Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Bukukuwan Sallah da gobara da ta laƙume shaguna 300 a kasuwar waya a Kano
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Tinubu ya yi Sallah a Legas, Shettima a Abuja
Tinubu ya karrama Bill Gates da lambar yabo ta CFR
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karrama ɗaya daga cikin hamshaƙan attajiran duniya, Bill Gates da lambar yabo ta CFR.
An yi bikin karrama attajirin ne ranar Talata a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Attajirin shi ne mai fitaccen kamfanin fasahar nan na Microsoft da kuma gidauniyar Bill Gates.
A watan da ya gabata ne dai attajirin ya alƙawarta rabar da kashi 99 cikin 100 na dukiyarsa da aka ƙimanta za ta kai dala biliyan 200 ga marasa galihu nan da 2045.
Najeriya na neman dala biliyan 25 don gina bututun gas zuwa Turai - Shettima
Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin aikin shimfiɗa bututun gas zuwa nahiyar Turai.
Mataimakin Shugaban Najeriya kashim Shettima ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban kamfanin Vitol Group a fadar shugaban ƙasa ranar Litinin.
Aikin bututun wanda zai bi ta ƙasar Morocco, za a yi amfani da shi wajen sayar wa ƙasashen Turai iskar gas, yayin da suke yunƙurin rage dogaro da Rasha a fannin makamashi.
Mataimakin shugaban ya nemi masu zuba jari na ƙasashen duniya da su antaya kuɗaɗensu a Najeriya, yana mai cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu "na aikin saita Najeriya".
'Gobara ta laƙume shaguna kusan 300 a kasuwar waya a Kano'
Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar sayar da wayoyi da ke birnin Kano ta haifar da ɗimbin asarar dukiya.
Shugaban kasuwar Amb. Jamilu Bala Gama ya shaida wa BBC cewa gobarar ta kwashe sa'o'i shida zuwa bakwai tana ci.
Ya ƙara da cewa gobarar ta shafi shaguna fiye da 300 a kasuwar, inda ta fi ƙamari a ɓangare masu sayar da wayoyin da kayan gyaran wayoyin.
''An yi ƙazamar asara ta dukiya da kadara, a shago guda za ka iya samun naira miliyan 500, wani ma har biliyan guda , kuma duka sun ƙone'', in ji shi.
Shugaban kasuwar ya ƙiyarta asarar da aka yi a gobarar da cewa ta kusa naira biliyan 100.
Kawo yanzu dai ba a san musababbanin tashin gobarar ba, kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta - CG Musa
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta.
Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas.
Mayaƙan ƙungiyar - wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka - sun kashe jami'an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi.
'Jihohin da za a iya samun ambaliya a Najeriya cikin watan Yuni'
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta ce akwai yiwuwar a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, musamman na arewa ta tsakiyar ƙasar.
NiMet ta bayyana haka ne a cikin hasashen yanayi da ta yi na wannan wata na Yunin 2025, wanda ya kama a ranar Lahadin da ta gabata.
Rahoton na zuwa ne yayin da ƙasar ke ci gaba da jimamin wata mummunar ambaliyar ruwa da aka samu a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar ƙasar, wadda ake kyautata zaton ta yi sanadin rayuka sama da 500.
NiMet ta ce duk da cewa yanzu ne damina ke kankama a yankin arewacin ƙasar, amma "ana hasashen samun marka-markan ruwan sama a cikin ƙanƙanin lokaci a wasu jihohin arewacin ƙasar, musamman Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da kuma yankin Babban birnin tarayya (Abuja).
Kifewar kwale-kwale ta kashe mutum biyar a jihar Sokoto
Mutum bakwai ne suka rasu sakamakon kifewar kwalekwale a yankin ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a lokacin da matafiyan suka fito daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:30 na safiya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.
Nema ta ce bayanai sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin ruwan.
A watan Oktoban 2024 ma wani jirgi ya kife da kusan mutum 300 a yankin Mokwa na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriyar.
Kafin haka, mutum 24 ne suka mutu a kifewar wani jirgin a watan Satumban 2023 a jihar.
Lokaci ya yi da ya kamata a fara zaɓen wuri a Najeriya - Shugaban Sojoji
Babban hafsan rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nuna goyon bayansa kan ƙudirin zaɓen wuri da majalisar dattawan ƙasar ta gabatar.
Janar Olufemi Oluyede, ya ce hakan zai taimaka wa jami'an sojin da ake girkewa domin bayar da tsaro a ranar zaɓe.
Yayin da yake jawabi ga tawagar majalisar dattawa da suka kai ziyara shalkwatar tsaron ƙasar, ranar Alhamis, babban hafsan ya bayyana ƙudirin a matsayin abin da ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.
"Ayyukanmu a lokacin zaɓe shi ne samar da yanayi mai kyau ga ƴan ƙasa domin kaɗa ƙuri'unsu, kuma saboda wannan aiki yana da matuƙar wahala ga duk sanye da kayan sarki ya samu damar kaɗa ƙuri'a," in ji shi.
Gwamnatin Najeriya ta karɓi 'yan ƙasarta 147 da suka maƙale a Nijar
Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.
Mutanen da suka ƙunshi maza 129 da mata 17 da jariri ɗaya, sun sauka ne a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas ranr Laraba da misalin ƙarfe 5:20 na yamma.
Nijar ce babbar hanyar da mazauna yammacin Afirka ke yin zango a yunƙurinsu na shiga ƙasashen Libya da Tunisia domin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.
Wannan dalilin kan jawo mutane da dama su maƙale a ƙasar ta yadda sai wasu ƙungiyoin ƙasashen duniya da gwamnatoci sun agaza musu domin komawa gida.