Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya Asabar 10/08/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, Asabar, 10/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bibiyar shafin namu, a nan ne kuma za mu rufe shi a wannan rana.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    A madadin abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Birtaniya ta tuhumi kusan mutum 350 kan zanga-zangar ƙyamar baƙi

    ..

    Asalin hoton, PA Media

    Masu gabatar da ƙara na tuhumar kusan mutum 350 kan hannu a zanga-zangar ƙyamar baƙi da ta ɓarke a wasu sassan Ingila da Ireland ta Arewa a makon da ya gabata.

    'Yansanda sun ce an zaɓi ma'aikata na musamman da bibiyar masu fafutika ko fitattun mutane a kafar intanet, waɗanda ke yaɗa kalaman ƙiyayya da tunzura mutane a shafukansu na intanet.

    Masu zanga-zangar a arewacin Ireland, sun ɗarsa tsoro da fargaba a zukatan baƙi 'yan cirani a faɗin ƙasar.

    An gudanar da zanga-zangar nuna wariyar launin fata a garuruwa da dama a Birtaniya.

  3. Alkalin kotun ƙolin Bangladesh ya sauka daga muƙaminsa

    Alkalin kotun ƙolin Bangladesh ya yi murabus, shi ne babban jami'in gwamnati da ya aje muƙaminsa, tun bayan tserewar Firaministar ƙasar, Sheikh Hasina daga ƙasar a makon da ya wuce.

    Obaidul Hassan shi ya yanke hukunci da umarnin aiwatar da hukuncin kan abokan hamayyar Ms Hasina.

    Shi ma dai gwamnan babban bankin ƙasar, Abdul Rouf Talukder, ya ajiye aikinsa, kodayake hukumomi ba su amince da matakin nasa ba.

    Mulkin Sheikh Hasina ya zo ƙarshe bayan shafe mako guda 'yan ƙasar na zanga-zangar da ta janyo mutuwar ɗaruruwan mutane.

  4. Gwamnatin jihar Plateau ta sake sassauta dokar taƙaita zirga-zirga

    .

    Asalin hoton, Caleb Muftwang

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang

    Gwamnatin jihar Plateau ta sake sassauta dokar taƙaita zirga-zirga da ta sanya a yankin Jos-Bukuru.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan jihar, Gyang Bere, ya fitar ya ce an ɗauki matakin ne lura da ingantuwar yanayin tsaro a yankin sakamakon yadda mazauna yankin suka bayar da haɗin kai wa dokar.

    Sanarwar ta ce a yanzu mazauna unguwar za su iya fita harkokin kasuwancinsu tun daga ƙarfe 10:00 na safe zuwa ƙarfe 6:00 na maraice.

    Sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga yau Asabar 10 ga watan Agusta, kamar yadda sanarwar ta yi bayano.

    Jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da aka sanya dokar taƙaita zirga-zirga bayan ɓarkewar tarzoma a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa jihar da aka fara gudanarwa tun daga ranar 1 ga wannan wata na Agusta.

  5. Gwamnatin Kaduna ta haramta duk wata zanga-zanga da hukumomi ba su sahale mata ba

    ..

    Asalin hoton, Kaduna Gov/X

    Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargaɗin cewa ba za ta sake amincewa da duk wani nau'in zanga-zangar da ba ta samu sahalewar jami'an tsaro ba.

    Cikin wata sanarwa da kawamishinan al'amuran tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne saboda zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar.

    Ya ƙara da cewa gwamnati ta fahimci yadda wasu ɓata-gari suka saje cikin masu zanga-zangar da aka gudanar a baya-bayan nan a jihar, inda suka aikata ɓarna mai yawa.

    An dai samu arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a jihar bayan da aka yi zargin ɓata-gari sun saje cikin masu zanga-zangar waɗanda suka haddasa ɓarna a faɗin jihar.

    Lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar ta-ɓaci a jihar, kodayake daga baya an sassauta dokar.

    Sanarwar ta ce ''zanga-zangar da ta auku a jihar daga rana 1 zuwa 5 ga watan Agusta alamu ne na yadda ɓata-gari suka yi amfani da ita wajen tayar da tarzoma, waɗanda kuma har yanzu a shirye suke domin shiga kowace irin zanga-zanga''.

    ''Haka kuma bayanan sirrin da muka samu na nuna cewa waɗanan ɓata-garin na nan suna ɗaukar ƙaanna yara da wasu mutane domin shiga cikin kowace irin zanga-zanga a faɗin jihar'', in ji sanarwar.

  6. Masar da Qatar sun yi Allah-wadarai da harin Isra'ila a makarantar Gaza

    Hari a makarantar Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashen Masar da Qatar, da ke shiga tsakani a yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza, domin dakatar da bude wuta sun yi Allah-wadarai da harin da Isra'ila ta kai a wata makaranta a Gaza.

    Ma'aikatar harkokin waje ta Isra'ila ta ce harin ya nuna Isra'ila ba ta da niyyar kawo karshen yakin.

    Qatar ta bukaci da a gudanar da bincike na duniya a kan hare-haren na baya-bayan nan.

    A farkon makon nan Qatar da Masar suka bi sahun Amurka wajen kiran da a koma tattaunawar dakatar da bude wuta da kuma sakin wadanda aka yi garkuwa da su.

    A ranar Alhamis aka tsara komawa bakin tattaunawar

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za su tura wakilai zuwa tattaunawar yayin da Hamas ta ce tana nazari kan sabon tayin tattaunawar.

  7. Zaftarewar ramin shara ta kashe mutane a Uganda

    Landfill Ethiopia

    Asalin hoton, Reuters

    Mutum akalla takwas ne da suka hada da yara biyu ake fargabar sun rasu bayan da wani ramin da ake zubar da shara ya rufta, inda ya binne gidaje da dabbobi a arewacin babban birnin Uganda, Kampala.

    Jami'ai a babban birnin sun ce bayan wadanda suka mutu, an kuma kwantar da mutum goma sha hudu a asibiti saboda raunukan da suka ji, amma kuma ba a bayyana irin yanayin da suke ciki ba.

    Ana can ana ci gaba da aikin ceto a inda lamarin ya faru, inda jama'ar gari da jami'an gwamnati da 'yansanda ke ta fama.

    Wasu daga cikin jama'ar gari na amfani da hannunsu zalla, wasu kuwa da kayan aiki na gargajiya, yayin da jami'an gwamnati ke amfani da manyanmotoci na tono wajen aikin zakulo wadanda ke da sauran numfashi ko gawarwaki.

    Binciken farko-farko ya nuna cewa ga alamu ruwan sama mai yawa ne ya haddasa zaftarewar.

    Daman an yi gargadin cewa wajen yana cike da hadarin zaftarewa.

  8. An yanke wa sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulki a Sierra Leone hukunci

    Sojoji a mota

    Asalin hoton, EPA

    Wata kotun soji a Saliyo (Sierra Leone) ta yi wa sojoji 24 hukuncin daurin shekaru masu yawa saboda samunsu da laifi hannu a yunkurin juyin mulki a watan Nuwamba na 2023.

    Kotun ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari da ya kai har shekara 120 a kan yunkurin kifar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Julius Maada-Bio.

    A yayin da alkalin kotun ke sanar da hukuncin jiya Juma'a da daddare, iyalan sojojin da dama sun fashe da kuka.

    Wadanda aka yanke wa hukuncin suna daga cikin mutum 27 da aka gurfanar a gaban kotun sojin a kan rawar da suka taka a yukurin juyin mulkin na watan Nuwamba, wanda a lokacin mutane dauke da makamai suka kai hari kan cibiyoyin tsaro, lamarin da ya kai ga kashe mutum sama da 20.

    An tuhume su ne da laifi 88, da ya hada da na bore da shirya makarkashiya don kisan kai.

    An wanke tare da sallamar hafsan sojin daya.

    An yi yunkurin juyin mulkin ne 'yan watanni bayan an sake zabar Shugaba Maada Bio a wa'adi na biyu na shugabancin kasar ta yammacin Afirka.

    An tuhumi wanda ya gada a mulki Ernest Koroma da laifin cin amanar kasa, a yunkurin juyin mulkin, amma kuma ya musanta hannu a ciki.

  9. An yi addu'ar musamman ta neman sauƙin matsin rayuwa a Kano

    Masu addu'o'i

    Asalin hoton, Rabi'u Shamma/Facebook

    Duk da kiraye-kirayen da aka rinƙa yi na neman a ɗage addu'o'i na musamman da aka tsara za a fara yi daga yau Asabar a Najeriya, bayanai sun nuna cewa an gudanar da addu'ar a masallacin, gidan Isiyaku Rabi'u da ke Goron Dutse, a yankin, ƙaramar hukumar Dala, da ke Kano.

    Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa, wani mai amfani da shafukan sada zumunta da muhawara a sanya a shafinsa na Facebook cewa: ''Ana karatun Qur'ani daga nan masallacin Khalifa Isyaku Rabiu, Goron Dutse, Kano, domin addu'a kan halin da kasarmu ke ciki, Allah Ya sawƙaƙa mana, Amin.''

    Daman jaridar ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka shirya addu'ar ƙasa da za a fara yau Asabar 10 ga watan Agusta, 2024, a masallacin na Isiyaku Rabi'u, da kuma sauran jihohin ƙasar, Mubarak Ibrahim Lawan, ya sanar da cewa an fasa saboda dalilai na tsaro.

    Masu addu'a

    Asalin hoton, Rabi'u Shamma

    Ganin yadda zanga-zangar lumana da aka fara a Najeriyar ranar 1 ga watan nan na Agusta ta tsawon kwana goma ta rikiɗe a wasu jihohin ƙasar ta zama tarzoma inda aka inka sace-sace da ɓarnata dukiya ta gwamnati ta 'yan kasuwa da sauransu, har ma da kisa da raunata jama'a, wanna ya sa wasu suka yi, tunanin karkata ga addu;a domin samun sauƙi a kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

    A wani saƙo na bidiyo da ya fitar, a Kano, Mubarak, ya ce kwamishinan ƴansanda na jihar, da kuma darektan hukumar tsaro ta DSS shi ma na jihar sun ankarar da su cewa wasu ɓata-gari a ƙasar sun shirya tura wasu miyagu wajen taron addu'ar, domin cimma manufarsu.

    Ya ce, an yi zargin cewa za su jagoranci wasu matasa da za su riƙa kwashe kayan jama'a da na hukuma, da sace-sace, kamar yadda aka yi a baya a lokacin da aka fara zanga-zanga, a saboda haka ya ce sun fasa taron addu'o'in.

  10. Gwamnatin sojin Nijar ta kafe kan zargin Najeriya da yi mata zagon-ƙasa

    Janar Abdourrahmane Tchiani

    Asalin hoton, ORTN

    Gwamnatin Mulkin sojin Nijar ta tsaya kai da fata, cewa lalle makwabciyarta Najeriya na bayar da mafaka ga masu shirya mata zagon-ƙasa duk kuwa da musanta hakan da Najeriyar ta yi.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, Janar Abdourrahmane Tchiani ya yi zargin cewa, ƙasashen Benin da Najeriya da Chadi na hada baki da jami’an leken asiri na ƙasar Faransa don kifar da gwamnatinsa, zargin da gwamnatin Najeriya ta ce bai da tushe ko makama.

    To amma a hirarsa da BBC, ministan harkokin Nijar Bakari Ya'u Sangare ya ce duk abin da Janar Tchiani ya fada gaskiya ne.

    Ministan ya ce suna da tarin hujjoji na maganganun da suka yi kan cewa Najeriya na taimaka wa wajen yi mata zangon-ƙasa, ''muna da hanyoyin samun bayanai,'' in ji shi.

    A zargin da ya yi a baya shugaban mulkin sojin na Nijar ya ce wasau daga cikin Turawan da suka kora daga Nijar, suna nan cikin Najeriya suna horar da 'yan ta'dda kuma suna taimaka musu da makamai da dabara iri-iri da za su tayar wa da Nijar hankali.

    Najeriya dai ta buƙaci hukumomin na Nijar su ba ta cikakken bayani kan zargin da suke yi cewa akwai wani mutum da ke jagorantar yi wa Nijar din tawaye da ke da sansani a wasu jihohin kasar.

  11. Wata tawagar masu rajin kishin Najeriya ta gana da Shugaba Tinubu kan sauya kundin tsarin mulki

    Shugaba Tinubu da tawagar Anyaoku

    Asalin hoton, NAN

    A Najeriya, wasu fitattun masu rajin kishin ƙasa daga sassa daban-daban, ƙarkashin jagorancin tsohon babban sakataren ƙungiyar ƙasashe renon Ingila (Commonwealth), Cif Emeka Anyaoku, sun shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki matakin samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Tawagar mutanen ta gabatar da buƙatar hakan ne, a lokacin da ta ziyarci Shugaban a Abuja, inda ta ba shi shawarwari da dama game da gaggan matsalolin da suka dabaibaye Najeriyar.

    Ɗaya daga cikin 'yan tawagar, Kwamared Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya sheda wa BBC cewa, sun bai wa Tinubun shawarwarin ne musamman batun kundin tsarin mulki saboda suna ganin yana daga cikin abubuwan da ke haifar wa da ƙasar matsala maimakon magance ta.

    Sanatan ya ce, matsalolin sun danganci tsaro da siyasa da zamantakewa tsakanin al'ummomin ɓangarorin ƙasar daban-daban da kuma ɓarna da ya ce ana yi a gwamnati.

    Ya ce tawagar tasu na ganin bai kamata a ce Najeriya tana da majalisun dokoki na tarayya biyu ba, wato ta dattawa da kuma ta wakilai, kamata ya yi a ce guda ɗaya ce, sannan ga ministoci wajen hamsin, kuma ga majalisun dokoki na jihohi duka ya ce wannan bai kamata ba, ganin irin ɗimbin kuɗaɗen da ake kashewa a kan haka.

    Kwamared Sani ya ce, kamata ya yi a riƙa amfani da kuɗaden ƙasar wajen ayyukan cigaba da kuma taimaka wa talakawa.

    Sannan ya ce akwai buƙatar samar da ma'aikatun tsaro na yankuna, domin hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ake fama da ita.

    Tsohon sanatan ya ce, suna ganin muddin ba a samar da sabon kundin tsarin mulki ga najeriyar ba to haka za a yi ta tafiya a ƙasar.

    Haka kuma ya ce tawagar tasu ta yi wa shugaban na Najeriya magana tare da ba shi shawara kan maganar zanga-zangar da ake yi a ƙasar, inda suka tuna masa cewa talakawa suna da 'yanci a ƙarƙashin mulkin dumukuraɗiyya su yi zanga-zanga , 'abin da ya kamata ya yi shi ne ya gayyato shugabannin da suka shirya ta ya tattauna da su a yi maslaha.''

    ''Sannan mun jawo hankalinsa a kan jami'an tsaro duk duniya akan yi zanga-zanga, jamian tsaro ya kamata su tsagaita amfani da makami wajen kwantar da mutane, akwai hanyoyi da yawa da za a kwantar da tarzoma ba tare da an dauki rayukan mutanne ba, '' in ji shi.

    Ya ce shugaban na Najeriya ya yi alƙawarin duba shawarwarin da suka ba shi, tare da gayyatar jagoran tafiyar Chief Emeka Anyaoku nan gaba kadan kan batutuwan.

  12. Shugaban Koriya ta Arewa ya ziyarci al'ummomin da ambaliya ta yi wa ɓarna a ƙasarsa

    Shugaba Kim Jong Un a cikin mota

    Asalin hoton, Rodong Sinmun

    Bayanan hoto, Shugaba Kim Jong Un, yana bi ta ruwa domin ya ga irin ɓarnar ambaliya da guguwa suka yi

    Kafar watsa labaran Koriya ta Arewa ta ce shugaban ƙasar, Kim Jong Un, ya kai ziyara ɗaya daga cikin yankunan da aka yi mummunar ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa.

    Rahotanni na cewa an ga yadda shugaban yake tsara yadda za a kwashe mutanen yankin da yawansu ya kai dubu 15, zuwa babban birnin ƙasar tare da sake gina sababbin gidaje a inda lamarin ya faru.

    Sai dai hukumomin ƙasar ta Koriyar ta Arewa ba su bayar da rahoton yawan mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba, illa dai kafar watsa labaran ƙasar ta bayyana lamarin da mummunan hadari.

  13. Rasha ta ɗauki mataki mai tsanani bayan harin da Ukraine ta kai mata na bazata

    Wani gini da aka kai hari a Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta gabatar da wani sabon tsarin tsaro mai tsanani a yankuna uku da ke kan iyakar Ukraine, a yunƙurinta na mayar da martanin hare-haren bazata da Ukraine ta kai a yankin Kursk.

    Za a aiwatar da matakan da Moscow ta bayyana da na daƙile yan ta'adda,a yankunan Bryansk da Kursk da kuma Belgorod a cewar hukumomin na Rasha.

    Matakan sun haɗa da taƙaita zirga-zirgar jama'a da motoci tare da ci gaba da aikin kwashe mutanen yankin.

    Ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙoƙarin kwashewa ta ce babu wani abin tashin hankali, komai yana tafiya yadda ya kamata, ''mun samu tikiti kyauta.''

  14. Shugaban Panama ya yi tayin sasanta dambarwar siyasar Venezuela

    Shugaban Venezuelan, Nicolas Maduro

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ana rikici ne kan zaɓen da Shugaba Maduro na Venezuela ya ce shi ne ya sake ci

    Shugaban ƙasar Panama,Jose Raul Mulino ya ce ya nemi sauran ƙasashen Latin Amurka da su mara masa baya domin tattaunawa kan matsalar siyasar Venezuela.

    Shugaban Venezuelan, Nicolas Maduro ya kafe cewa shi ne ya sake cin zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar, sai dai jagoran hamayyar ƙasar da mafi yawancin ƙasashen Latin Amurka ba su amince da sakamakon ba.

    Shugaba Mulino ya ce shugabannin ƙasashe bakwai a yankin sun amince za su halarci taron tattaunawar, kodayake ba a tsayar da rana da lokacin yin zaman ba.

  15. Falasɗinawa aƙalla 90 sun mutu a harin da Isra'ila ta kai kan makaranta a Gaza

    Hari kan makaranta a Gaza

    Asalin hoton, AFP

    Majiyoyin Falasdinawa a Gaza sun yi zargin cewa an yi asarar rayuka da dama bayan hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a Zirin Gaza.

    Hukumar kare fararen hula ta Hamas ta ce aƙalla mutum 90 ne suka mutu tare da jikkata gwammai a harin bam da Isra'ila ta kai kan makarantar al-Tabi'in da ke gundumar Daraj.

    Kamfanin dillacin labaran Falasdinawa ya ce an shawo kan wutar da ta tashi a yankin sakamakon harin bam din.

    Sojojin Isra'ila sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai sun ce sun kai harin ne saboda sansanin Hamas da suka ce yana makarantar.

  16. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Asabar.

    Ni Muhammad Annur Muhammad zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Ɗanyen kasko ba ya kai ruwan wanka banɗaki