Rufewa
A nan za mu rufe wannnan shafin na labaran kai-tsaye na yau Takata.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 30/09/2025
Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida
A nan za mu rufe wannnan shafin na labaran kai-tsaye na yau Takata.
Sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Firaministan Qatar ya ce ƙasarsa za ta koma kan teburin sulhu domin ci gaba da shiga tsakani domin samar da zaman lafiya a Zirin Gaza.
Wannan na zuwa ne bayan Netanyahu ya nemi afuwar Qatar game da hare-haren da ya kai a Doha kan jagororin Hamas.
A wayar da Trump da Netanyahu suka yi da Firaministan na Qatar, Netanyahu ya bayyana nadamarsa kan mutuwar wani ɗan Qatar a harin na ranar 9 ga watan Satumba, wanda ya ce ya karya ƴancin ƙasar na Qatar, sannan ya ce Isra'ila ba za ta sake irin haka ba.
Ministan harkokin wajen Qatar ya ce afuwar da Netanyahu ya nema ce ta sa Qatar ta amince ta ci gaba da shiga tsakani, "domin tabbatar da zaman lafiya a Zirin Gaza ta hanyar amfani da tsare-tsaren da Amurka ta tsara," in ji shi.
Shugaba Trump ya shaida wa daruruwan manyan hafsoshin soji da aka tara a wani taro na musamman, cewa ya kamata su yi amfani da biranen Amurka a matsayin filin atisaye, kan abin da ya kira abokan gaba na cikin gida.
Wakilin BBC ya ce shugaba Trump yayi jawabin nasa ne akan yaƙin cikin gida, da ta'azzarar matsalar tsaro a birane kamar su Sanfransisko da Chicago da Los Angeles.
Mista Trump ya kuma kare matakin tura rundunar tsaro ta cikin gida da ya yi, yana mai cewa zai gyara biranen da yake ganin cike suke da laifi ɗaya bayan ɗaya.
Haka kuma ya caccaki abin da ya kira wasa da aiki, yana mai cewa a ƙarƙashin mulkinsa an farfado da ruhin jarumtar soji.
Sojojin Ecuador sun ce an saki ragowar dakarun su huɗu daga cikin goma sha bakwai da aka yi garkuwa da su a ranar Lahadin da ta gabata, yayin zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali akan cire tallafin man fetur.
Sojojin sun kasance tare da wata tawagar agaji ƙarƙashin jagorancin Shugaba Daniel Nabowa, wanda mutane kusan dari uku suka tare, suna jefa masu wani nau'in bam haɗin gida.
Tawagar na raba tallafi ne ga al’ummomin da yajin aikin gama garin ya shafa, wanda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama a ƙasar ta kira.
Mutanen na zanga-zanga ne kan matakin shugaban na cire tallafin man fetur.
Shugaba Trump ya ce Hamas na da kwanaki uku zuwa hudu ta mayar da martani kan daftarin samar da zaman lafiyar da ya gabatar domin kawo karshen yakin Gaza.
Ya shaida wa ‘yan jarida cewa idan har kungiyar ba ta amince da shi ba, to hakan zai zama mummunan karshe a gare ta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed al-Ansari, ya ce ya yi wuri a ce an yi martani, amma daftarin na buƙatar a duba shi sosai cikin tsanaki.
Wakilin BBC ya ce akwai abubuwa da dama da ya kamata a cimma matsaya akansu game da daftarin, kamar taswira da tsarin ƙasar Falasɗinun da za a samar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce matakin da hukumomin Taliban suka dauka na katse intanet a Afghanistan, barazana ce da ka iya cutar da al’ummar kasar baki ɗaya.
Shirin tallafawa al'umma na majalisar dinkin duniya dake Afghanistan ya buƙaci hukumomin Taliban da su dawo da intanet, da hanyoyin sadarwa ba tare da bata lokaci ba.
Wakilyar BBC ta ce katsewar hanyoyin sadarwa a ciki da wajen ƙasar ya shafi hada-hadar bankuna, da kasuwanci ta Internet, da soke tashin jiragen sama da dama.
Har yanzu dai Hukumomin Taliban ɗin ba su bayar da cikakken bayani kan dalilin ɗaukar matakin ba.
Kotun soji ta musamman a Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo wato DR Congo ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Joseph Kabila hukuncin kisa.
Kotun ta yanke masa hukuncin ne bisa samunsa da aikata laifukan yaƙi da cin amanar ƙasa duk da cewa bai bayyana a kotun ba.
Sai dai ya yi watsi da hukuncin, wanda ya bayyana da rashin adalci, sannan ya yi zargin cewa ana amfani da shari'a wajen "murƙushe ƴan hamayya."
Kabila ya yi mulkin ƙasar na tsawon shekara 18 bayan ya gaji mahaifinsa Laurent, wanda ake harbe a shekarar 2001.
Tsohon shugaban ya miƙa mulki ne ga shugaban ƙasa Félix Tshisekedi a shekarar 2019, sai suka fara takun-saƙa, lamarin da ya sa Kabila ya tsere daga ƙasar a 2023.
A watan Afrilun wannan shekarar ne Kabila ya ce zai iya taimakawa wajen kawo ƙarshen mummunan yaƙin da ake gwabzawa a ƙasar tsakanin gwamnati da ƙungiyar M23 da ta fi ƙarfi a Goma, sannan aka ruwaito ya shiga ƙasar, amma ya tafi ɓangaren da ke ƙarƙashin ƴantawayen.
Bayan wannan ne Tshisekedi ya zargi Kabila da kasancewa cikin waɗanda suke goyon bayan ƙungiyar, sannan sanatacin ƙasar suka cire masa rigar kariya domin ya fuskanci hukunci.
An tsinci gawar Jakadan Afirka ta Kudu a brinin Paris na Faransa, kwana guda bayan an sanar da rahoton ɓacewar sa.
Nathi Mthethwa ya faɗo ne daga bene hawa na 22 a wani otal da ke yankin.
Rahotanni sun ce ya ɓata ne da yammacin jiya Litinin, lamarin da ya sa ƴansanda suka fara gudanar da bincike. Kawo yanzu ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu ba ta fitar da wata sanarwa ba akai.
Margayin mai shekara 58 ya fara aiki ne a Paris a bara bayan ya taba rike mukamin ministan al’adu da kuma na ‘yansanda.
Shugabannin Turai da na Gabas ta tsakiya sun yi maraba da yarjejeniyar da Amurka ta tsara na tabbatar da zaman lafiya a Gaza.
Shugaba Trump ya ja kunnen Hamas kan kada ta sake ta ƙi amincewa da yarjejeniyar.
Shawarwarin da shugaban Amurka Donald Trump da Firaiminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu suka amince da su sun buƙaci kawo ƙarshen yakin nan take da sakin ƴan Isra'ila 20 da har yanzu ke raye cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sannan a mayar daga warwakin sauran duka a cikin kwana uku, yayin da Isra'ila za ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa da take riƙe da su a gidajen yarinta.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta sanar da hana sayarwa da amfani da wasu magunguna guda 101 a faɗin ƙasar.
Hukumar ta bayyana haka ne a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce daga yanzu sana'anta magungunan da kasuwancinsu da ma amfani da su "laifi ne" a Najeriya.
NAFDAC ta ce daga cikin dalilan haramta magungunan akwai rashin ingancin lasisi da wasu laifukan da hukumar ta bayyana.
NAFDAC ta lissafin magungunan baki ɗaya a shafin nata da ke ƙasa.
Falasɗinawa na ci gaba da taruwa domin karɓar agaji a Gaza yayin da ɗaruruwan motocin ɗaukar kayan agaji suka shiga Gaza jiya.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da yaƙi ke ci gaba da ɓarkewa a Gaza
Shugaban Amurka Donald Trump dai ya sanar da tsare-tsaren tsagaita wuta yayin da ake sauraran martanin Hamas.
Sabbin hotuna daga Nuseirat a tsakiyar Gaza sun nuna ɗimbin jama’a suna taruwa domin karɓar tallafi daga cibiyar da asusun tallafin bil’adama na Gaza ke kula da ita.
Fadar shugaban Najeriya ta ce tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
To amma cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce ƴan Najeriya na sane da abin da ta kira ''rashin takaɓus'' a mulkin Jonathan ɗin na shekarun baya.
Goodluck ya mulki Najeriya a daidai lokacin da ƙungiyar Boko Haram ke kan ganiyarta wajen ƙaddamar hare-hare kan fararen hula.
A baya-bayan nan dai akwai ƙaruwar kiraye-kiraye tsakanin wasu ƴan jam'iyyar hamayya ta PDP kan tsohon shugaban ƙasar ya fito takara a zaɓen 2027.