Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 01/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/10/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

  1. Shugaban Iran ya yi gargaɗi ga Isra'ila

    Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya kare matakin harin da ƙasarsa ta kai tare da yin gargaɗi ga Isra'ila.

    A shafinsa na X, shugaban ya ce "bisa la'akari da haƙƙin Iran tare da manufar zaman lafiya da tsaron Iran da yankin, an mayar da martani ga Isra'ila don kare muradun Iran da ƴan ƙasa."

    Da ambaci Netanyahu, inda ya ce Firaministan Isra'ila ya sani cewa "Iran ba mayyar yaƙi ba ce, amma za ta kare kanta daga duk wata barazana.

    Ya yi gargaɗi ga Isra'ila cewa wannan harin kamar kyaftawar ido ne" na ƙarfin Iran da kuma kaucewa shiga yaƙi da Iran..

    Wannan na zuwa yayin da rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta ƙaddamar da harin martani cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

  2. An harbe mutum shida a Isra'ila

    An harbe mutum shida a wani hari da aka kai a Tel Aviv. Akalla wasu mutane bakwai kuma sun jikkata, da dama daga cikinsu sun samu munanan raunuka.

    'Yan sanda sun ce harin ya auku ne a kusa da tashar jirgin kasa da ke yankin Jaffa na birnin.

    Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce maharan biyu da aka gani suna sauka daga jirgin kasa, wani mai wucewa ne da kuma wani mai gadi ne suka harbe su.

    Hotunan sun nuna daya daga cikin maharan dauke da bindiga.

    Zuwa yanzu ba a san dalilin kai harin ba.

  3. Isra'ila ta ce za ta mayar wa Iran martani a lokacin da ta ga ya dace

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce babu mugun lahani da hare-haren makaman Iran suka yi kan ƙasarta.

    Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce hare-haren za su haifar da mummunan sakamako.

    "Muna da tsari, kuma za mu rama a wuri da kuma lokacin da muka ga ya dace," in ji sanarwar rundunar sojin Isra'ila.

    "Muna cikin shirin ko-ta-kwana ta bangaren tsaro da na kai farmaki, za mu kare 'yan kasar Isra'ila. Wannan harin zai haifar da sakamako."

    Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kare ƴan kasarta kuma zuwa yanzu bayan hare-haren a cewarta babu wani babban ta'adi da suka yi illa raunika biyu da aka samu.

    Tun da farko Iran ta yi gargadi ga Isra'ila kada ta kuskura ta yi tunanin mayar da martani inda Iran ta ce hare-haren martani ne ga hare-haren Isra'ila

  4. Hotunan hare-haren roka da aka gani a Tel Aviv na Isra'ila

  5. Iran ta kai wa Isra'ila hare-haren makamai masu linzami

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce Iran ta kaddamar mata da hare-hare masu linzami.

    Sanarwar da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce hare-haren sun fito ne daga Iran.

    Iran ta tabbatar da kaddamar da hare-haren kan Isra'ila, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar IRNA ya tabbatar.

    Isra'ila ta bukaci ƴan ƙasarta su kasance cikin shiri tare da neman wurin fakewa idan har sun ji ƙara ta gargaɗi.

    Masu aiko da rahotanni sun ce an kakkaɓo wasu makaman a sararin samaniyar Jordan.

    Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce harin makamai masu linzami kusan 100 Iran ta harbo.

    Sai dai rahotanni sun ce Amurka ta taimaka wa Isra'ila wajen kakkaɓo makaman kafin isa Tel Aviv.

    Bayanai sun ce wasu makaman da Iran ta harbo sun faɗa yankunan Falasɗinawa

  6. Abin da China da Rasha da Turkiyya suka ce kan mamayar Isra'ila a Lebanon

    Farmakin da Isra'ila ta ƙaddamar ta ƙasa kan Hezbollah a kudancin Lebanon na ci gaba da fuskantar sukar wasu manyan ƙasashe inda suka yi kiran dakatar da ruru wutar yaƙi a yankin.

    China ta bayyana adawa da abin da ta kira "keta haƙƙin Lebanon a matsayinta ƙasa mai cin gashin kanta da kuma tsaronta," tare da bayyana damuwa kan rura wutar rikici a yankin da kuma kira ga Isra'ila ta dakata.

    Rasha ta yi allawadai da harin da Isra'ila ta kai wa Lebanon tare da kira ga Isra'ila ta dakatar da hare-hare da kuma gaggauta janye dakarunta daga yankin Lebanon da kuma neman hanyoyin lalama na kawo ƙarshen rikicin.

    Turkiyya ma ta yi kakkausar suka kan abin ta kira "yunƙuri na mamayar Lebanon" tare da kira ga Isra'ila ta gaggauta janye sojojin ba tare da ɓata lokaci ba.

    Ministan harakokin wajen Spain Jose Manuel Abares ya yi kira ga Isra'ila ta dakatar da farmaki ta ƙasa a kudancin Lebanon domin kaucewa bazuwar rikicin a yankin. Turkiyya ta jaddada cewa kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa da kare fararen hula ne kawai hanyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya a dukkanin ɓangarorin.

  7. Haƙƙinmu na kan wuyan gwamnonin jihohi ba Abuja kaɗai ba – MURIC

    Ƙungiyar da ke rajin kare muradun musulman Najeriya (MURIC) ta buƙaci ƴan Najeriya su mayar da hankalinsu kan gwamnonin jihohi maimakon mayar da hankali kacokan kan matsalolin ƙasar ga gwamnatin tarayya.

    A sanarwar da ta fitar albarkacin bikin cika shekara 64 da samun ƴancin Najeriya, ƙungiyar ta ce idan har ana son tabbatar da shugabanci nagari har sai an dinga sa ido kan gwamnonin jihohi.

    “A kullum ƴan Najeriya na taƙaita buƙatunsu ne kan gwamnatin tarayya yayin da kuma galibin buƙatun na kan wuyan gwamnonin jihohi. An rarraba haƙƙin tsakanin jihohi 36,” a cewar sanarwar da shugaban Muric, Ishaq Akintola ya fitar a ranar Talata.

    Ƙungiyar ta nuna cewa sa ido kan gwamnoni zai ƙara tabbatar da gaskiya da adalci wanda kuma zai tabbatar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya wanda zai tilasta wa gwamnoni sauke haƙƙin da ke wuyansu.

  8. Ba mu fara fafatawa da Hezbollah gaba da gaba ba tukunna - Rundunar sojin Isra'ila

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya amsa wasu tambayoyin manema labarai game da farmakin da suke kaiwa kan mayaƙan Hezbollah a Lebanon.

    "Zuwa yanzu ba fafatawa muke yi gaba da gaba da mayaƙan Hezbollah ba amma dai muna ɗaukar lamarin da muhimmanci," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa dakarun Isra'ila sun shirya tsaf don yaƙar ƙungiyar, amma shi ma ya ce Isra'ila ba za ta ƙarasa birnin Beirut ba, ko kuma wani gari a arewacin Lebanon.

    n tambaye shi game da abin da zai faru yayin "kutsen" a kwanaki masu zuwa.

    "Kuna cewa kutse ni kuma ina kiran sa samame," a cewarsa.

    "Wannan samame ne mai ɗan tsawo," kuma ya ƙara da cewa za mu kammala cikin sauri iya yinmu, za mu kawar da barazanar".

  9. Isra'ila ta lalata ramukan da Hezbollah ta gina

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta lalata ramukan karkashin kasa da dama na Hezbollah da ma'ajiyar makamanta.

    IDF ta shaida wa mazauna kauyuka fiye da 25 a kudancin Lebanon da su bar gidajensu nan take.

    Mai magana da yawun rundunar, Daniel Hagari, ya ce kudancin Lebanon na ci gaba da zama mafakar 'yan kungiyar Hezbollah.

    "Hezbollah ta mayar da kauyukan da ke makwabtaka da na Isra'ila wuraren aikin sojinsu, kuma sun shirya amfani da su don kai irin harin ranar 7 ga watan Oktoba," in ji Hagari.

    A cewarsa, hakan zai bai wa 'yan Isra'ila 60,000 damar komawa gidajensu da ke kusa da kan iyaka.

  10. Na ji koke-kokenku game da tsadar rayuwa - Tinubu

    Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankali a yau bayan bikin 'yancin kai a Najeriya har da zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu matasa suka yi a wasu biranen ƙasar.

    Da yake jawabi ga 'yanƙasa a safiyar yau, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce "ina sane da ƙalubalen da akasarinku ke shan fama da su a irin wannan lokaci".

    A cewarsa: "Gwamnatinmu na sane cewa da yawanku suna fama da hauhawar farashi da kuma neman aikin yi. Ina tabbatar muku an ji koke-kokenku."

    'Yan mintuna bayan fitowar masu zanga-zangar a yankin Utako na babban birnin ƙasar Abuja 'yansanda suka fara harba musu barkonon tsohuwa tare da tarwatsa su.

    An gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihar Legas da ke kudancin ƙasar, sai dai ita ma ba ta yi wani tasiri ba yayin da mutane ke cikin gidaje suna yin hutun Ranar 'Yanci.

  11. An soma yunkurin tsige mataimakin shugaban Kenya

    'Yan majalisar dokokin Kenya sun fara shirin tsige mataimakin shugaban kasar.

    Ana zargin Rigathi Gachagua da laifin cin hanci da rashawa, da taka rawa a zanga-a zangar tarzoma, da zagon kasa ga gwamnati da kuma siyasar kabilanci.

    Yunkurin tsige shi ya samo asali ne sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakaninsa da shugaban Kenya William Ruto.

    Masu aiko da rahotanni sun ce ana sa ran yunkurin tsige Mista Gachagua zai samu amincewar majalisar wakilai da ta dattijan kasar.

    A baya-bayan nan ne dai babbar jam'iyyar adawa ta hada kai da jam'iyyar shugaba Ruto bayan zanga-zangar da aka yi a watan Yuni. Mista Gachagua ya musanta aikata ba daidai ba.

  12. An baza jami'an tsaro a Legas saboda masu zanga-zanga

    A wurare da dama a Lagos cibiyar kasuwancin Najeriya, an baza jami'an tsaro domin jiran kota-kwana.

    Matasa dai sun kira a gudanar da zanga-zangar lumana a yau domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma abin da suka ce rashin iya gudanar da tattalin arziki karkashin gwamnatin Tinubu.

    Sai dai tabanin yadda suka yi ta yekuwa a shafukan sada zumunta, zanga-zangar ta yau ba ta yi armashi ba.

  13. Babu hada-hadar motoci a Abuja

    Manyan hanyoyin a cikin garin Abuja babban birnin Najeriya babu hada-hadar motoci sakamakon hutun da gwamnati ta bayar saboda bikin zagayowar ranar 'yancin kai.

    Kodayake wadansu matasa sun shirya zanga-zanga a yau din amma kuma bai yi tasiri ba.

    Sai dai kuma akwai hanyoyi da dama da 'yan sanda suka rufe domin tabbatar da tsaro.

    An girke 'yan sanda a manyan titunan Abuja musamman a unguwannin Wuse da Garki da Utako da kuma Jabi.

  14. 'Har yanzu ba a fara gwabzawa tsakanin Hezbollah da sojin Isra'ila ba a kan iyaka'

    Wani babban jami'in tsaro ya shaida wa BBC cewa dakarun sojan ƙasa na Isra'ila sun "matsa kusa sosai" da iyakar Lebanon amma har yanzu ba a "gwabzawa yaƙi ba".

    "Muna magana ne kan kai wa wuraren Hezbollah hari, waɗanda ke kusa da iyakar Isra'ila," a cewar jami'in.

    "Ba zan iya faɗar adadi ba, amma ba wai wani adadi ba ne mai yawa na dakarun da za su kai samame ta ƙasa," a cewarsa.

    Ya bayyana aikin a matsayin "ƙayyadajje" kuma ba irin wanda suke yi a Zirin Gaza ba.

  15. Na'urorin ankararwa sun yi ta kaɗawa a birnin Tel Aviv bayan harin Hezbollah

    Rahotonni sun ce na'urorin ankararwa sun yi ta karkaɗawa a babban Isra'ila Tel Aviv, inda aka ce an kakkaɓo aƙalla makamai uku a sararin saman birnin.

    Bayanan na zuwa ne bayan Hezbollah ta ce ta kai wa hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Isra'ila Mossad hari da makami mai linzami da ta kira "Fadi 4" a kusa da birnin na Tel Aviv.

    Kazalika, ta ce ta hari sansanin Glilot na sojan Isra'ila na leƙen asiri shi ma a Tel Aviv.

  16. Hezbollah ta kai wa dandazon sojin Isra'ila hari a arewacin ƙasar

    Hezbollah ta ce ta kai wa dakarun Isra'ila hari a garin Metula da ke kan iyakar ƙasar da Lebanon a safiyar Talata.

    An harba gungun makaman roka da misalin ƙarfe 08:05 (06:05 agogon Najeriya), kamar yadda wata sanarwa ta nuna, da kuma makaman atilare bayan minti 25.

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce hakan ya sa na'urorin ankararwa sun yi kaɗawa, tana mai cewa an kakkaɓo wasu daga ciki, wasu sun fashe, wasu kuma "sun faɗa a fili".

    A jiya IDF ta ayyana yankunan da ke kusa da Metula, da Misgav Am, da Kfar Giladi a arewacin Isra'ila a matsayin "kullallen yankin soja", abin da ke nufin an hana mutane shigarsa.

  17. Amurka ta jaddada goyon bayan Isra'ila a yaƙin da take da Hezbollah a Lebanon

    Sakataren tsaron Amurka Llyod Austin ya nuna goyon baya ga takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant kan dalilan kaddamar da hari ta kasa a Lebanon.

    Ma'aikatar tsaro ta ce mutanen biyu sun amince da bukatar ruguza duk wani wuri da ake kaddamar da hare-hare a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

    "Manufar hakan ita ce tabbatar da cewa Hezbollah ba ta samu damar sake maimaita irin harin da Isra'ila ta gani ba a yankunanta na arewaci.

    Wakilin BBC ya ce abin da wannan ke nufi shi ne Amurka tana bai wa Isra'ila cikakken goyon bayan kan hare-haren da take kaiwa a Lebanon.

    Sanarwar ta kuma ce Mista Austin ya jadadda gargaɗi ga Iran cewa za ta dandana kudarta muddin ta kaddamar da hari kai-tsaye a kan Isra'ila.

  18. 'Yansandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja

    'Yansandan Najeriya sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari a Abuja da safiyar yau.

    Dandazon matasa ne ɗauke da kwalaye da ƙyallaye suka taru a yankin Utako na tsakiyar babban birnin ƙasar suna yin waƙe-waƙen "yunwa muke ji", da "a kawo ƙarshen rashin shugabanci nagari".

    Babu daɗewa 'yansandan da ke wurin suka fara harba musu barkonon tsohuwa.

    Masu zanga-zangar sun tsara nuna ɓacin ransu ne a ranar da ake bikin cika shekara 64 da samun 'yancin kan Najeriya.

  19. Zan shirya taron ƙasa na matasa don ba su damar gina Najeriya - Tinubu

    Albarkacin Ranar 'Yancin Kai ta Najeriya, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa 'yanƙasa jawabi, inda a ciki ya bayyana abubuwa da dama kamar taron ƙasa da ya ce zai shirya domin matasa "da zimmar inganta makomar ƙasa".

    A cewarsa: "Jagorancinmu a yanzu yana ɗamfare da tunanin makomar da muke son gadar wa jikokinmu, kuma muna sane ba zai yiwu a gina rayuwarsu ta gaba ba ba tare da su a cikin aikin ba. A saboda haka ne nake farin cikin sanar da ku wani Taron Ƙasa Na Matasa."

    Ya ƙara da cewa taron wata dama ce da za a tattauna matsaloli da damarmaki da ke gaban matasan da su ne kusan kashi 60 na al'ummar ƙasa.

    "Taron zai taɓo muhimman batutuwa kuma ya bai wa matasanmu damar saka hannu wajen gina ƙasa. Taron na kwana 30 zai haɗa kan matasa na ƙasa baki ɗaya domin lalubo mafita game da batutuwa kamar ilimi, da aikin yi, da ƙirƙira, da tsaro, da kuma adalci."

  20. Isra'ila ta ƙaddamar da samame ta ƙasa kan Hezbollah a Lebanon

    Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da hare-hare ta kasa kan Hezbollah a Lebanon.

    Sojojin Isra'ila sun ce hare-haren nasu a yanzu sun hada da ta sama da kasa, inda kuma suke amfani da makaman atilare da bama-bamai.

    Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar IDF ta fitar ta ce suna kai farmaki ne kan maboyar Hezbollah a kauyuka da ke kusa da iyakarsu da Lebanon.

    Daya daga cikin hare-haren nasu ya fada a sansanin Falasdinawa da ke kusa da Sidon a kudancin Lebanon.

    Kafin wannan kuma, hare-hare ta sama da suke kai wa a Beirut na sake kamari bayan sun gargadi mazaunan yankin kudancin birnin su fice.

    Mataimakin shugaban Hezbollah Sheikh Qasssem ya jadadda cewa mayakansu a shirye suke domin tunkarar mamayar Isra'ila.