Congo ta zargi maharan M23 da kai mata harin jirage maraa matuƙa a filin jirgin Kisangani
Lardin Tshopo na Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo ya sanar da cewa jami'an tsaron ƙasar sun samu nasarar daƙile yuƙurin harin jirage marasa matuƙa a babban filin jirgin saman Bangoka da ke birnin Kisangani a ranar 1 ga watan Fabrailun da ta gabata, kamar yadda tashar rediyo ta Radio Top Congo FM ta ruwaito.
Kakakin gwamnatin lardin ne ya sanar hakan, inda ya zargi mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da ƙaddamar da harin, sannan ya ƙara da cewa maharan sun yi amfani da jirage marasa matuƙa.
"Wannan zalunci ne da rashin hankali da Rwanda da ƙawayenta suke yi domin tayar da zaune tsaye a ƙasarmu. Muna godiya da yabo bisa ƙoƙari da jajircewar jami'an tsaronmu wajen daƙilewa tare da kakkaɓo jirage marasa matuƙa guda 8," in ji shi.
Sai dai babu tabbaci ko harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane ko yanayin asara da aka yi.
Kisangani na yammacin biranen Nord da Sud Kivu, waɗanda M23 suka fi ƙarfi, kuma a baya mayaƙan sun yi barazanar kutsawa Kinsaha ta hanyar Kisangani.