Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/07/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 22 ga watan Yuli, 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025

    Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar 2025, a cewar rahoton Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).

    Sanarwar da NBS ɗin ya fitar ranar Litinin, ta ce wannan ya zarta kashi 2.27 cikin 100 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2024.

    Rahoton ya ce ɓangarorin da suka fi ba da gudummawa wajen haɓakar tattalin arziƙin sun haɗa da na ayyuka da kuma masana’antu.

    A lokaci guda kuma an sabunta ƙididdigar GDP daga shekarar 2019, inda sabon adadin ya kai naira tiriliyan 205, a cewar shugaban hukumar ƙididdiga ta ƙasa, Adeyemi Adeniran.

    Ya bayyana cewa sabon adadin ya ƙaru da kashi 41.7 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2014.

    Adeniran ya ƙara da cewa sassa guda biyar da suka fi taka rawa wajen wannan ci gaban sun haɗa da: noman da kasuwanci da ɓangaren masana'antu da kamfononin sadarwa da kuma man fetur da iskar gas.

  2. WHO ta buƙaci Isra’ila ta saki ma’aikacinta da aka kama a Gaza

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya bukaci Isra’ila ta saki wani ma’aikacin hukumar da ya ce sojojin Isra’ila sun kama a wani farmaki da suka kai a tsakiyar Gaza ranar Litinin.

    Tedros Ghebreyesus ya ce sojojin sun jefa ma'aikatan agaji da iyalansu cikin hatsari a lokacin da suka shiga gidajensu da kuma babban dakin ajiyar kaya a Deir al-Balah.

    Ya yi alƘawarin cewa WHO za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a yankin.

    Deir al-Balah dai na cike makil da Falasɗinawa da suka rasa matsugunansu a kusan shekaru biyu na yakin Gaza

  3. Bangladesh na zaman makokin mutum 27 da suka mutu a hatsarin jirgin soji

    An sassauta tuta a sassan Bangladesh yayin da kasar ke zaman makokin mutum 27 da suka mutu a lokacin da wani jirgin soji ya yi hatsari a wata makaranta.

    An gudanar da addu'o a masallatai. An kuma ɗage jarabawar makaratun sakandare.

    Galibin waɗanda suka mutu yara ne. Sama da mutum 170 kuma sun jikkata, galibinsu ɗalibai a wata kwaleji da ke babban birnin ƙasar.

    Shugaban riko na ƙasar Muhammad Yunus ya yi alkawalin gudanar da bincike kan abin da ya janyo hatsarin jirgin

  4. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Talata.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.