Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu, za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni da bayanai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya 08/06/25
Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu, za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.
Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Kara a Birnin Kebbi, ta lalata shaguna da kuma dukiyoyi da dama.
Gobarar wadda ta soma a safiyar yau Lahadi, ta janyo asarar kayayyaki da kuɗinsu ya kai na miliyoyin naira.
Wasu shaidu sun bayyana cewa wutar ta yaɗu da sauri kafin a samu zuwan masu kashe gobara, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
"Mun ga hayaki na tashi ko ta ina, nan da nan wutar ta karaɗe yawancin shaguna da ke cikin wannan kasuwa," in ji wani ɗan kasuwa mai suna Musa Bello.
Ba a samu rahoton asarar rai ba a gobarar, sannan zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa ta ba.
Gwamnatin jihar Kebbi ta jajantawa waɗanda lamarin ya shafa a wata sanarwa da ta fitar.
Ta nuna takaicinta kan afkuwar lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutum huɗu sun mutu sakamakon ruftawar ramin da suke haƙar ma'adinai a arewa maso yammacin ƙasar Kenya.
Jami'ai a lardin West Pokot sun ce ɓaraguzai sun ɗanne waɗanda suka mutum, lokacin da ramin ya rufta.
An kuma garzaya da wasu biyar da suka jikkata zuwa asibiti.
An daɗe ana nuna damuwa kan rashin ɗaukar matakan kariya na haɗari a wajen haƙar ma'adinai a yankin, inda rashin matakan da kuma rikice-rikice suka janyo rufe wuraren haƙar ma'adinai da dama.
Ellie ta ce da farko ta ji farin ciki mara misaltuwa.
Ta haihu a gida, ba tare da maganin kashe zafi ba, ta kuma yi farinciki sosai da zama uwa.
Kuma duk da ba ta samu isashen bacci cikin kwanaki uku ba, ta na ganin cewa ba ta bukatar yin bacci.
''Yadda zan iya bayyana abin da naji shi ne kamar na tashi daga wani mugun mafarki, ba na iya bam-bance mene ne mafarki kuma menene zahiri,'' in ji ta. ''Kuma wannan yanayin da nake ji ya ƙi wucewa.''
Dubun-dubatar mutane ne suka fita kan tituna a Madrid, babban birnin Sifaniya kan zargin gwamnatin Firaminista Pedro Sánchez mai marasa rinjaye, da cin hanci.
Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Party ce ta shirya zanga-zangar, inda shugabanta, Alberto Nuñez Feijóo ya yi kiran gudanar da zaɓen wuri.
Ya zargi Mista Sánchez da kasancewa dumu-dumu cikin badaƙaloli da dama.
Mista Sánchez da ƙawayensa sun ce an shirya zanga-zangar ce kawai don ɓata wa gwamnati suna.
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tayin shiga jam'iyyar APC mai mulki.
Ministan ya yi tayin ne ranar Asabar a garin mahaifarsa ta Maradun, lokacin da ya karɓi bakuncin dubban magoya bayansa da suka kai masa gaisuwar barka da sallah.
Matawalle wanda ya kasance tsohon gwamnan Zamfara, ya ce APC jam'iyya ce ta mutanen kirki da dattako, don haka ya shawarci Dauda Lawal ya shiga jam'iyyar.
Ministan ya ce maimakon gwamnan ya bi ta ɓarauniya hanya, gara ya fito fili ya bi hanyar da ta dace wajen shiga APC.
"Ba ni da matsala da gwamnan idan yana son shiga APC. Ya zo ya bi sahun masu yunkurin kawo ci gaba a ɓangaren tsaro da zaman lafiya da kuma ayyukan raya ƙasa," in ji Matawalle.
Ya kuma ce shugaba Bola Tinubu jagora ne na gari mai son kawo zaman lafiya a kodayaushe, inda ya mayar da hankali wajen ayyukan da za su kawo cigaba a ƙasar.
Mutum tara sun rasu sakamakon hatsarin mota da ya afku a ƙauyen Kyaramma, da ke karamar hukumar Ringim na jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar bayan da wasu motoci ƙirar Golf suka garu, inda mutane da dama suka jikkata.
Sanarwar da mai magana da yawun ƴan sandan Jigawa, Shiisu Adam ya fitar, ta ce ɗaya daga cikin motocin wanda wani mai suna Adamu Sanusi ke tukawa, ta fito ne daga Hadejia zuwa garin Gujungu a Abuja lokacin da lamarin ya faru.
Binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa motocin sun yi taho mu-gama ne bayan da mota ta ƙwace wa ɗaya daga cikin direbobin, abin da ya janyo duka suka kauce daga kan hanya.
Sanarwar ta ce ƴan sanda sun kai taimako nan take, inda suka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ringim don kula da su.
Da yake jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ransu, kwamishinan ƴan sandan jihar, CP A.T. Abdullahi ya buƙaci direbobi da su riƙa bin dokokin hanya da guje wa gudun wuce sa'a, da kuma tabbatar da cewa ababen hawansu na da ingancin hawa kan hanya.
An kama wani sojan Birtaniya da zargin yi wa wata mata fyaɗe a kusa da barikin sojojin Birtaniya a Kenya.
Lamarin wanda ya faru a garin Nanyuki - mai nisan kilomita 200 da arewacin Nairobi, babban birnin Kenya - ya biyo bayan zarge-zargen da suka gabata cewa wani sojan Birtaniya na da hannu a kisan wata mata a 2012.
Cikin wata sanarwa, ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce irin waɗannan "ɗabi'u" ba su da wurin zama a rundunar sojin ƙasar.
Yanzu dai hukumomin ƙasar na ci gaba da bincike kan lamarin.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya zargi wasu ƴan siyasa da ke ci a majalisar tarayya da ɗaukar nauyin hare-hare da ake kai wa jihar, inda ya ce ba za su lamunci hakan ba.
Gwamnan ya yi wannan zargi ne yayin tattaunawa a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels.
Duk da cewa bai bayyana sunayen ƴan siyasar ba, gwamnan ya ce kwamitin da ya naɗa domin yin binciken kan batun kai hare-haren ya gano akwai sunayen manyan ƴan siyasa, inda ya sha alwashin ɗaukar mataki nan take idan ya karɓi rahoton kwamitin a mako mai zuwa.
"Abin takaici yadda wasu manyan ƴan siyasa ke ci gaba da bai wa ƴan bindigar da ke kai hare-haren mafaka da kuma saya musu makamai. Za mu ɗauki mataki tun da ba su damu da irin rayuka da suke salwantar wa ba," in ji gwamna Alia.
Jihar ta Benue dai na fama da ƙaruwar hare-hare a ƴan makonnin nan, inda ƙananan hukumomi da dama da ke fuskantar mummunan tashin hankali da ya janyo asarar rayuka da dama.
Wani ɗan bindiga ya harbi fitaccen ɗan majalisar dattawan ƙasar Colombia Miguel Uribe a babban birnin ƙasar Bogota.
Bidiyon da aka yi ta yaɗa wa a Intanet ya nuna yadda harsashi ya samu kan ɗan takarar shugaban ƙasar yayin da yake jawabi ga wasu mutane.
Nan take jam'iyyarsa ta Centro Democratico mai ra'ayin mazan jiya da gwamnati suka yi Alla-wadai da harin.
Mista Miguel Uribe na cikin mawuyacin hali, kuma babu cikakken bayani kan yanayin da yake ciki da kuma yawan waɗanda suka kai harin.
Ƴan sanda sun kama wani da ake zargi.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio yayi Alla-wadai da harbin da aka yi, yana mai kira ga shugaban ƙasar mai barin gado Gustavo Petro, da ya rage kalaman ta da hankali a yaƙin neman zaɓe.
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai wa iyalan sojijin da aka kashe da kuma waɗanda aka jikkata a fagen daga a yaƙi da ƴan ta da ƙayar-baya a arewa maso gabas, tallafin naira miliyan 100.
Gwamnan ya bayar da tallafin ne ranar Asabar yayin liyafar cin abinci a daidai lokacin da ake ci gaba da bukukuwan sallah, inda babban hafsan sojin ƙasa Laftanar-Janar Olufemi Oluyede da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar suka halarci liyafar a barikin sojoji na Maimalari a Maiduguri.
Zulum ya gabatar da chekin kuɗin na naira miliyan 100 ga hannun kwamandan dakarun Haɗin-Kai, Manjo-janar Abdussalam Abubakar.
Ya bayyana cewa kowane soja da aka raunata a fagen daga zai samu naira 500,000, yayin da za a raba sauran kuɗin ga iyalan sojojin da aka kashe.
Gwamna Zulum ya kuma yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewarsu, inda ya ce ba za a taɓa manta irin sadaukarwar da suka yi ba.
"Jajircewarku a fagen daga, duk da irin barazana da kuma wahala ba zai tafi a banza ba. Muna ƙara godiya bisa amanar tsaron ƙasa da kuka ɗauka," in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mara wa sojojin baya.
"Gwamnatin Borno za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da sojojin Najeriya da kuma dukkan jami'an tsaro a yaƙi da ƴan ta da ƙayar-baya, da kuma sake gina garuruwan mu don samar da zaman lafiya da makoma mai kyau," in ji gwamna Zulum.
Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da tsohon mai ba shi shawara kuma abokinsa, Elon Musk.
Shugaba Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta NBC cewa Mista Musk zai fuskanci "mummunan sakamako" idan har ya sake ya ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓen ƴan jam’iyyar Democrat don kalubalantar ƴan majalisar Republican da suka goyi bayan kudurin kashe kuɗinsa, da Elon da ya yi ta caccaka.
A baya dai Trump ya yi barazanar sake duba kwangilolin gwamnati da kamfanonin Mista Musk.
Yawancin ƴan Republican sun nuna goyon bayansu ga Trump.
Ƙwarewa na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke jawo mummunan rauni ko mutuwa a ƙananan yara, musamman waɗanda ba su kai shekara biyar ba.
Ƙwarewa na iya faruwa cikin ƙanƙanin lokaci ko da a lokacin cin abinci, lokacin da yaron yake shan mama, lokacin wasa, ko ma lokacin barci.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, dubban yara a faɗin duniya na rasa rayukansu duk shekara ta dalilin ƙwarewa ko shaƙewa saboda hanyoyin numfashi ne ke toshewa.
Dalililin haka ne BBC ta tuntuɓi Dr. Aisha Bako, wata likitar yara a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, wadda ta bayyana muhimman matakan taimako da kowanne iyaye ko mai kula da yara ya kamata ya sani idan yaro ya shaƙe.
Rasha ta sake kai hari birnin Kharkiv, da ke arewa maso gabashin Ukraine, a wannan karon da rana, bayan hare-haren da aka kai cikin dare.
Jami'ai sun ce wasu bama-bamai sun fashe a tsakiyar birnin, inda suka kashe mutum guda, tare da jikkata aƙalla mutum 19.
Shugaba Zelensky ya kira hare-haren da ake kai wa fararen hula da "ta'addanci tsantsa".
Ya ce hare-hare ne na gan-gan da zummar lahanta ƙasar, yana mai watsi da duk wani iƙirari na cewa hare-haren ramuwar gayya ne.
Masu bibyar mu barkan ku da warhaka.
Ku kasance da mu domin kawo muku labarai da rahotanni daga Najeriya da sauran ƙasashen duniya.