Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 8 ga watan Satumba, 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Isra'ila da Hamas sun amince da sharuɗan Trump na tsagaita wuta a Gaza

    Hamas ta ce ta samu wasu dabaru daga wajen Amurka ta hanyar masu shiga tsakani a kan yadda za a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

    Hamas ta fitar da wata sanarwa bayan shugaba Donald Trump ya gabatar da abin da ya kira gargadi na karshe ga Hamas din akan ta amince da cimma yarjejeniya ta saki Isra'ilawan da take tsare da su.

    Wakiliyar BBC ta ce tun da farko shugaban Amurkan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa Isra'ila ta amince da sharudansa, yanzu ya ragewa Hamas ita ma ta amince da sharudan.

    A cewar kafar yada labaran Isra'ila, abin da kunshin yarjejeniyar baya-bayan nan ya kunsa shi ne Hamas za ta saki dukkan mutanen da take tsare da su su 48 wanda yawancinsu an kashe su a ranar farko da yarjejeniyar za ta fara aiki, inda kuma za a sako dubban Falasdinawa fursunoni a matsayin musaya.

    Akwai kuma tattaunawar da za a yi akan kawo karshen yakin da ake yi gaba daya.

  2. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC.

    A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.