Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Tinubu ya naɗa Jega mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kiwon dabbobi

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara na musamman sannan kodinetan shirin shugaban ƙasa na kawo sauyi a harkar kiwon dabbobi.

    Cikin sanarwar naɗin da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar da maraicen ranar Juma'a, Shugaba Tinubu ya ce yana fatan naɗin zai kawo gagarumin sauyi mai ma'ana a harkar kiwon dabbobi a ƙasar domin ƙarfafa burin shugaban na gina ƙasar.

    Dama dai Farfesa Jega tare da Tinubu sun jagoranci kwamitin shugaban ƙasa kan inganta harkokin kiwo.

    ''Kwamitin ya kuma gabatar da cikakken rahoto da shawarwarin inganta harkokin kiwo a ƙasar nan, ciki har da shawarar kafa hukumar kula da kiwon dabbobi da a yanzu haka ke da minista'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Farfesa Jega mai shekara 68 - wanda tsohon shugaban Jami'ar Bayero ta Kano ne - ya jagoranci hukumar zaɓen Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.

  2. Gwamnan yankin Donestk ya ke mutum 20 ne suka mutu a harin Rasha

    Gwamnan yankin Donestk, Vadym Filashkin ya ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin Rasha na ranar Juma'a ya kai 20.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Telegram da safen nan ya ce harin ya kuma jikkata mutum 43.

    Gwamnan ya kuma ƙara da cewa sabbin alƙaluman ba su ƙunshi waɗanda aka raunata a biranen Mariupol da Volnovakha ba, waɗanda a yanzu haka ke ƙarƙashin ikon sojojin Rasha.

  3. Harin Rasha ya kashe mutum 11 a kusa da birnin Donetsk - Ukraine

    Hukumomin Ukraine sun ce wani hari da Rasha ta kai garin Dobropillya ya kashe mutum 11 tare da jikkata gommai.

    Garin - na Dobropillya - na a yankin arewa maso yammacin birnin Donetsk

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin Donestk ta ce harin - wanda aka kai cikin daren da ya gabata - ya lalata gidaje takwas tare da wani ofishin gwamnati.

    A baya-bayan nan dai Amurka ta sanar da dakatar da bai wa Ukraine bayanan sirri a yaƙinta da take yi da Rasha.

  4. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya bayyana ra'ayoyinku a shafukan sada zumunta, kan labaran da muke wallafawa.