Kungiyar Bournemouth ta kammala sayen dan wasan gaba Rayan daga Vasco da Gama kan kudin farko na fam miliyan 24.7, bisa kwantiragin shekaru biyar da rabi, wanda kuma ya kunshi kari na fam miliyan 5.6 idan an cika wasu sharudda.
Bournemouth ta doke wasu kungiyoyi da dama daga Turai, da kuma kungiyoyi daga Saudiyya da Rasha, domin samun sa hannun dan wasan Brazil mai shekaru 19.
Wannan shi ne saye na biyu mafi tsada a tarihin Bournemouth, tare da fam miliyan 32 da suka biya a 2024 domin dauko dan kasar Brazil kuma dan wasan gaba Evanilson daga Porto.
Rayan ya koma gabar tekun kudancin Ingila ne a matsayin maye gurbin dan wasan gaba Antoine Semenyo, wanda ya koma Manchester City kan kusan fam miliyan 65 a farkon wannan wata.
Matashin dan wasan na taka leda ne a matsayin dan wasan gaba na tsakiya mai amfani da kafar hagu, amma yana iya buga wasa a bangarori biyu na gaba. Dan wasan tawagar Brazil ta ‘yan kasa da shekaru 20 ya ci kwallaye 14 a wasanni 34 na gasar firimiya ta Brazil a kakar da ta gabata.
Haka kuma, kungiyar Bournemouth ta kammala yarjejeniyar aro da golan kasar Girka, Christos Mandas, daga kungiyar Lazio ta gasar Serie A ta Italiya.
Golan mai shekaru 24, wanda ya zama dan wasan Girka na farko a tarihin kulob din, ya zo ne a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa, tare da zabin saye gaba daya.
Bournemouth na biyan kudin aro na euro miliyan 1.5 (fam miliyan 1.3), sannan za su biya karin fam 860,000 idan suka yanke shawarar kada su saye shi gaba daya.
Idan suka zabi sayen sa a dindindin, farashinsa zai kai fam miliyan 16.