Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 14/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 14/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Isiyaku Muhammed

  1. Faransa ta dakatar yunƙurin gyara shekarun ritaya

    Faransa

    Asalin hoton, Reuters

    Fira Ministan Faransa, Sebastien Lacornu, ya sanar da dakatar da shirin yi wa tsarin fansho na kasar kwaskwarima wanda ya kara shekarun yin ritaya daga aiki zuwa 64 wanda ya shugaba Macron ya bulo da shi shekara biyu da suka gabata.

    Jam'iyyar Socialist wadda ta sanya shi a matsayin abinda za ta fi ba fifiko , domin ta goyi bayan gwamnatin da ba ta da rinjaye.

    A yanzu ta ce ba za ta goyi bayan kudurin yanke kauna da zaa kada a ranar Alhamis mai zuwa ba, wanda jam'iyyu masu tstsauran ra'ayin kawo sauyi da masu ra'ayin rikau suka gabatar.

    Wakilin BBC ya ce shirin yi wa tsarin fansho na kasar garambawul na cikin muhiman sauye-sauyen shugaba Macron a wa'adinsa na biyu kan mulki.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaba Macron ya sake nada Mist Lacornu a matsayin firaministan bayan kwanaki hudu da ya yi murabus.

  2. Majalisa ta bayyana dalilin kafa kwamitin bincike kan zargin kashe kiristoci a Najeriya

    NIGERIA SENATE

    Asalin hoton, NIGERIA SENATE

    Majalisar dattawan Najeriya ta yi ƙarin bayani kan dalilanta na kafa wani kwamitin mutum 12 da zai ba ta shawara kan yadda za ta mayar da martani a game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa kiristoci a Najeriya, lamarin da ya ja hankali tare da sanya damuwa a duniya.

    Majalisar dattawan ta ce ta ɗauki matakin ne a yayin wani zaman sirri da ta gudanar a yayin zaman majalisar na yau Talata, inda aka tattauna kan kalaman da wani ɗan majalisar Amurka ya yi cewar ana aikata kisan kiyashi kan kiristocin da ke a wasu sassan Najeriyar.

    A yayin zaman dai wasu daga ciki sanatocin sun yi ta kiraye-kiraye wajen ganin an bi matakin diflomasiiya wajen ganin an shawo kan lamarin tare da warware zare da abawa don kar hakan daga shafar dangantakar ƙasashen da Najeriya.

    Dr. Mohammad Tahir Monguno, shi ne mai tsawatarwa a majalisar dattawan ta Najeriya kuma daya daga cikin 'yan kwamitin ya ce an kafa kwamitin ne domin tattara bayanan da za su gabatar wa majalisar dattawar Amurka.

    ''Mun tattauna ne a majalisar dattawa game da kisan kiyashin da ake zargi ana yi wa kiristocin Najeriya. Daga majalisar Amurka aka kawo mana rahoton cewa ana cin zarafin kiristoci a Najeriya kuma ana musu kisan kiyashi. Shi ya sa muka kafa kwamiti domin mu gano bakin zare.''

    Ya ce za su yi aiki tuƙuru domin warware matsalar, domin a cewarsa, "idan Amurka ta yi doka a kai, za a iya saka wa Najeriya takunkumi, kuma hakan zai shafi tattalin arzikin ƙasarmu."

    Ya ƙara da cewa za su kafa wani kwamiti na musamman da zai je Amurka domin ya fahimtar da majalisar "cewa zargin ba haka ba ne, domin an fi kashe musulmi a matsalolin tsaron Najeriya," in ji shi.

  3. Hamas ta san ba wasan yara nake yi ba - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dole ne Hamas ta ajiye makami ta rungumi zaman lafiya bayan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

    Trump ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a fadar gwamnatin Amurka bayan ganawarsa da shugaban ƙasar Argentina, Javier Milei.

    Da aka tambaye shi ko zuwa yaushe yake tunanin Hamas za ta ajiye makami, da kuma ko yana tabbacin hakan zai faru, sai ya ce yana da tabbaci.

    Ya ce, "za su ajiye makami, sun faɗa da kansu cewa za su ajiye makami. Amma idan sun ƙi ajiyewa, za mu raba su da makaman da ƙarfi da yaji," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa jami'an Amurka sun tattauna da Hamas, kuma ƙungiyar ta shaida musu cewa za ta miƙa makamanta.

    "Hamas ta san cewa ba wasa nake yi ba," in ji shi.

  4. Yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki na karuwa a arewacin Najeriya - MSF

    MSF

    Asalin hoton, MSF/Reuters

    Kungiyar agaji ta likitoci ta MSF ta yi gargadi kan karuwar yaran da ba sa samun abinci mai gina jiki a arewacin Najeriya.

    Ta ce ta yi wa yara fiye da dubu dari uku magani a jihiho bakwai a bana. Kungiyar ta kara da cewa lalurar na shafar lafiyar kwakwalwar yara inda wasu daga cikinsu sun kebe kansu, ba sa son su yi mu'amala da mutane.

    Wasu jihohin arewacin Najeriya sun shafe tsawon shekaru suna fama da tashin hankali, abin da ya haifar da karancin abinci tare da raba miliyoyi da muhallansu.

  5. An tashi wasa: Najeriya 4 - 0 Benin

    An tashi wasan na Najeriya da Benin, inda Super Eagles ta lallasa Benin da ci hudu da nema.

    Yanzu Najeriya na da maki 17, Afirka ta Kudu kuma da ta doke Rwanda da ci uku da nema ta kare da maki 18.

    Yanzu dai Afirka ta Kudu ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya, inda ita kuma Najeriya ke jiran sauran sakamakon wasannin domin samun gurbin buga wasannain raba-gardama.

  6. Isra'ila ta taƙaita shigar da kayan agaji Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Isra'ila sun ce gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar taƙaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza, sannan za ta ɗan dakata ta buɗe bakin iyakar zirin daga Rafas.

    Isra'ila ta ce ta ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ta kira jan ƙafa da a cewarta Hamas ke yi wajen mayar da sauran gawarwaki da ke hannunsu.

    Zuwa yanzu dai gawarwaki huɗu kawai Hamas ta miƙa, sannan akwai rahotannin da ke cewa ƙungiyar za ta miƙa wasu gawarwakin guda huɗu, amma ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske.

    Shi ma Donald Trump ya yi ƙorafi, inda ya buƙaci Hamas ta mayar da gawarwakin "kamar yadda aka yi alƙawari," in ji shi.

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce wasu gawarwakin sun ɓace, kuma zai yi wahala a gano su.

  7. Osimhen ya ƙara ta uku. Najeriya 3 - 0 Benin

    Najeriya ta ci ƙwallo ta uku, inda yanzu Osimhen ya zura ƙwallo rigis.

    Yanzu haka ana minti 53 a wasa.

  8. Hutun rabin lokaci: Najeriya 2 - 0 Benin

    An tafi hutun rabin lokaci Najeriya na doke Benin da ci biyu da nema.

    A ɗaya ɓangaren kuma, Afirka ta Kudu na doke Rwanda da ci biyu da nema ita ma.

    A yanzu haka dai Afirka ta Kudu na da maki 18, Najeriya na da 17, ita ma Benin 17, sai dai na Najeriya ta fi Benin yawan ƙwallaye.

  9. Najeriya 2 - 0 Benin

    Najeriya ta zura ƙwallo ta biyu a wasanta da Benin na neman samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

    Ɗanwasa Victor Osimhen ne ya zuwa ƙwallo na biyu bayan Chukwueze ya jefa masa.

    Osomhen ya ci ƙwallo biyu ke nan.

  10. Kotu a Japan ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum da ya kashe mutane huɗu

    Wata kotu a yankin Nagano da ke tsakiyar Japan ta yanke wa wani mutum mai suna Masanori Aoki hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin kashe maƙwabtansa biyu da jami’an ‘yan sanda biyu, lamarin da ya girgiza ƙasar shekaru biyu da suka gabata.

    Kotu ta ƙi amincewa da hujjar lauyansa da ke cewa ya kamata a ba shi hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda yana fama da matsalar tabin hankali da cutar ƙwaƙalwa ta schizophrenia.

    Bayan wannan mummunan lamari, gwamnatin Japan ta ƙara tsaurara dokokinta kan mallakar makamai da takobi.

    Duk wanda ke son siyan bindiga a Japan dole ne ya fuskanci gwaji mai tsauri da kuma binciken lafiyar kwakwalwa kafin a ba shi izini.

  11. Najeriya 1-0 Benin

    Dan wasan Najeriya Victor Osimhen

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dan wasan Najeriya Victor Osimhen

    Najeriya ta shiga gaba a karawar da take da Benin na neman zuwa gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya

    Victor Osimhen ne ya ci wa Najeria ƙwallo a minti uku bayan take wasa.

    Najeriya na bukatar kara cin ƙwallaye, sannan za ta jira sakamakon Afirka ta Kudu da Rwanda.

  12. Asibitin Gaza ya ce sojojin Isra'ila sun kashe mutum 7

    Gaza

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Asibitoci a Gaza sun ce mutum bakwai ne sojojin Israila suka kashe a lokacin da suka bude wuta da tsakar dare.

    Sojojin Israila sun ce alamari ya faru ne a wata unguwa da ke kwaryar birnin Gaza, kuma sun bude wuta ne bayan da wasu suka yi kokarin tsallaka bangarensu kuma sun ki tsayawa.

    Kakakin Hamas ya bayyana alamarin a matsayin karya kaidojin yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

    A wani labarin kuma mayakan hamas sun yi mussayar wuta da wasu kungiyoyi masu rike da makama da ke gaba da kungiyar, yayin da take kokarin sake tabbatar da ikonta a GAZA.

  13. DR Congo da ƴan tawayen M23 sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya

    M23

    Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ƴan tawayen M23 sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ake ganin mataki ne mai muhimmanci wajen kawo ƙarshen rikicin da ake ci gaba da gwabzawa a gabashin ƙasar.

    Yarjejeniyar ta kafa wani kwamiti da ya ƙunshi wakilai daga ɓangarorin biyu domin sa ido kan karya dokar tsagaita wuta.

    Wannan mataki na daga cikin sharuɗɗan da ake buƙata kafin fara tattaunawar cikakken yarjejeniyar zaman lafiya.

    Tun a watan Agusta ne DRC da M23 – waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda – suka gaza kammala yarjejeniyar zaman lafiya kamar yadda aka tsara.

    Ƴan tawayen M23 sun mamaye manyan yankuna a gabashin Kongo tun farkon wannan shekarar yayin da suka ƙaddamar da sabbin hare-hare.

  14. Labarai da dumi-dumi, Sojojin Madagascar sun ce sun karɓe mulkin ƙasar

    Sojojin Madagascar

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Rundunar sojin Madagascar ta ce ta karɓe mulkin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Shi ma kamfanin dillancin labari na AFP ya ruwaito wani soja mai muƙamin Kanal na cewa sojoji sun karɓe mulki.

    Kanal Michael Randrianirina, shugaban rundunar sojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasar, ya karanta sanarwar karɓe mulkin a gidan radion ƙasar.

    Yana mai cewa ''mun karɓe mulki daga yanzu'', kamar yadda ya karanta.

    A ƙarshen mako ne rundunar da ke tsaron fadar shugaban ƙasar ta juya wa shugaban baya, ta hanyar shiga zanga-zangar masu neman ya sauka daga mulki.

  15. Majalisar Dokokin Madagascar ta kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar

    Shugaban Madadascar

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan majalisar dokokin Madagascar sun kaɗa ƙuri'ar tsige shugaban ƙasar, Andry Rajoelina.

    Mambobin majalisar 130 ne suka zaɓi ''tsigewa'', yayin da ƙuri'a ɗaya ta zama babu rubutun komai a kanta.

    Mista Rajoelina dai ya yi Allah wadai da ƙuri'ar tsige shin da majalisar dokokin ta kaɗa.

    A yanzu ana jiran majalisar tsarin mulkin ƙasar ta amince da ƙuri'ar da majalisar ta kaɗa.

  16. Shugaban Madagascar ya ce ya rusa majalisar dokokin ƙasar

    Shugaban Madagascar na jawabi

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya ce ya rusa majalisar dokokin ƙasar, duk da cewa ba a san halascin matakin nasa ba.

    Tuni dai Mista Rajoelina ya fice daga ƙasar yayin da ya dage ba zai yi murabus ba.

    Sanarwar tasa na zuwa ne gabanin yunƙurin ‘yan adawa na tsige shi, saboda ya yi watsi da aikinsa na shugaban ƙasa.

    Rahotonni na cewa alummar ƙasar na son shugaban ƙasar da zai saurari kokensu.

    Shugaba Rajoelina dai ya tsere daga ƙasar zuwa wani wuri da ba a sani ba, yana mai cewa yana fargabar rayuwarsa bayan da zaratan sojojin ƙasar suka shiga zang- zangar nuna ƙin jinin gwamnati da ke gudana ƙarƙashin jagorancin matasa.

    Rahotanni daga ƙasar na cewa suma ƴansandan ƙasar a yau sun mara mu su baya.

  17. An lalata fiye da kashi 80 na gine-ginen Gaza - MDD

    wani mutum

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ci gaban ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) - wadda ke auna irin ɓarnar da aka yi a Gaza - ta ce an ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen yankin.

    UNDP ta ce a Birnin Gaza kaɗai an lalata fiye kashi 92 cikin 100 na gine-ginen birnin.

    Kakakin hukumar ya bayyana rugujewar gine-ginen da ''mummuna''.

    Hukumar ta ƙiyasta cewa akwai aƙalla tan miliyan 55 na ɓaraguzai da ke buƙatar sharewa a yankin.

    UNDP ta ce tuni ta fara aikin share ɓaraguzan yankin, amma ɓarazanar abubuwan fashewa da aka danne na kawo musu cikas a aikin.

    Hukumar ta ƙara da cewa akwai gawarwakin mutanen da za a iya ganewa da adanawa da ake ta tonowa yayin aikin.

    Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai sun ƙiyasta buƙatar dala biliyan 70 domin sake gina Gaza.

  18. Sanata Kaila daga Bauchi ya koma APC bayan ficewa daga PDP

    Sanata Kaila sanye da fararen tufafi da farar hula

    Asalin hoton, Sanato Samaila Kaila

    Ɗanmajalisar dattawan Najeriya mai wakiltra mazaɓar Bauchi ta Arewa, Samaila Kaila, ya fice daga jam'iyarsa ta PDP tare da komawa APC mai mulkin Najeriya.

    Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a lokacin zaman majalisar na yau Talata.

    A lokacin da yake karanto wasiƙar ficewar da ɗanmajalisar ya aike masa, Sana Kaila ya bayyana matsalolin cikin gida da PDP ke fama da su a matsayin dalilin ficewar tasa.

    “Matsalar da PDP ke ciki na kawo min tarnaƙi wajen sauke nauyin al'ummata da kundin tsarin mulki ya ɗora min,'' kamar yadda wasiƙar ta nuna.

    Sanata Kaila ya ce sauye-sauyen Shugaba Tinubu ne suka ja ra'ayinsa wajen komawa jam'iyyar APC mai mulki.

    Jihar Bauchi da Sanata Kaila ya fito na daga cikin jihohin da jam'iyyar PDP ke mulki.

    Sanarwar sauya shekar tasa na zuwa ne sa'o'i bayan da gwamnan jihar Enugu ya sanar da ficewa daga PDP tare da komwa APC shi da kusan duka muƙarraban gwamnatinsa da wasu jiga-jigan ƴansiyasar jihar.

  19. 'Ba lallai a samo wasu gawarwakin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su ba'

    Wani mutum na zaune a saman ɓaraguzai

    Asalin hoton, .

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce gano ragowar gawarwakin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa a Gaza zai zama da ''gagarumin ƙalubale', saboda yadda yabkin ya cika da ɓaraguzai.

    ICRC ta ce akwai yiwuwar cewa ba za a iya gano wasu daga ciki ba.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta tabbatar da gawarwaki bakwai da Hamas ta miƙa musu a ranar Litinin.

    Hukumar lura da gine-gine ta Amurka ta yi ƙiyasin cewa akwai aƙalla tan miliyan 55 na ɓaraguzai da ya kamata a share a Gaza, yayin da aka ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen yankin.

    shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan ya ce ya yi imanin cewa za a samar da kuɗin sake gina Gaza.

  20. MSF ta yi gargaɗin ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki a arewacin Najeriya

    Ƙungiyar Agajin Likitoci ta MSF ta yi gargaɗin samun ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki tsakanin ƙananan yara a arewacin Najeriya.

    MSF ta ce a wannan shekara kaɗai ta duba ƙananan yara fiye da 300,000 aka samu da matsalar a jihohin yankin bakwai.

    Ƙungiyar ta ce rashin abinci mai gina jiki na shafar lafiyar kwakwalen yara, lamarin hana su cimma wasu muhimman bangarori na ginuwar gaggar jikinsu.

    Arewacin Najeriya ya shafe shekaru yana fama da rashin tsaro, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da gidajensu tare da haifar da rashin noma.