Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An canja alƙalin da ke shari'ar Nnamdi Kanu

    Kanu

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban alƙalin kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, John Tsoha ya canja alƙalin da ke shari'ar jagoran ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, kamar yadda shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito.

    Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

    A baya dai mai shari'a Binta Nyako ce take sauraron shari'ar, wadda ake zargin Kanu da cin amanar ƙasa da tayar da zaune tsaye.

    A watan Satumban shekarar da ta gabata ne Kanu ya buƙaci mai shari'a Nyako ta sauka daga jagorancin sauraron shari'ar, inda ya zarge ta da rashin adalci.

  2. Red Cross ta buƙaci a ba ma'aikatan lafiya damar shiga yankin da ake rigima a Syria

    Red Cross

    Ƙungiyar agai ta Red Cross ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da suke tankiya a Syria da ba ma'aikatan lafiya damar shiga yankin ƙasar da ake rikici tsakanin sabuwar gwamnatin ƙasar da magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasar, Bashar al-Assad.

    Rahotanni sun nuna cewa an kashe sama da mutum biyar a yankunan Latakia da Tartous daga ranar Alhamis zuwa yanzu a lokacin da aka yi wa dakarun gwamnatin ƙasar kwanton-ɓauna lokacin da suke yunƙurin kama wani tsohon jami'an gwamnatin Assad.

    Rahotannin sun ƙara da cewa yawancin waɗanda aka kashe ɗin fararen hula ne daga tsagin alawy, inda wasu daga cikinsu kisan glla aka musu, lamarin da ya gwamnatin Faransa ta yi allawadai.

  3. Ba za mu tattauna da Amurka kan dakatar da shirin nukiliya ba - Khamenei

    Iran

    Asalin hoton, EPA

    Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya yi watsi da buƙatar Shugaban Amurka Donald Trump ta neman ƙasar Iran ta buɗe ƙofar tattaunawa domin dakatar da shirinta na samar da makamin nukiliya.

    Khamenei ya ce Iran ba za ta shiga tattaunawa ba domin matsin lamba daga ƙasar da ya bayyana da "mai raini da wulaƙanci."

    A shekarar 2018 ce Trump ne fice daga yarjejeniyar rage wa Iran takunkuman da aka ƙaƙaba mata, wanda aka yi domin a rarrashe ta ko hakan zai sa ta fara nazarin dakatar da shirin nata na nukilya.

    Sai dai bayan wannan matakin Iran ɗin ta cigaba da sarrafa uraniun ɗinta, wanda a yanzu ya kusa kai matakin makamin na nukiliya.

  4. Girke-girken Ramadan: Yadda ake haɗa danderun naman rago da shinkafa

    A yau Amina Idris, wacce aka fi sani da amnas kitchen za ta nuna muku yadda za ku yi danderun naman rago da shinkafa.

    Ku biyo Amina domin ganin yadda ake yin wannan haɗin.

    Bayanan bidiyo, Girke-girken Ramadan: Yadda ake haɗa danderun naman rago da shinkafa
  5. 'Harin Isra'ila a Lebanon ya kashe mutum ɗaya'

    Hezbollah

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin watsa labarai A Lebanon sun ruwaito cewa harin jirgi mara matuƙi na Isra'ila a ƙasar ya yi kashe mutum ɗaya, tare da jikkata wani.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin kan wani mayaƙin Hezbollah wanda yake fara tattara kadarori da kayan aikin mayaƙan ƙungiyar.

    A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin da aka ɗauka sama da shekara ɗaya ana gwabzawa tsakanin Hezbollah da Isra'ila.

    A watan Fabrairu ne aka tsara Isra'ila za ta janye sojojinta daga Lebanon, amma har yanzu akwai sojojin ƙasar a wasu yankuna biyar da ta ce, "suna da matuƙar muhimmanci."

  6. Waɗanda hare-haren Rasha suka kashe a Ukraine sun kai 21

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Kamar yadda rahotanni suke nunawa, waɗanda hare-haren Rasha suka kashe a ƙasar Ukraine sun kai 21 zuwa yanzu.

    Daga cikin waɗanda hare-haren ya rutsa da su akwai mutum 17 daga yankin Donetsk, inda hukumomin yankin suka ce an aƙalla mutum 11 aka kashe, wasu mutum 30 suka jikkata, ciki har da ƙananan yara. Sannan wasu mutum shida suka mutu a wasu sassan yankin birnin.

    A yankin Kharkic kuwa, hukumomi sun ce aƙalla mutum uku ne suka mutu, sannan mutum bakwai suka jikkata a wani harin jirgi mara matuƙi.

    Sai kuma yankin Kherson, inda wani dattijo mai shekara 54 ya rasu.

  7. An bayar da lasisin buɗe sababbin matatun man fetur a Najeriya

    FAROUKAHMED

    Asalin hoton, FAROUKAHMED/FACEBOOK

    Hukumar Kula da Albarkatun Mai Na Ƙasa (NMDPRA) ta bayar da lasisin buɗe sabbin matatun man fetur a Najeriya.

    Hukumar ta ce ta ba wasu kamfanoni guda uku lasisin ne domin buɗe matatun a jihohin Abia da Delta da Edo.

    A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X, ta ƙara da cewa za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a jihar Edo.

    Za kuma da Matatar MB wadda za ta riƙa tace ganga 30,000 a kullum a jihar Delta, sai Matatar HIS wadda ita kuma za ta riƙa tace ganga 10,000 a kullum a jihar Abia, kamar yadda sanarwar, wadda shugaban hukumar, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna.

    Idan aka kammala su, matatun guda uku za su riƙa tace ganga 140,000 ke nan a kullum.

  8. DR Congo ta sa ladar dala miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka aka kama jagororin M23

    M23

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin DR Kongo ta sanya ladar dala miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka wajen kama jagororin ƴantawayen ƙasar ta M23 waɗanda suka ƙwace iko da mafi yawan gabashin ƙasar.

    Tun a shekarar da ta gabata ce dai aka yanke musu hukunci ba tare suna hannu ba, inda kotun sojoji ta yanke musu hukuncin kisa bisa samunsu da laifin cin amanar ƙasa.

    Gwamnatin ƙasar ta kama wani wanda a baya ya taɓa shugabantar hukumar zaɓen ƙasar mai suna Corneille Nangaa, amma yanzu yake jagorantar wata ƙungiyar ƴantawaye ta Congo River Alliance.

    Ma'aikatar shari'ar ƙasar ce ta bayyana haka, inda ta ce duk wanda ya taimaka wajen kama Bertrand Bisimwa da Sultani Makenga da suke jagorantar ƙungiyar M23 za su samu ladar dala miliyan biyar, duk da cewa hakan zai yi wahalar gaske.

  9. MDD ta gargaɗi jagororin Sudan ta Kudu kan jefa ƙasar cikin yaƙi

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Sudan ta kudu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga shugabannin ƙasar da su magance matsalar rikicin ƙasar ta hanyar siyasa da sulhu, inda ta yi gargaɗi cewa cigaba da rikicin zai jefa yankin cikin tashin hankali.

    A ranar Juma'a ce aka kashe wasu sojoji bayan wasu ƴanbindiga sun kai hari kan helikwaftar Majalisar Ɗinkin Duniya da ta je kwaso sojoji a jihar Upper Nile da ke ƙasar.

    Shugaban Ƙasar Salva Kiir ya zargi mataimakinsa, kuma tsohon jagoran ƴantawayen ƙasar, Riek Machar da hannu a samun matsalar, wadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana da laifin yaƙi.

    Hukumar ta ce ana ƙoƙarin mayar da hannun agogo baya a ƙasar ta Sudan, musamman fafutikar riƙe ƙarfin iko, wanda shi ne a baya ya jefa ƙasar cikin yaƙi.

  10. Somaliya ta yi wa mayaƙan al-Shabab tayin afuwa idan suka ajiye makamai

    mayakan al-Shabb

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Mayaƙan Al-Shabab sun shafe fiye da shekara 10 suna yaƙi da gwamnatin Somaliya mai samun goyon bayan MDD

    Shugaban ƙasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya yi wa mayaƙan ƙungiyar al-Shabab tayin yi musu afuwa idan suka ajiye makamansu.

    Shugaban ya kuma alƙawarta cewa ba za a ci zarafinsu ko ɗaure su a gidan yari ba, matsawar suka amince da tayin nasa.

    Hassan Sheikh Mohamud ya ce tuni waɗanda suka ajiye makaman nasu ke zaune cikin aminci, inda wasu ma suka shiga aikin sojin ƙasar, wasu kuma ayyukan gwamnati da kasuwanci.

    An sha yi wa mayaƙan Al Shabab afuwa cikin shekara 15 da suka gabata.

    A lokuta da dama gwamnatin Somaliya kan ayyana ajiye makaman gomman mayaƙan.

    Ƙungiyar Al-Shabab ta shafe shekaru tana yi wa tsaron Somaliya barazana, inda sojojin Amurka da na AU suka riƙa taimaka wa ƙasar a lokuta da dama.

  11. 'Saboda saɓa doka muka dakatar da Natasha ba don zargin cin zarafi ba'

    Michael Opeyemi Bamidele

    Asalin hoton, Michael Opeyemi Bamidele/X

    Bayanan hoto, Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Michael Opeyemi Bamidele

    Majaliar Dattawan Najeriya ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalaisar ba.

    Cikin wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar, ya ce dakatar da Sanatar, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da Sanata Natasha ta yi.

    ''An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa'idojin majalisa, da nuna rashin ɗa'a a majalisar, wannan shi ne laifinta babu daɗi babu ragi.'' kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta ce in da ƴarmajalisar ta yi aiki da dokoki da ƙa'idojin majalisar, da majalisar za ta karɓi ƙorafinta, kamar yadda doka ta tanada, ''amma ba ta bi ƙa'ida da dokokin da suka kafa majalisar da take aiki a cikinta ba''.

    Sanata Bamidele ya ce majalisar ta ɗauki matakin dakatar da ƴarmajalisar ne bisa shawarar kwamitin ɗa'a, wanda ya sameta da laifin saɓa wa sashe na 6.1 da sashe na 6.2 na dokokin majalisar, sannan ya bayar da shawarar dakatar da ita.

    Sanarwar ta kuma zayyano wasu laifuka biyar da ta ce Sanata Natasha ta aikata, ciki har da ƙin zama a kujerar da aka sauya mata a lokacin zaman majalisar na ranar 25 ga watan Fabrairu, da yin magana ba tare da amincewar jagoran zaman majalisar ba, da yin kalaman zagi da rashin girmamawa da shugabancin majalisar.

  12. Najeriya ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man fetur uku a ƙasar

    Matatun mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku.

    Cikin wata sanarwa hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun ne a jihohin Abia da Delta da kuma jihar Edo.

    NMDPRA ta ce sabbin matatun uku idan an kammala su za su iya tace gangan 140,000 a kowace rana.

    Bayanai daga hukumar ta NMDPRA sun nuna cewa Najeriya na da matatun man fetur tara, ciki har da sabuwar matatar Dangote da ke birnin Legas.

    Waɗannan matatu na tace ganga 974,500 a kowace rana, yayin da matatar Dangote kaɗai ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.

  13. Manyan ƙasashen Turai sun nuna goyon bayan shirin Larabawa na sake gina Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan ƙasashen Turai huɗu sun bayyana goyon bayansu ga ƙasashen Larabawa kan shirin zaman lafiyar Gaza.

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen Faransa da Jamus da Italiya da Birtaniya sun yi maraba da shirin a matsayin abu na zahirin - saɓanin shawarar Amurka da Isra'ila da suka riga suka yi watsi da shirin.

    Shirin ƙasashen Larabawar ya tanadi sake gina Gaza cikin shekara biyar, ƙarƙashin kulawar ƙwararrun Falasɗinawa, kafin lokacin da gwamnatin Falasɗinawa za ta karɓe iko da shirin.

    Ƙasar Masar ce ta jagoranci ɓullo da shirin, a wani mataki na martani kan shawarar shugaban Amurka Donald Trump na kwashe al'ummar Gaza domin sake gina yankin.

  14. Ƙasashe nawa ne mata ba su taɓa mulka ba?

    A faɗin duniya, shigar mata cikin siyasa na ƙaruwa a hankali a hankali, inda shigar mata siyasa ya fi samun tagomashi a ƙarshen ƙarni na 20 zuwa farkon ƙarni na 21.

    A 2008, majalisar dokokin Rwanda ta zamo ta farko a duniya da ta zaɓi mace a matsayin shugabar masu rinjaye.

    A yanzu, a ƙasashe uku ne kacal cikin 193 - wato Rwanda da Cuba da kuma Nicaragua - mata ke da rinjaye a majalisar dokoki.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  15. Ministar mata ta ce za ta sasanta rikicin dakatar da Sanata Natasha

    Ministar mata

    Asalin hoton, Ministry of Women Affairs

    Ministar al'amuran mata da walwalar jama'a ta Najeriya, Imaan Suleiman ta ce a shirye take ta shiga domin sasanta rikicin dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta tsakiya.

    Yayin da take jawabi ga manema labarai a fadar shugaban ƙasar ranar Juma'a, ministar ta bayyana takaicinta kan zargin cin zarafin lalatar da aka yi a majalisar dattawan, lamarin da ta bayyana da ''abin takaici''.

    Tana mai cewa bai kamata irin wannan abu ya riƙa faruwa a majalisar dokokin Najeriya ba.

    Imaan Sulaiman ta ce ma'aikatarta za ta tattauna da majalisar dattawan domin duba yadda za a sasanta matsalar cikin salama.

    “Za mu sasanta batun. Za mu tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sasanci cikin kwanciyar hankali.”

    A ranar Alhamis ne Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida, saboda saɓanin da ya shiga tsakaninta da shugaban majalisar, kan sauya mata wurin zama, inda daga baya ya koma zargin cin zarafin lalata.

  16. An zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya kashe iyayen budurwarsa a Amurka

    Brad Sigmon

    Asalin hoton, South Carolina Department of Corrections

    Hukumomi a jihar South Carolina ta Amurka sun zartar da hukuncin kisa kan wani mutum da kotu ta samu da laifin kashe iyayen tsohuwar budurwarsa.

    Wannan shi ne hukuncin kisa na farko da aka zartar kan wanda aka samu da laifin kisan kai a Amurka cikin shekara 15.

    Jami'an gidan yari uku ne suka harbe Brad Sigmon a ƙirjinsa, da wasu alburusai na musamman a ranar Juma'a da maraice.

    A tsakiyar mako ne dai kotu ta samu Sigmon, mai shekara 67 da laifin kashe iyayen tsohuwar budurwasa a 2001, kafin ya yi garkuwa da budurwar da ƙarfin bakin bingiga, kodayake ta samu nasarar kuɓuta duk da harbinta da ya yi.

    Rabon da a zartar da hukuncin kisa a Amurka ta 2010, lokacin da aka zartar da hukuncin kan Ronnie Lee Gardner.

  17. Al-Sharaa ya ce gwamnatin Syria za ta farauto masu goyon bayan Bashar Assad

    al-Sharaa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria, Ahmed Al-Sharaa ya ce gwamnatinsa za ta farauto sirarun mutanen da har yanzu ke nuna goyon baya ga hamɓararren shugaban ƙasar, Bashar Al-assad, domin su fuskanci shari'a bayan shafe kwana biyu ana rikici a yankin Latakia.

    Al-Sharaa ya ce waɗanda suka aikata kisa kan fararen hular da ba su ji ba su gani ba za su fuskanci hukunci.

    Wata ƙungiya da ke sanya idanu kan yaƙin Syria ta zargi dakarun gwamnati da aikata kisan fareren hula fiye da 160 a yankin da ke gaɓar teku.

    Wani mai fafutika a yankin na Latakia ya faɗa wa BBc cewa mayaƙan da ke goyon bayan gwamnati sun aikata kisan ba sani ba sabo a ƙauyukan da tsiraru ƴan ƙabilar Assad ta Alawi ke zama,

  18. Zelensky ya ce harin Dobropillya manuniya ce har yanzu manufar Rasha ba ta sauya ba

    Shugaban Ukraine

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce ''harin da Rasha ta kai garin Dobropillya ya nuna cewa har yanzu manufar ba ta sauya ba''.

    Shugaban na jawabi ne a matsayin martani kan harin da aka kai yankin gabashin Ukraine cikin daren da ya gabata.

    "Don haka yana da kyau mu ci gaba da kare rayukan ƴanƙasarmu da ƙarfafa tsaron sararin samaniyarmu tare da tsananta takunkumai kan Rasha,'' kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Telegram.

    "Duk abin da ke taimaka wa Rasha wajen ɗaukar nauyin yakin nan dole ne a rusa shi" in ji shi.

  19. Za mu maido da hare-hare a Tekun Maliya idan Isra'ila ba ta bari aka shigar da agaji Gaza ba - 'Yantawayen Houthi

    houthi

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban mayaƙan Hothi a Yeman ya ce idan Isra'ila ba ta bari aka ci gaba da shigar da kayan agaji zuwa Gaza nan da kwana huɗu ba, ƙungiyarsa za ta dawo da hare-hare kan manyan jiragen ruwa a Tekun Maliya.

    Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Abdulmalik Al-Hothi ya jaddada matsayar ƙungiyar ga duniya baki ɗaya.

    A farkon watan nan ne Isra'ila ta datse damar ci gaba da shigar da agaji yankunan Falasɗinawa a wani mataki na matsa wa Hamas lamba ta amince da buƙatar tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.

    A shekarar 2023 mayaƙan Hothi suka soma ƙaddamar da hare-hare kan jigaren ruwa da ke hada-hada tsakanin ƙasashe, a wani mataki da suka ce nuna goyon baya ne ga Falasɗinawa a Gaza

  20. Fararen hula ake kashewa a kowace rana - Wani babban jami'i sojin Ukraine

    Wani babban jami'in soji a rundunar sojin Ukraine, Manjo Volodymyr Omelyan ya bayyana harin Dobropillya a matsayin "wanda aka saba gani".

    "A wannan kuma an yi amfani da makami mai linzami ne. Amma akwai hare-haren bom na yau da kullum a yankin Donetsk," kamar yadda ya shaida wa BBC.

    "A kowace rana ana kashe fararen hula tare da raunata su."