Sojoji sun kuɓutar da mutum 86 da aka yi garkuwa da su a Borno
Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce sojojinta sun samu nasarar kuɓutar da mutum 86 daga masu garkuwa da mutane, sannan ta kama ƴanbiniga da masu taimaka musu guda 29 a sassa daban-daban na jihar Borno da ke arewa maso gabas.
A wata sanarwa da kakakin aikin soji na musamman na Hadin Kai, Sani Uba ya fitar, ya ce sojojin bataliya ta musamman ta 135 a ƙarƙashin sashe na 2 ne suka yi artabu da ƴan Boko Haram a ranar 9 ga watan Nuwamba a yankin Dutse Kura.
"Ƴan Boko Haram sun kai hari ne kan matafiya a hanyar Buratai zuwa Kamuya. Nan ne sojojinmu suka kai ɗauki, wanda ya sa maharan suka tsere, amma sai sojojin suka bi bayansu a hanyar zuwa Mangari har suka ci ƙarfinsu," kamar yadda sanarwar ta nuna.
Ya ce daga bisani sojojin sun baza ƙomarsu a dazukan, inda suka samu nasarar gano sansanin mayaƙan guda 11, "inda muka ceto mutum 86 ciki har da mata da ƙananan yara, sannan muka ƙwato bindigar AK-47 da harsasai da sauran makamai."