
Ƙasashen Turai za su kaɗa ƙuri'ar ƙaƙaba wa Amurka ƙarin haraji
Asalin hoton, Reuters
Ƙasashe 27 mambobin Tarayyar Turai za su kaɗa ƙuria'a a yau Laraba domin saka wa wasu jerin kayayyakin Amurka haraji a mako mai zuwa.
Matakin martani ne ga ƙarin harajin kashi 25 cikin 100 da Shugaban Amurka Donald Trump ya saka wa ƙasashen a makon da ya gabata kan ƙarafan da suke kaiwa ƙasarsa.
Haraje-harajen na Turai za a kasa su zango uku.
Daga Talata mai zuwa, za a saka harajin kashi 25 kan jerin farko da ake tunanin za su ƙunshi babura, da jiragen ruwa na alfarma, da lemukan roba.
Tun farko an tsara za su fara aiki daga 1 ga wtaan Afrilu amma sai aka jinkirta domin samun damar tattaunawa.
Tayin da shugabar hukumar Turai Ursula von der Leyen ta yi na cire dukkan haraje-haraje ba ta samu karɓuwa ba a wajen Trump.
Mazauna Tilaberi a Nijar na guduwa daga gidajensu saboda barazanar 'yanbindiga
Mazauna garin Makalondi na jihar Tillaberi a Jamhuriyar Nijar sun fara guduwa zuwa Yamai babban birnin ƙasar sakamakon barazanar da 'yanbindiga suka yi musu.
Rahotonnin da BBC ta tattara sun nuna cewa 'yanbindigar da suka kwana biyu suna addabar yankin sun bai wa mazauna wurin wa'adi na ko dai su fice ko kuma su fuskanci hare-hare.
A 'yan kwanakin nan dai an sha jin mazauna garin na kiraye-kiraye ga gwamnatin sojan ƙasar da ta kai musu ɗauki saboda da yadda 'yanbindigar ke yi musu barazana.
A makon da ya gabata maharan sun sace dabbobi masu aywa a yankin tare da cinna wa shagunan kasuwanci wuta bayan sun kwashe kayayyakin ciki.