Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 27 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotonni

    Nan za mu dakatar da kawo rahotonni a wannan shafi na ranar Lahadi.

    Ku kasance da mu a babban shafinmu domin ganin wasu labaran da za mu wallafa, da kuma shafukanmu da sada zumunta.

    Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.

  2. Har yanzu matakan da Isra'ila ta ɗauka sun yi kaɗan wajen rage yunwa a Gaza - MSF

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar bayar da agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce sabbin hanyoyin kai agaji Gaza da Isra'ila ta bari ake yi bai isa ba.

    "Bayan wata biyar ana azabtar da mutane da yunwa, mutane na buƙatar tabbacin cewa za su ci gaba da samun wani abu," a cewar shugabar sashen ayyuka ta MSF Amande Bazerolle yayin hira da kamfanin labarai na Reuters.

    Bayan tsagaita wuta na ɗan lokaci a kullum da barin shigar da kayan da sojojin Isra'ila suka sanar, Bazerolle ta ce ya kamata a bayyana ƙarara wuraren da za a dinga kai kayan "saboda kowa ya san cewa agajin zai kai masa".

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce mutum 127 ne suka mutu saboda yunwa, cikinsu har da yara 85.

  3. Jordan da UAE sun jefa tan 25 na kayan agaji a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Jordan ta ce jiragen yaƙin ƙasar sun gudanar da aikin jefa kayan abinci ta sama a Gaza tare a na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

    Jiragen sun jefa tan 25 na abinci da sauran muhimman abubuwa a Gaza.

    Jiragen Jordan biyu ƙirar C-130 da wani na Daular Larabawan ne suka gudanar da aikin a yankuna da dama na zirin, a cewar rahoton.

    Gidan talabijin ɗin ya ce aikin na yau shi ne na 127 jimilla da Jordan ta gudanar tun bayan fara yaƙin a Gaza a watan Oktoban 2023.

  4. Kwale-kwale ya kife da fasinjoji da dama a jihar Neja

    Kwale-kwale

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana fargabar fasinjoji da yawa sun rasu sakamakon kifewar kwale-kwale a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

    Rahotonni sun ambato hulkumar bayar da agajin gaggawa ta jihar NSEMA na cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar.

    Shugaban hukumar, Ibrahim Hussaini, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa kwale-kwalen da ke ɗauke da mutanen da ba a san yawansu ba da kuma kayayyaki, ya kife ne a kan hanyar zuwa garin Kuta.

    Hussaini ya nuna cewa matuƙin jirgin da wasu fasinjojin sun tsira, yayin da ɗaya daga cikinsu ke jinya a asibiti Kuta.

    Ya ƙara da cewa ba za su iya bayyana yawan mutanen da lamarin ya shafa ba yayin da suke ci gaba da aikin ceto.

  5. Yadda wasu Falasɗinawa suka fara karɓar abinci a yau

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa hotunan wasu mazauna Zirin Gaza ɗauke da kayan abinci da suka karɓa a yau Lahadi a unguwar Beit Lahia.

    Sun samu kayan ne bayan Isra'ila ta ce ta tsagaita wuta na ɗan lokaci a wasu sassan Gaza domin bai wa ma'aikata damar raba kayan agajin.

    An ga yadda dandazon mutane ke hawa kan manyan motocin da ke ɗauke da kayan, da kuma yadda suke ɗauke da buhu a kafaɗa.

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

  6. 'Yansandan Adamawa na taimakawa yayin ambaliyar ruwa

    Yola

    Asalin hoton, SP Suleiman Yahaya

    Yola

    Asalin hoton, SP Suleiman Yahaya

    Yola

    Asalin hoton, SP Suleiman Yahaya

  7. Ambaliya ta mamaye sassan Yola na jihar Adamawa

    Yola

    Asalin hoton, Abdulaziz Ibrahim

    Rahotonni daga birnin Yola na jihar Adamawa na cewa ambaliyar ruwa ta mamaye wani ɓangare na garin da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce wuraren da ambaliyar ta fi shafa su ne Shagari Low cost, da Sabon Pegi, da Modire Yolde Pate da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.

    Ya wallafa hotunan dakarun rundunar da suka ƙware a fannin koguna cikin jiragen ruwa da ke kan hanyarsu ta kai agaji ga al'ummomin yankunan.

    A ɗaya daga cikin wuraren, zurfin ruwan ya kai rabin tsawon mutum.

    Yola

    Asalin hoton, Abdulaziz Ibrahim

    Yola

    Asalin hoton, Abdulaziz Ibrahim

  8. Motocin agaji sun shiga Gaza bayan amincewar Isra'ila

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Manyan motoci ɗauke da kayan agaji sun tsallaka Gaza daga Masar bayan samun izini daga Isra'ila.

    Isra'ilar ta ce ta tsagaita wuta ta ɗan lokaci a wasu sassan Gaza domin bayar da damar shigar da kayayyakin abinci da magani, waɗanda ta hana tsawon watanni.

    Matakin na zuwa ne yayin da ma'aikatar lafiya a Gazan ta ce ƙarin mutum shida sun mutu saboda yunwa cikin awa 24 da suka gabata.

    Shugaban hukumar ba da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya Tom Fletcher ya yi maraba da dakatar da buɗe wutar, yana mai cewa yana magana da ma'aikatan da ke gudanar da aikin raba kayan.

  9. Yadda Tinubu ya gana da 'yanwasan Super Falcons ta bidiyo

    Super Falcons

    Asalin hoton, Getty Images

    Jim kaɗan bayan jinjina kofin ƙasashen Afirka, tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya ta gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta bidiyo.

    Shugaban ya ce ya "ƙagu su zo da kofin Abuja" domin yin bukukuwan murna.

    Karo na 10 kenan Najeriya na cin kofin a tarihi bayan doke masu masaukin baƙi Morocco 3-2 a daren da ya gabata.

    Latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyo:

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
  10. Tinubu ya faɗa wa tawagar Super Falcons: 'Najeriya na alfahari da ku'

    'Yanwasan Najeriya

    Asalin hoton, Super Falcons

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya faɗa wa 'yanwasan tawagar mata ta ƙasar cewa "dukkan Najeriya" na alfahari da su bayan sun lashe kofin ƙasashen Afirka karo na 10.

    "Ina matuƙar farin ciki da alfahari da ku. Baki ɗayan Najeriya na alfahari da ku," a cewar shugaban yayin da yake magana da su ta bidiyo jim kaɗan ɗaga kofin.

    "Za a taya ku murna, kuma ina taya dukkan kociyoyin murna, da sauran jami'ai."

    Tawagar Najeriya ta Super Falcons ta doke 'yanmatan Morocco masu masaukin baƙi 3-2 a wasan ƙarshen da aka buga a daren da ya gabata a gasar ta 2024.

    Morocco ba ta taɓa cin kofin ba, amma karo biyu kenan a jere tana zuwa wasan ƙarshe.

  11. 'Yansandan Najeriya sun kama sojoji cikin 'ƴan ƙungiyar asiri' a jihar Ogun

    'Yansandan Najeriya

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Ogun ta tabbatar da kama mutum 21 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri, ciki har da sojojin ƙasar biyu yayin wani samame kan wani otel a birnin Abeokuta.

    A cewar kakakin rundunar a Ogun, Omolola Odutola, an kai samamen ne ranar Juma'a bayan samun bayanan sirri game da taron mambobin ƙungiyar Aiye.

    Daga cikin abubuwan da suka karɓe daga hannun mutanen akwai bindiga ƙirar gida, da gatari, da shuɗayen huluna masu yawa, da saura kayayyakin da masu asiri ke amfani da su.

    "Tuni aka miƙa mutanen ga sashen binciken laifuka da ayyukan asiri domin ci gaba da bincike," in ji kakakin.

  12. Dakarun Isra'ila sun kama masu fafutikar kai agaji Gaza

    Jirgin Freedom Flotilla

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar fafutika ta 'Freedom Flotilla' mai goyon bayan Falasɗinawa ta ce sojojin Isra'ila sun shiga cikin jirgin ruwansu da ke ƙoƙarin kai agaji Gaza ta cikin teku.

    Ta ce jirgin mai suna Handala, an kama shi a tsakiyar teku.

    Hotunan bidiyo sun nuna masu fafutikar a cikin jirgin sun ɗaga hannaye lokacin da sojoji suka ƙwace iko da jirgin, sannan daga bisani aka daina jin ɗuriyarsu.

  13. Barkanmu da hantsin Lahadi

    Ni ne Umar Mikail zan kawo muku rahotonni kai-tsaye a wannan shafi na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Amma za mu fi mayar da hankali kan Najeriya, da Nijar, da maƙwabtansu.