Najeriya ta kwashe ƙarin mutanenta 266 daga Afirka ta Kudu
Ƴan Najeriya sama da 260 sun isa birnin Legas a safiyar Juma'a yayin da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da kwashe mutanenta da ke zaune a Afirka ta Kudu sanadiyyar zanga-zangar ƙyamar baƙi da ta ɓarke a baya-bayan nan.
Yanzu yawan ƴan Najeriya da gwamnatin ƙasar ta kwashe daga ƙasar ta Afirka ta Kudu ya kai 700.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya shaida wa BBC cewa mutane 266 ɗin da suka isa Najeriya a yau sun sauka birnin Legas ne da ƙarfe 10:40 na safe.
Najeriya ta fara kwashe mutanenta daga Afirka ta Kudu ne bayan jerin zanga-zangar da wasu ƙungiyoyi suka riƙa yi, inda suke far wa baƙi, lamarin da ya sa ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu suka riƙa kira ga gwamnatinsu da ta kwashe su zuwa gida.
Wannan ne jirgi na huɗu na ƴan Najeriya da ya isa gida a ƙarƙashin shirin.
Hukumomin Najeriya sun kuma ce akwai wasu jiragen ɗauke da ƴan Najeriya da ake sa ran za su sauka a ƙasar a ranakun 6 da kuma 9 ga watan Yuli.
Haka nan gwamnatin Najeriyar ta shawarci ƴan ƙasar nata da ake mayarwa gida su tantance dukiyoyinsu da suka bari a baya, inda hukumomin ke sa ran neman gwamnatin Afirka ta Kudu ta biya diyya.