Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/08/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Amurka ta bukaci 'yan kasarta su gaggauta ficewa daga Lebanon

    Jirgin sama a Beirut

    Asalin hoton, Getty Images

    Ofishin jakadancin Amurka da ke babban birnin Lebanon Beirut, ya bukaci Amurkawa da su gaggauta barin kasar yayin da zaman dar-dar ke karuwa a Gabas ta Tsakiya.

    Daman shi ma Sakataren harkokin waje na Birtaniya, David Lammy, ya yi irin wannan kira ga 'yan kasarsa da ke can, yana mai cewa yanayin yankin ka iya tabarbarewa cikin sauri.

    Hakan dai na kasancewa ne bayan da Iran, ta lashi takobin abin da ta kira ramuwar gayya a kan Isra'ila, wadda ta dora wa alhakin kisan shugaban bangaren siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh, a Tehran ranar Laraba.

    An kashe jagoran ne sa'o'i bayan da Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan Hezbollah Fuad Shukr a Beirut.

    Ana fargabar cewa kungiyar Hezbollah da ke Lebanon, wadda Iran ke mara wa baya, ka iya taka rawa sosai a ramuwar-gayya da za ta iya biyo bayan kashe-kashen, abin da ake ganin zai iya sa ita ma Isra'ila ta mayar da mummunan martani.

  2. Shugaba Tinubu zai yi wa al'ummar Najeriya jawabi gobe

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi wa 'yan kasar jawabi a gobe Lahadi da safe da karfe bakwai na safe.

    Sai dai sanarwar jawabin wadda mai taimaka wa Shugaban na musamman kan harkokin yada labarai Chief Ajuri Ngelale ya fitar, ba ta yi wani cikakken bayani kan abin da jawabin zai kunsa ba.

    Amma ana sa ran ba zai rasa nasaba da halin da ake ciki a kasar ba, a kwanin nan biyu sakakon zanga-zangar tsadar rayuwa, wadda ta rikide a wasu jihohin zuwa tarzoma.

    Sanarwar ta ce jawabin wanda za a yada kai tsaye ta tashar talabijin da rediyo na gwamnatin kasar, za a sake watsa shi da karfe uku na rana da kuma bakwai na dare a goben.

  3. Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 10 a wata makaranta

    Hari a Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Akalla Falasdinawa 10 aka kashe, a wani hari da sojojin Isra'ila suka kai da makami mai linzami a wata makaranta da ke Gaza.

    Ofishin yada labarai da Hamas ke tafiyarwa, ya ce jiragen yakin Isra'ila ne suka fara kai hari makarantar Hamama, inda Falasdinawan da suka rasa muhallansu ke tsugune.

    Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce, kungiyar Hamas na amfani da ginin makarantar wajen kera makamai.

    Tun da fari jirage marassa matuka biyu na Isra'ila sun hallaka Falasdinawa tara a yamma da gabar kogin Jordan, ciki har da kwamandan Hamas mai kula da wannan yankin.

  4. Kungiyar Amnesty ta gargadi hukumomin Najeriya kan masu zanga-zanga

    'yansanda sun kama wani matashi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar kare hakkin dan'Adam ta duniya, ta Amnesty International ta ce dole ne hukumomin Najeriya su kawo karshen yadda suke kokarin murkushe masu zanga-zangar lumana da suka taru a babban filin wasa na kasar da ke Abuja, Moshood Abiola Stadium, nan take.

    A wani sako da ta sanya a shafinta na X (Twitter), kungiyar ta kuma ce dole ne hukumomin su saki masu zanga-zangar lumana su sama da hamsin da aka kama haka kawai a fadin babban birnin tarayyar, Abuja, nan take kuma ba tare da wani sharadi ba.

    Wannan sanarwa da kungiyar ta fitar na daga cikin irin martanin da take yi kan matakan da hukumomin Najeriyar musamman jami'an tsaro ke dauka kan masu zanga-zangar.

    Ko a yau Asabar sai da rundunar 'yansandan Najeriyar ta fitar da wata sanarwa wadda a ciki take suka ga kungiyar ta Amnesty kan irin bayanai da alkaluman yawan mutanen da kungiyar take fitarwa, wadanda take zargin jami'an tsaro da kashewa a zanga-zangar.

    Tun a ranar Alhamis 1 ga watan nan na Agusta 2024, aka fara gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna damuwa da matsin tattalin arziki da rashin tsaro da rashin mulki na gari a Najeriyar.

    Yayin da zanga-zangar ke gudana lami lafiya a wasu sassan kasar a wasu garuruwa da birane musamman na arewacin kasar tana juyewa ta zama tarzoma, lamarin da kan kai ga sace-sace da lalata dukiya.

    Hakan ya sa aka sanya dokar hana zirga-zirga a wasu jihohin.

  5. Kungiyar marubuta kare hakkin dan'Adam ta gargadi 'yansanda kan masu zanga-zanga

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar marubuta ta masu rajin kare hakkin dan'Adam a Najeriya, HURIWA, ta soki 'yansandan kasar kan yadda suke amfani da karfin da ya wuce kima da kuma makamai a kan masu zanga-zangar da ake yi a Najeriya, wadda ta shiga kwana na uku.

    A sanarwara da kungiyar ta fitar ta hannun shugabanta Emmanuel Onwubiko, ta ce yadda 'yansanda ke tunkarar masu zanga-zangar ta lumana a rana ta uku, ko kadan babu kwarewa da nuna mutuntaka, kuma mugun laifi suke aikatawa.

    Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ta ce 'yansandan sun kama mutane da dama da suka taru a babban filin wasa na kasar da ke Abuja,Moshood Abiola Stadium, domin ci gaba da zanga-zangarsu ta lumana a yau Asabar.

    Kungiyar ta yi gargadin cewa mummunan matakin da 'yansandan ke dauka a kan masu zanga-zangar idan ba a ga illarsa ba yanzu to a nan gaba za a gani, abin da zai biyo baya.

    Haka kuma ta ce idan ba a fito da 'yansandan da suka harbi masu zanga-zanga ba an gurfanar da su gaban shari'a, tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada, lamarin zai iya sake janyo zanga-zangar da aka yi ta neman kawo karshen cin zalin da 'yansanda ke yi wato #ENDSARS.

  6. Yansandan Najeriya sun gargaɗi ƙungiyar Amnesty kan zanga-zanga

    IG Kayode Egbetokun

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar 'yansandan Najeriya ta karyata wani rahoto da kungiyar kare hakkin dan'Adam ta Amnesty International ta fitar da ke cewa an kashe mutum 13 a yayin zanga-zangar da ake yi a kasar, wadda aka fara ranar Alhamis 1 ga watan Agustan nan.

    Haka kuma rundunar a musanta ikirarin da kungiyar ta yi na cewa da gangan jami'an tsaro suna amfani da dabaru don kashe mutane, a yayin da suke kula da taruka tare kuma da amfani da bindigogi wajen tarwatsa zanga-zanga.

    Dangane da alkaluman mutanen da suka mutu, wanda rundunar ta karyata na kungiyar ta ce gabadaya mutanen da aka rasa a lokacin zanga-zangar bakwai ne, wasu ba ma a sanadin zanga-zangar ba ma suka mutu.

    A sanarwar da kakakin 'yansandan na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce, a tsawon kwana biyu na zanga-zangar, mutum hudu sun mutu, talatin da hudu kuma suka samu raunuka a jihar Borno a wani hari na 'yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

    Sannan ya ce wasu mutum biyu kuma a masu zanga-zanga sun mutu bayan da wani mai mota kirar Honda ya kutsa cikinsu, kuma yanzu haka ana neman direban wanda ya tsere ya bar motar.

    Ya kara da cewa can a karamar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi kuma wani dan kungiyar sa-kai ta bijilanti ya harbi wani daga cikin masu zanga-zanga da suke satar kayan mutane, inda mutumin ya mutu.

    Kakakin ya ce bayan wadannan da ya bayyana mutum bakwai babu wani da ya mutu a lokacin zanga-zangar.

    Sai dai an samu yadda wasu ke fashi da makami da barnatawa da satar kayan jama'a da na hukuma da sauransu a lokacin a cewar kakakin.

    Rundunar ta kuma karya cewa jami'anta na amfani da bindiga, inda kakakin ya ce jami'ansu na aiki cikin tsanaki da kwarewa kamar yadda ya kamata, suna amfani da hayaki mai sa hawaye ne kawai domin tarwatsa jama'a idan abu ya yi kamari.

    Rundunar ta kuma ce mutanen da ta kama ta tsare a lokacin zanga-zangar, ba wai kama su ta yi ba, kawai ta rike su ne tana gudanar da bincike.

    A don haka ta yi gargadi kan bayar da bayanan da ba na gaskiya ba a kan zanga-zangar.

  7. Ana ta kiraye-kirayen sako jagororin zanga-zanga na Katsina

    .

    Asalin hoton, .

    Ƙungiyoyin da suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Katsina da ke Najeriya na ta kiraye-kirayen sako jagororinsu, bayan da suka zargi jami'an tsaro da tsare su.

    “Jami'an tsaron ne suka gayyaci jagororinmu domin su amsa wasu tambayoyi, sai dai tun bayan zuwansu sai aka tsare su, bisa zargin zuga wasu da ake zargi da aikata ba daidai ba a lokacin zanga-zangar,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida yadda aka kama jagororin zanga-zangar.

    Ya ce mutanen da jami'an tsaron ke tsare da su sun haɗa da: Shugaban ƙungiyar 'Struggle for Good Governance', Habibu Muktar Ruma, da sakataren ƙungiyar 'Coalition for Civil Society', Kwamared Kabiru Shehu 'Yanɗaki.

    A lokacin zanga-zangar dai a wasu wurare musamman arewacin Najeriya an samu matsalolin fashe-fashen wurare da sace-sace da lalata dukiyoyi.

    To sai dai waɗannan ƙungiyoyin sun nesanta kansu daga hakan. ''Mun rubuta musu cewa za mu yi zanga-zanga daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 10:00 na safe, kuma da rakiyar jami'an tsaro muka yi zanga-zangarmu, har muka ƙare su ne suka ba mu kariya'', in ji shi.

    ''Kuma koda muka ƙare, sai da muka kira shi jagoran hukumar DSS na jihar muka sanar masa cewa ga shi mun tashi daga zanga-zangar kamar yadda muka aiko musu a rubuce, kuma ya tabbatar mana cewa yaransa ma sun shaida masa haka''.

    Ya bayyana cewa bayan sun kammala ta ne wasu ɓata-gari da ke iƙirarin zanga-zangar suka je suka aikata abin da bai dace ba.

    Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka sanya dokar taƙaita zirga-zirga, sakamakon fargabar ɓarkewar rikici a lokacin zanga-zangar da aka fara a ranar Alhamis.

  8. 'An kashe Haniyeh bayan harba wani makami daga tazara da ke kusa'

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Dakarun juyin-juya hali na ƙasar Iran (IRGC) sun zargi Isra'ila da amfani da wani makamai da aka harba daga 'yar tazara maras nisa daga masaukin shugaban ƙungiyar Hamas, Ismaila Haniyeh a birnin Tehran domin kashe shi.

    Rundunar ta ce makamai mai nauyin kilogiram 7 ya haifar da fashewa mai ƙarfi, da kisan Haniyeh tare da mai tsaron lafiyarsa.

    Shugaban ƙungiyar Hamas ɗin ya je birnin Tehran ne domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban IranMassoud Pezeshkian.

    Jami'ai sun zargi Amurka da goyon bayan samamen, Kawo yanzu dai Isra'ila ba ta ce komai ba game da mutuwar Haniyeh.

    Bayanan da runduar dakarun juyin-juya halin suka fitar ya yi karo da rahotonnin kafofin yaɗa labaran ƙasashen Yamma, waɗanda ke cewa sojojin Isra'ila ne suka dasa abin fashewa a gidan da Haniyeh ya sauka.

    Kisan shugaban na Hamas a Tehran, musamman a ranar da aka tsaurara tsaro a Iran, wani abin kunya da raini ne ga ƙasar da kuma Dakarun IRGC.

    Gomma dakarun juyin-juya halin ne aka kama ko aka kora daga aiki tun bayan faruwar lamarin, kamar yadda jarudar New York Times ta ruwaito, ranar Asabar.

  9. 'Yansanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Abuja

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an 'yansanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abuja, domin tarwasu.

    Masu zanga-zangar - waɗanda adadinsu bai kai yadda suka fito a 'yan kwanakin bayan nan ba - sun taru a filin wasan domin ci gaba da gudanar da zanga-zangar.

    Wasu matasan ƙasar ne dai suka shirya zanga-zangar da suka ce ta kwana 10 ne da nufin nuna adawa da matsin rayuwa da ake ciki.

    To sai dai bayanai sun ce sa'o'i bayan fara zanga-zangar tasu sai 'yansanda suka fara harba musu tiyagas da nufin tarwatsa su.

    Hukumomin birnin Abuja ne dai suka ware filin wasan a matsayin wurin da za a gudanar da zanga-zangar, bayan umarnin wata kotu ta hana masu zanga-zangar zuwa wasu sassan birnin.

    Ko a ranar Juma'a ma 'yansandan sun harba wa masu zanga-zangar hayaƙi mai sa hawaye a shataletalen Berger da ke tsakiyar Abuja.

  10. "Mu bar yaudarar kanmu shugabanni mu ne matsalar arewa"

    Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce lokaci har yanzu bai ƙure ba, ga shugabanni a arewacin Najeriya da su farka, su tsamo al'ummominsu daga halin fatara da rashin ilmi da ke addabar yankin.

    Ya ce duk da yake, masu zanga-zangar yunwa suna da hujjar su fito su nuna fushinsu ga gwamnati, amma masu zugasu don fitowa zanga-zangar, akasari sun riƙe madafun iko a baya, amma suka kasa inganta rayuwar jama'a.

    Gwamnan ya bayyana haka ne yayin zantawa da BBC a kan zanga-zangar da aka shiga a faɗin Najeriya da kuma tarzomar da aka samu a wasu jihohi ciki har da jiharsa ta Kaduna.

    Ya ce lokaci ya yi da shugabanni a yankin za su faɗa wa kansu gaskiya kuma yana kiran dukkansu 'ciki har da ni a kan mu ji tsoron Allah'

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  11. Ra'ayi Riga: Kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

    Shirin Ra'ayi Riga na wannan mako ya mayar da hankali kan zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu talakawan Najeriya ke gudanarwa.

    Masu shirya zanga-zangar sun ce za su shafe kwanaki 10 suna gudanar da ita a faɗin ƙasar.

    Tuni dai wasu jihohin ƙasar suka sanya dokar taƙaita zirga-zirga domin daƙile ɓarna da wasu ɓata-gari suka yi a lokacin zanga-zangar.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  12. Yadda birnin Kano ya kasance yayin dokar taƙaita zirga-zirga

    Wasu titunan Kano

    Titinan birnin Kano sun kasance fayau, babu jama'a sakamakon dokar taƙaita zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka ranar Alhamis, bayan da wasu masu zanga-zanga suka riƙa fasa wasu wurare tare da kwashe kayayyaki.

    Kano

    Wakilin BBC da ke birnin ya ce mutane sun ci gaba da zama a gidanjensu domin yin biyayya ga dokar.

    ''Mutane sun ci gaba da zaman gida sakamakon dokar hana fita da gwamnatin Kano ta saka. Tituna babu ababen hawa sai jifa-jifa''.

    Kano

    Ya ce mutanen da fitan ya zame musu dole, suna tafiya ne a ƙasa.

    ''Babu mutane a waje sai cikin unguwanni inda za ka ga jama'a na zama a kofar gidaje suna hira. an girke jami'an tsaro a wurare daban-daban a cikin birnin, haka kuma kasuwanni sun ci gaba da kasancewa a rufe'', in ji wakilin na BBC.

    Kano

    Jihar Kano na daga cikin jihohin da suka sanya dokar taƙaita zirga-zirga saboda zanga-zangar, bayan da aka samu arangama tsakanin wasu da ake zargin ɓata-gari ne - da suka saje cikin masu zanga-zangar - da kuma jami'an tsaro.

    Kano

    Tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar ce ta tilasta wa hukumomin Kanon sanya dokar hana fita ta sa'a 24

  13. 'Abin da ya sa ban saka dokar taƙaita zirga-zirga a Kaduna ba'

    ,,

    Asalin hoton, Kaduna Gov/X

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce bai yi tunanin sanya dokar taƙaita zirga-zira a jihar ba, saboda wasu dalilai.

    Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, Gwamna Uba Sani ya ce mutanen da suka fita zanga-zanga a jihar tun ƙarfe 3:00 na rana suka tashi.

    ''Shi ya sa ni ban taɓa tunanin sanya wata dokar taƙaita zirga-zirga ba, saboda hakan zai cutar da wasu da dama a jihar''.

    ''Idan ka sanya dokar, kana nufin duk wani ɗan kasuwa, ya rufe kasuwancinsa, to kuma ka san nawa ake asara?

    ''Akwai fa wanda sai ya ce ya buɗe kasuwa a ranar sannan ya samu abin da za a ci a gidansa a wannan ranar'', in ji gwamnan.

    Gwamnan ya kuma ce bai ji daɗini yadda wasu mutane suka yi ta ɓarna a wasu yankunan arewacin ƙasar ba.

    Ya ƙara da cewa rashin fitar waɗanda suka kira zanga-zangar ne ya haifar da tashin hankali a wasu jihohin ƙasar.

  14. Kamala Harris ta zama 'yar takarar Democrats a hukumance

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta zama 'yar takarar shugaban Amurka ƙarƙashin jam'iyyar Democrats a hukumance.

    Ms Harris ta samu wannan nasara ne bayan da ta samu adadin ƙuri'un wakilan jam'iyyar da take buƙata domin zama 'yar takara.

    Wakilan jam'iyyar dai sun yi ta kaɗa ƙuri'a ta Intanet, kuma za su ci gaba har zuwa ranar Likitin.

    Yayin da take jawabi ta wayar tarho, Ms Harris ta ce ''ta samu alfarmar zama 'yar takara'', yayin da take ci gaba da samun goyon baya gabanin babban taron jam'iyyar da za a gudanar nan gaba cikin wannan wata a birnin Chicago.

    Ms Harris ce mace baƙar fata ta farko kuma 'yar asalin kudancin Asiya ta za ta yi takarar shugabancin Amurka a ƙarƙashin ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun ƙasar.

    Idan har ta doke Donald Trump - ɗan takarar jam'iyyar Republican, a zaɓen watan Nuwamba da ke tafe - za ta kasance mace ta farko da ta shugabanci Amurka.

  15. Zulum ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Borno

    ..

    Asalin hoton, Zulum/X

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga da aka sanya a jihar, bayan fashewar bom a Kawori ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 tare da jikkata wasu.

    Yayin da yake jawabi da aka yaɗa a kafofin yaɗa labaran jihar, Gwamna Zulum ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu a harin na Kawori.

    ”Ina miƙa saƙon ta'aziyyar ga iyalan waɗanda harin ya shafa da kuma duka mutanen Borno, ina kuma jajanta wa waɗanda suka jikkata, waɗanda a yanzu haka ke asibiti suke kuma samun kulawar likitoci”.

    Gwamnan ya kuma ce tun da farko an sanya dokar ne domin hana mayaƙan Boko Haram amfani da damar wajen haifar da tashin hankali a jihar.

    Ya ƙara da cewa ɓata-gari ne suka yi shigar burta domin shiga cikin masu zanga-zangar lumana, inda suka yi yunƙurin kawo hargitsi, sai dai a cewarsa jami'an tsaro sun samu nasarar kwantar da hankula.

    Yayin da yake bayyana janye dokar taƙaita zirga-zirgar, Gwamna Zulum ya ce mutane su fita harkokinsu, amma jami'an tsaro za su ci gaba da sanya idanu, domin magance duk wani abu da suka ga zai kawo tashin hankali.

  16. Amurka ta tura jiragen yaƙi Gabas ta Tsakiya bayan ƙaruwar zaman ɗar-ɗar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar tsaron Pentagon ta ce za ta ƙara tura dakaru da jiragen yaƙin Amurka zuwa Gabas ta tsakiya, yayin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin.

    Iran da ƙawayenta sun sha alawashin mayar da martani kan Isra'ila na kisan shugaban Hamas a Tehran da kwamandan Hizbollah a Beirut.

    Wani mai gabatarwa a gidan talabijin Iran ya ce nan da wasu sa'o'i masu zuwa duniya za ta ga abun mamaki.

  17. Isra'ila ta ce ta kashe jagoran mayakan Hamas a Gabar Yamma da Kogin Jordan

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar watsa labaran Isra'ila ta bayar da rahoton kashe jagoran mayaƙan Hamas a wani hari ta sama da Isra'ilar ta kai Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Sojojin Isra'ilar sun ce sun yi niyyar kai hari ne kan sansanin mayaƙan Hamas da ke yankin.

    Kafar watsa labaran Falasɗinawa ta tabbatar da kai harin, inda ta ruwaito cewa harda ƙarin wasu mutum hudu suka mutu a yayin da aka kaiwa motar da jagoran mayaƙan Hamas din yake ciki.

    A cikin wannan ne dai Isra'ila ta kashe shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a birnin Tehran na kasar Iran

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana da Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna kuma iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.