Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a duniya da sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 20/01/25
Taƙaitattu
- Biden ya yi wa Trump maraba da 'dawowa gida'
- Ƴanbindiga sun miƙa mutanen da suka yi garkuwa da su da bindigogi ga sojoji
- EFCC za ta yi gwanjon motoci kusan 900 da ta ƙwace
- Dole gwamnati ta kare Hamdiyya da launyanta daga barazana - Amnesty
- Manhajar TikTok ta koma aiki a Amurka
- Ƙungiyar su Shekarau ta yi watsi da matakin gwamnoni kan dokar haraji
- 'A watan Yuli za a fara amfani da sabuwar dokar haraji'
- Mun kashe ƴanbindiga ciki har da ɗangidan Bello Turji - Sojoji
- NAHCON ta sanar da kuɗin aikin hajjin 2025 a Najeriya
- Ƙungiyoyin Saudiyya sun dage kan Vinicius Jr, Manchester City na son Luiz
- Yadda aka cimma yarjejeniyar Gaza mai cike da tarihi
- Abin da ya sa India ke son alaƙa da Taliban
- Jami'an tsaro sun yi nasarar kashe ƴanbindiga a jihar Katsina
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar
Putin ya taya Donald Trump murnar shan rantsuwa
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya taya zababben shugaban Amurka, Donald Trump murna yayin da yake shan ranstuwa a yau.
A cikin wani bayani ta kafar talabijin, ga majalisar tsaro ta Rasha, Putin ya bayyana aiyar Trump ta tattaunawa da Rasha, da kuma bayanin da Trump ya yi a a baya na ƙoƙarin ganin ya kare afkuwar yaƙin duniya na uku.
"Tabbas muna maraba da matsayarsa kuma muna taya sabon shugaban Amurka murna kan karɓar mulki," in ji Putin.
Shugaban na Rasha ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da Trump game da yaƙin Ukraine.
Trump ya isa majalisa gabanin rantsar da shi a hukumance
Yanzu haka dai Donald Trump ya isa babban dakin taro na majalisar dokokin ƙasar, inda za a gudanar da bikin rantsar da shi na yau.
Ya yi tafiya kafada da kafada da shugaba mai barin gado Joe Biden.
Trump ya kama hanyar zuwa majalisar dokoki
Hotunan yadda aka shirya rantsar da Donald Trump
A wani lamari da ya saɓa wa al'ada, yau za a yi bikin rantsar da shugaban Amurka a ginin majalisar dokokin ƙasar.
Bisa tarihi, ana rantsar da shugabannin ne a waje a gaban ɗimbin jama'a da ke zaune a kan kujeru a lambun fadar shugaban ƙasa.
Amma yanayin matsanancin sanyi - da masu hasashen ke cewa zai kai -11C (12F) - a birnin Washington DC yana nufin cewa wannan karon bikin zai gudana ne a cikin ginin majalisar dokokin.
Biden ya yi wa Trump maraba da 'dawowa gida'
Joe Biden ya ce wa Donald Trump "Maraba da dawowa gida" yayin da ya isa Fadar White House cikin ƴan mintunan da suka gabata.
Shugabannin biyu ba su amsa tambayoyin manema labarai kafin ya shiga fadar White House ɗn ba.
Ganawar shan shayin za ta gudana ne a asirce, ba tare da manema labarai ba.
Al'adar ganawar shan shayi dai ta fara ne a shekarar 1837, da Shugaba Martin Van Buren da Andrew Jackson.
A shekarar 2021,Trump bai karbi baƙuncin Biden don shan shayi ba, domin a lokacin yana iƙirarin cewa shi ne ya lashe zaben na 2020.
Ƴanbindiga sun miƙa mutanen da suka yi garkuwa da su da bindigogi ga sojoji
Wasu jagororin ƴanbindiga sun mayar da bindigogi da waɗanda suka yi garkuwa da su a yankin Batsari da ke jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce bayan ƙara ƙaimi wajen matsa lamba da sojojin suka yi wa ƴanbindigar ne wasu jagororin ƴanbindiga, Abu Radde da Umar Black da suke harkokinsu a ƙananan hukumomin Batsari da Safana a jihar Katsina, suka mayar da bindigoginsu da kuma mutanen da suke riƙe da su
"Wannan na cikin ƙoƙarin da jami'anmu suke yi na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar."
Taron miƙa mutanen ya samu halartar wakilan rundunar sojin da sauran masu ruwa da tsaki.
Sai dai rundunar na nanata cewa miƙa bindigogin ba sulhu aka yi ba, sannan ta ce an miƙa bindigogin ga ofishin sojin da ke Katsina.
EFCC za ta yi gwanjon motoci kusan 900 da ta ƙwace
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) za ta yi gwanjon motoci da dama da ta ƙwace a faɗin ƙasar.
Hukumar ce ta sanar da hakan, inda bayanin ya nuna cewa za ta yi gwanjon motoci guda 891, ga masu buƙata.
Za a yi gwanjon ne a wurare 16 a jihohin Edo da Kwara da Sokoto da Kaduna da Legas da Kano da kuma Abuja.
Hukumar, wadda aka kafa a shekarar 2003, ta yi ƙaurin suna wajen kame tare da ƙwato kadarori a hannun masu laifi.
EFCC, a kai-a kai kan sanar da kai samame a maɓuyar masu aikata damfara ta intanet, inda taƙan ƙwato motoci masu tsada da kwamfutoci da kuma wayoyi.
Jamus za ta cigaba da ayyukan agaji a Nijar
Ƙasar Jamus za ta koma harkoki da aikace-aikacen tallafi a Jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar Africa Intelligence da ke Paris ta ruwaito.
Kafar ta ruwaito cewa a ranar 20 ga Janairu cewa Jamus za ta tattaunawa da Nijar domin cigaba da harkokin da take yi a ƙasar, kusan shekara ɗaya da rabi bayan ƙasashen biyu sun raba-gari.
"Wakilan ma'aikatar haɗaka domin bunƙasa tattalin arziki da ci gaba za su isa birnin Niamey a wannan watan, ƙarƙashin jagorancin wakilin ma'aikatar na yankin sahel da Afirka ta yamma, Berhard Braune domin tattaunawa hanyoyin da Jamus za ta koma domin cigaba da ayyukanta na agaji a Jamhuriyar Nijar.
Jamus ta dakatar da aikin agaji a ƙasar ne a watan Yulin 2023 bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
Kafar ta ƙara da cewa an samu jan-ƙafa ne kan dawo da yarjejeniyar harkokin tsakanin ƙasashen biyu saboda tsamin dangantaka da ke tsakanin Nijar da tarayyar Turai.
Dole gwamnati ta kare Hamdiyya da launyanta daga barazana - Amnesty
Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta yi bincike tare da tabbatar da kare lafiyar Hamdiyya Sidi Shariff da lauyanta Abba Hikima daga barazana ga rayuwarsu.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya fitar, ya ce, "yanzu haka bayan fuskantar shari'a saboda ta yi amfani da ƴancinta na tofa albarkacin baki, Hamdiyyya Sidi Shariff da lauyanta Abba Hikima suna fuskantar barazana ta hanyar kiraye-kirayen waya da fuskantarsu da wasu ɓatagari ke yi da ma masu ikirarin cewa su 'jami'an sirri' ne."
Sanarwar ta ƙara da cewa dole lauyanta sai da ya nemi kariyar ƴansanda a zaman kotun da aka yi na ƙarshe saboda fargabar da suke ciki, "wanda hakan ya sa zuwansu kotun ke da wahala."
Hamdiyya na fuskantar shari'a ne saboda zargin ɓata sunan gwamnan jihar Sokoto, lamarin da ya ɗauki hankalin mutane da dama.
Ƴanjarida sun koka da gwamnatin Nijar
A jamhuriyar Nijar ƴan jarida ƙasar ne ke kokawa da halin da aikin jarida yake ciki duba da yadda hukumomin mulkin sojin ƙasar ke ɗaukar matakan tsaurara yin aikin.
Lamarin baya-bayan nan dai ya biyo bayan wani labari da tashar talabijin na Kanalturo ta yi na auna ƙoƙarin ministocin gwamnatin ƙasar.
Shirin ne ake tunanin ya sa hukumomin ƙasar sun ɗauki matakin dakatar da kafar talabijin ɗin na wani lokaci, sannan daga bisani suka kama editan gidan talabijin ɗin.
Manhajar TikTok ta koma aiki a Amurka
Manhajar TikTok ta koma aiki a ƙasar Amurka bayan wani ɗan lokaci da aka sanar da dakatawa.
Kafar ta sada zumunta, wadda ta China ce, ta gode wa Donald Trump, wanda ya ce zai yi ƙokari ya warware batun da ya jawo matsalar tun a farko.
Sama da Amurkawa miliyan ɗari da saba'in ne ke amfani da TikTok.
Kamfanin ya ce zai yi aiki tare da Trump don samar da mafita ta dogon lokaci don ci gaba da kasancewa a Amurka.
Wakiliyar BBC ta ce kamfanin Bytedance da ya mallaki TikTok ya musanta zargin satar bayanai yana baiwa China, kuma ya ɗauki wasu matakai don nuna hakan, ciki har da mayar da shalkwatar kamfanin zuwa Singapore.
Tun da farko, Mista Trump ya ce zai ba da umarnin zartarwa lokacin da ya hau kan karagar mulki a yau domin ba TikTok damar ci gaba da aiki a Amurka.
Ƙungiyar su Shekarau ta yi watsi da matakin gwamnoni kan dokar haraji
Ƙungiyar LND mai fafutukar wanzar da dimukraɗiyya a arewacin Najeriya ta yi watsi da matakin gwamnonin arewacin ƙasar na amincewa da sabuwar dokar harajin da ake ta taƙaddama a kanta.
Ƙungiyar ta ce har yanzu, ba ta gamsu da tsarin da aka yi na rabon harajin VAT dai dai da gudummawar da kowacce jiha ke bayarwa ba, kuma idan aka tafi kan matsayar da gwamnonin suka cimma karshe arewacin kasar ne zai faɗa cikin matsala.
Alhaji Ladan Salihu, kakakin ƙungiyar ta LND, ya ce '' an kashe maciji ne ba a fille kansa ba, mutane miliyan ɗari da talatin da bakwai ko fiye a Najeriya su na cikin tsananin talauci, miliyan tamanin da bakwai daga arewa su ke''
Sojoji sun kashe masu haƙar ma'adinar ba bisa ƙa'ida ba a Ghana
Sojoin ƙasar Ghana suka ce sun kashe aƙalla masu haƙo ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba guda takwas.
Sojojin sun ce sun kashe mutanen a wani yanki da ake haƙo ma'adinan da yankin Ashanti, bayan sun yi musayar wuta, kamar yadda sanarwar sojoji ta nuna, sannan ta ƙara da cewa mutanen ne suka buɗe wuta kan sojojin, kafin suka mayar da martani.
Tuni Shugaban Ƙasa Ghana John Mahama ya bayar da umarni a gabatar da bincike kan lamarin.
Mutuwar tasu dai ta janyo zanga-zanga, a birnin Obuasi, inda aka ƙona motoci.
Ana samun ƙaruwar ayyukan haƙar ma’adanai ta haramtantun hanyoyi a Ghana, wanda ake dangantawa da matsin tattalin arziki.
SERAP ta buƙaci Trump ya mayar wa Najeriya kadarorinta da aka ɓoye a ƙasarsa
Ƙungiyar SERAP mai rajin yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya gaggauta zaƙulowa da mayar wa Najeriya ƙaddarorin ta da jami’ai suka sata, suka kuma tara a Amurkan.
SERAP ta ce dole ne sabuwar gwamnatin Amurkan ta tabbatar an bi tsauraran matakan gaskiya da adalci wajen mayar wa Najeriya da kuɗaɗen nata.
Ta kuma yi kira ga Trump ya sanya ido domin ganin an yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata.
Mun kashe ƴanbindiga ciki har da ɗangidan Bello Turji - Sojoji
Dakarun Najeriya da suke aikin soji na musamman Fansan Yamma sun ce sun kashe ƴandinga da dama, ciki har da ɗan cikin Turji a wani samame da suka kai a sansanin ɗanbindigar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hedkwatar taron Najeriya, Edward Buba ya fitar, inda ya ce, "a ranar 17 ga Janairu, dakarun Fansan Yamma sun kutsa dazukan da ke yankin Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da Chindo, inda suka kashe gomman ƴanbindiga, sannan suka kashe ɗan cikin Bello Turji a Fakai, inda yake ɓoyewa."
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun samu ƙashe ƴanbindiga da dama, da ɓarnata ma'ajiyarsu, "sannan sun ceto wasu waɗanda Bello Turji ya yi garkuwa da su, bayan ya tsere."
Sanarta ta ce sojojin sun kai wani samamen a sansanin wani ɗanbindigar mai suna Idi Mallam, "inda sojoji suka kashe ƴanbindiga 3, da kama mutum 3 da ake zargi da taimakon ƴanbindiga, tare da ƙwato wasu makamai da dabbobin da suka sace."
A ƙarshe Buba ya ce sojojin za su cigaba da fatattarkar ƴanbindigar a ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
'A watan Yuli za a fara amfani da sabuwar dokar haraji'
Shugaban kwamitin gyare-gyaren haraji ta Najeriya, Taiwo Oyedele, ya ce ƙudurin haraji da ke gaban majalisar ƙasar zai zama doka kafin rubu'in farko na shekarar nan ta 2025 na ƙare.
Dokar dai ta ɗauki hankalin mutane ƙasar, lamarin da ya jawo tsaiko wajen tabbatar da shi a majalisar, musamman bayan majalisar tattalin arzikin ƙasar ta buƙaci a dakata.
Sai dai a makon jiya ne ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta amince da ƙudurin, amma tare da yin wasu kwaskwarima da ta ce zai magance abubuwan da ake fargaba.
Da yake jawabi a wajen wani taro mai taken The Platform, Oyedele ya ce za a fara amfani da dokar ne a watan Yulin bana.
"Muna sa ran za a amince da ƙudurorin haraji kafin ƙarshen rubu'i na farko na wannan shekarar, inda za mu ba masu biyan haraji lokaci domin su fara shiri kafin ya fara aiki a watan Yuli," in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A game da cire tallafin man fetur, Oyedele ya ce yana cikin manyan matakai masu muhimmanci da aka ɗauka a Najeriya.
An yi jana'izar aƙalla mutum 83 da suka rasu a fashewar tankar Suleja
Gwamnatin tarayya ta buƙaci a mayar da waɗanda suke jinya sakamakon fashewar tankar man fetur ta Suleja zuwa manyan asibitoci domin a kula da su da kyau.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ya fitar bayan ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya zuwa inda gobarar ta auku, inda ya ce lamarin ya matuƙar ɗaga hankalin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Gobarar wadda ta auku a garin Dikko da ke ƙaramar hukumar Gurara a jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 83, sannan wasu na asibiti, a daidai lokacin da ake neman wasu.
Aƙalla mutum 55 da suka samu raunuka a hatsarin na kwance a babban asibitin Suleja da babban asibitin Sabon Wuse da cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ne, wanda hakan ya sa ministan ya buƙaci a kwashe su, a sauya musu asibitoci.
A ƙarshe ministan ya ce gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti na musamman domin duba musabbabin yawaitar goara a sanadiyar fashewar tanka a Najeriya.
Trump ya ce zai ɗauki matakai manya a ranarsa ta farko a mulki
Donald Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa zai rattaba hannu kan wasu jerin umarni na zartarwa a ranarsa ta farko a matsayin shugaban Amurka.
Daga cikin matakan da ya ce zai akwai waɗanda za su shafi shige da fice ba bisa ƙa'ida ba, da daƙile ƙa'idojin muhalli da kuma kawar da manufofin bambance-bambance daga aikin soja.
A lokacin da yake jawabi ga ɗimbin magoya bayansa, a wani gangami a birnin Washington a jajibirin rantsar da shi karo na biyu, Mista Trump ya kuma yaba da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Gaza, yana mai cewa hakan ta faru ne kawai albarkacin nasararsa.
Shi ma hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya hau duro ya yi jawabi a taƙaice yana mai cewa martaba da buwayar Amurka na daf da dawowa a idon duniya.
Motocin kayan agaji na ta zirya a Zirin Gaza
Yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni a Gaza ta shiga rana ta biyu bayan shafe watanni goma sha biyar ana yaki.
Musayar fursuna ta farko ta yi nasara, inda Hamas ta saki wasu Isra'ilawa guda uku da aka yi garkuwa da su, kafin a sako Falasdinawa 90 daga gidan yari a yammacin gabar kogin Jordan.
Jama'a da dama sun kewaye motocin bas din da suka dakko Falasdinawan da aka saki suna shewa da murnar sakin mutanen da yawancinsu mata ne.
Wadda ta fi fice a cikinsu ita ce Khalida Jarrar, wata yar gwagwarmayar yankin.
A gefe guda yanzu haka sama da motocin agaji 500 sun shiga zirin Gaza.
Suma mutane 3 yan Isra'ilar da Hamas ta saki sun koma gida, har ma sun hadu da yan uwansu a asibitin da ake kula da su.
An ga matan cikin hawaye suna rungume da 'yan uwansu.
A wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wutar, za a sake sakin wasu Isra'ilawa 30 da aka yi garkuwa da su cikin makonni shida masu zuwa.