Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 14/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 14/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Muhammed

  1. Gwamnan Enugu ya koma APC bayan ficewa daga PDP

    Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya fice daga jam'iyyarsa ta PDP tare da komawa APC mai mulkin Najeriya.

    Mista Mbah ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya shirya a fadar gwamnanatin jihar da ke birnin Enugu.

    “Bayan dogon lokaci da muka ɗauka muna nazari, a yau mun yanke shawarar ficewa daga PDP tare da komawa APC,'' kamar yadda gwamnan ya bayyana.

    Mbah ya ce ya koma APC ne saboda kyawawan manufofin jam'iyyar da ayyukan ci gaba da take samarwa a Najeriya da ma jiharsa ta Enugu.

    Gwamnan ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa komawarsa APC za ta samar wa jihar ƙarin damarmaki da ci gaba.

    Taron ya samu halartar manyan ƴansiyasar jihar da suka haɗa da mataimakin gwamnan jihar, Barr Ifeanyi Ossai da tsoffin gwamnonin jihar, Sullivan Chime da Rt Hon. ifeanyi Ugwuanyi,da Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Chief Ken Nnamani, da tsoffin ƴanmajalisar tarayya daga jihar da kuma masu ci, da shugaban majalisar dokokin jihar da shugaban jam'iyyar APC na jihar, da sauran muƙarraban gwamnatinsa, kamar yadda mataimaki na musamman ga gwamnan kan kafofin yaɗa labarai, Dan Nwomeh ya wallafa a shafinsa na X.

    Dama dai tun jiya wasu daga cikin kwamishinonin gwamnan suka fice daga PDP tare da komawa APC.

  2. Zan yi shawara game da kafa ƙasar Falasɗinu - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai yi shawara ''kan abin da yake ganin ya dace'' game da yiwuwar amincewa da kafa kasar Falasɗinu a matsayin masalaha a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Shugaba Trump ya ce zai yi aiki tare da sauran ƙasashen duniya game da batun.

    Mista Trump ya bayyana hakan ne ga ga manema labarai a kan hanyarsa ta komawa Amurka daga ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya ranar Litinin, domin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Gaza.

    A baya-bayan nan dai ƙasashen duniya da dama sun yi ta kiraye-kiyaren amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu musamman a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a Amurka.

    Ko a ranar Litinin ma yayin da Trump ke tsaka da jawabi a majalisar dokokin Isra'ila, wani ɗanmajalisa ya buƙace shi ya amince kafuwar ƙasar Falasdinu, lamarin da ya sa nan take jami'an tsaro suka yi gaggawar fitar da shi daga zauren.

  3. PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwarta karo na 103

    Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ɗage babban taron kwamitin zartarwarta da aka tsara yi ranar Laraba 15 ga watan Oktoban 2025.

    Cikin wata sanarwar da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta ɗauki matakin ne a taron gaggawa da kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya yi a Abuja ranar Litinin.

    Jam'iyyar ta ce ta ɗage taron zuwa wani lokaci da za ta sanar a nan gaba, don haka ta buƙaci mambobinta su jira sanarwa ta gaba game da sabuwar ranar taron.

    Jam'iyyar PDP dai na fuskantar matsin lamba, sakamakon yawan ficewar mambobinta zuwa APC mai mulki.

    Ko a baya-bayan nan ma an yi ta raɗe-raɗin ficewar wasu gwamnoninta biyu zuwa APC mai mulki.

  4. Majalisar Dokokin Najeriya na son a yi zaɓen shugaban ƙasa a watan Nuwamban 2026

    Majalisar Dokokin Najeriya ta bayar da shawarar sauya lokacin gudanar da zaɓen shugaban ƙasar zuwa watan Nuwamban 2026 maimakon Fabrairun 2027.

    Shawarar na ƙunshe cikin daftarin ƙudurin dokar zaɓe ta 2025, da aka gabatar ranar Litinin a lokacin zaman sauraron jin ra'ayin jama'a na haɗin gwiwa tsakanin kwamitocin zaɓe na majalisun dokokin biyu da aka yi a Abuja.

    Ƙudurin, ya nemi a sauya dokar zaɓe ta 2022 tare da amincewa da sabuwar dokar zaɓe ta 2025.

    A cewar daftarin, ''za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na gwamnoni ƙasa da kwana 185 kafin ƙarewar wa'adin waɗanda ke riƙe da muƙaman''.

    Ƴanmajalisar sun ce manufar sauyin shi ne tabbatar da kammala duka shari'o'in ƙorafe-ƙorafen zaɓe kafin ranar 29 ga watan Mayun 2027 da za a rantsar da shugaban ƙasa da gwamnoni.

  5. Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirarin samun nasara a zaɓen Kamaru

    Jagoran adawar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirari samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi.

    Cikin wani bidiyo da ya fitar, da tsakar daren da ya gabata, Mista Bakary ya gode wa al'ummar Kamaru kan ''yarda da samar da canji'' da ya ce sun yi a ƙasar.

    Iƙirarin nasa na zuwa a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan.

    “Ina son bayyanawa cikin girmamawa da nutsuwa cewa al'ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu,'' in ji Bakary.

    Ya kuma alƙawarta wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar.

    “Haƙiƙa wannan nasara ba tawa kaɗai ba ce ni kaɗai, ta kowa ce,'' in ji shi.

    Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan cikin gida na ƙasar, Paul Atanga Nji ya nanata haramcin iƙirarin nasara daga ɗaiɗaikun ƴantakara tare da wallafa abin da ya kira ''haramtaccen'' sakamakon zaɓe.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa, kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kada ku manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa