Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. Laraba 6 ga Agustan 2025

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Laraba.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Da dama daga cikin ma'aikatan gwamnatin Najeriya ba su da tarbiyya - Sanusi II

    Muhammadu Sanusi II

    Asalin hoton, Kano Emirate

    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya zargi da dama daga cikin ma'aikatan gwamnatin Najeriya da aikata cin hanci da rashawa saboda "rashin tarbiyya tun daga tasowarsu".

    Da aka tambayi sarkin ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Laraba dangane da cin hanci da rashawa, Sanusi ya ce da yawa ba a koya musu yin gaskiya da riƙon amana ba.

    "Da dama daga cikin mutanen da ke riƙe da ofisoshin gwamnati ba su da wannan tarbiyyar, mafi yawa na shiga gwamnati ne bisa dalilai marasa kyau," in ji shi.

    "Ina ganin an rusa kusan baki ɗayan ɗabi'un kirki na ƙasar nan. Marasa tarbiyya ne suke mulkar mu, waɗanda ba su da wani abin alfahari kuma ba su da niyyar barin wani abin alfahari a bayansu.

    "Mutane ne da ke alfahari kawai da yawan dukiyarsu, da yawan gidaje, da yawan jiragen da suka mallaka. Ba su taɓa tunanin cewa mutane na yi musu kallon ɓarayi ne.

    "Ba matsalar mutum ɗaya ba ce, shugaban ƙasa ko gwamna. Ku duba yadda shugabannin addininmu suka zama 'yan bambaɗanci, su ma sarakuna suka kiɗime. Kusan kowa ya auka cikin wannan ruɗanin."

  3. Iyalan 'yanwasan Kano 22 da suka rasu za su samu kyautar miliyoyi da fili

    Gwamnatin Kano

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce za ta bai wa iyalan 'yanwasan nan 22 'yan asalin jihar kuɗaɗe da filaye a matsayin gudummawa bayan rasuwarsu a kan hanyar komawa gida daga jihar Ogun.

    Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar a yau Laraba ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarni a bai wa iyalin kowane mamaci naira miliyan 11,709,375 jimilla da kuma fili.

    Da yake magana yayin zaman majalisar zartarwa, gwamnan ya kuma yi alƙawarin bai wa waɗanda suka tsira daga hatsarin motar naira miliyan 3,709,375 jimilla da kuma fili.

    Sanarwar ta ce wasu daga cikin kuɗaɗen na gudummawa ne, waɗanda Uwargidan Shugaban Ƙasa Remi, da ɗanmajalisa Sagir Koki, da gwamnatin jihar Ogun, da ƙungiyar wasannin Vollyball ta ƙasa suka bayar.

    Gwamnan Kano

    Asalin hoton, Kano State Government

  4. Ku kawo mana ƙorafin gurɓatattun ƴansanda - CP Bakori

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Rundunar 'yan sandan Kano ta shawarci al'umma su kai mata rahoton duk wani ɗan sanda da suke zargin yana karɓar cin hanci don haɗa baki ko rufa asirin wasu ɓata-gari ko masu aikata laifi a yankunansu.

    Matakin na zuwa ne bayan wani matashi ya wallafa wani bidiyo wanda a ciki ya yi manyan zarge-zarge ga wasu 'yan sanda a unguwarsu ta Sheka.

    Matashin ya yi zargin cewa wasu ɓata-garin 'yan sanda a yankin nasu suna zuwa su karɓi toshiyar baki a wajen dillalan ƙwaya da masu aikata laifi, tare da kawar da kai ga abubuwan da suke yi.

    Ya kuma ce a wasu lokutan ma ana samun ɓata-gari a cikin 'yan sanda da ke kiran masu laifi su tsegunta musu cewa jami'an tsaro za su zo kame, lamarin da zai ba su damar arcewa.

    Matashin ya yi iƙirarin cewa irin wannan halayya ta sa da wuya a iya kawo ƙarshen matsalar faɗan daba da yaƙi da matsalar shan ƙwayan da suka addabi al'ummar Kano.

    Abin da ya sa kwamishinan 'yan sandan Kano ya ba da umarnin gudanar da bincike kan waɗanda ake zargi nan take.

    An daɗe ana zargin wasu ɓata-garin 'yan sanda da karɓar toshiyar baki ko 'return' daga masu aikata laifi kamar dillalan ƙwaya don kawar da kai daga abin da suke aikatawa.

    Ba a cika ganin 'yan sanda sun saurari ƙorari irin wannan ba, balle har ta kai ga gudanar da bincike.

    Sannan ya bai wa al'ummar Kano tabbacin cewa duk mai irin wannan ƙorafi ya kai wa rundunar, don ɗaukar mataki, ba tare da mutum ya fuskanci cusgunawa ba.

  5. Faransa na fama da bala'in gobarar daji 'mafi muni a tarihi'

    Gobarar daji

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Faransa ya bayyana gobarar dajin da ta tashi a kudancin Faransa a matsayin wani bala'i da ba a taba ganin irinsa ba.

    François Bayrou ya ziyarci yankin Aude, inda gobarar daji ta lakume wani yanki da ya fi birnin Paris girma.

    An tabbatar da mutuwar wata mata yayin da wani mutum ɗaya ya ɓace a daidai lokacin da jami’an kashe gobara 1,800 ke ƙoƙarin shawo kan gobarar.

    Magajin garin yankin Jonquières ya ce gobarar ta lashe kashi 80 cikin 100 na kauyen nasu.

    Mista Bayrou ya ce bala'in gobarar daji da ake fama da ita na da nasaba da ɗumamar yanayi da fari.

  6. Tinubu ya jajanta wa al'ummar Ghana kan mutuwar ministoci

    Tinubu da Mahama

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga takwaransa na Ghana John Mahama game da mutuwar ministocin ƙasar biyu a hatsarin jirgi yau Laraba.

    Hatsarin jirgin samfurin helikwafta ya yi sanadiyyar mutuwar Ministan Tsaro Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli Ibrahim Murtala Muhammed, da wasu mutum shida.

    "Wannan lokaci ne na alhini matuƙa ga 'yan'uwanmu maza da mata na Ghana," in ji Tinubu cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta.

    "Waɗannan mutanen sun mutu ne yayin da suke tsaka da hidimta wa ƙasarsu cikin alfahari. Najeriya na taya Ghana alhini a wannan lokaci na makoki."

    Tinubu ya yi addu'ar nema wa mamatan sauƙi da kuma rarrashin zukatan iyalansu.

  7. Italiya za ta gina gada mafi tsawo a duniya

    Wata gada

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Italiya ta amince da wani aikin gina gadar da ta fi kowacce tsayi a duniya, wacce za ta hada tsibirin Sicily da suaran kasar.

    Aikin wanda kudin aiwatar da shi zai kai sama da dala biliyan goma sha biyar, zai kusnshi layukan dogo guda biyu a tsakiya da kuma manyan hanyoyin zirga-zirgar motoci guda uku a kowane bangare.

    Ana sa ran kammala aikin gadar mai tsayin sama da kilomita uku, a shekara ta dubu biyu da talatin da biyu.

    Sai dai tsare-tsaren sun haifar da cece-kuce har da ma zanga-zanga a kasar, kan illar gadar da za ta yi kan muhalli da kuma tsadar aikin.

    Shekara hamsin da suka gabata ne aka kyankyashe shirin gina gadar.

  8. Tinubu ya bayar da umarnin ɓullo da inshorar lafiya ga tsoffin ma'aikata

    Shugabar hukumar pensho tare da Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Bayanan hoto, Shugabar hukumar pensho tare da Shugaba Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga masu ƙaramin ƙarfi da suka yi ritaya a ƙarƙashin shirin fansho na karo-karo.

    Shugaban Najeriyar ya bayyana matakin a matsayin muhimmin tsari na kare lafiyar jama'a da kuma tabbatar da ƙimar mutanen da suka yi ritaya.

    Tinubu dai ya bayar da umarnin ne bayan ya karɓi baƙuncin Ms Omolola Oloworaran, shugabar hukumar Fansho ta ƙasar a fadarsa.

    Sanarwar da Bayo Onanuga, Kakakin Shugaba Tinubu ya fitar, ta ambato shugaban ƙasar na neman shugabar hukumar Fansho da ta gaggauta biyan haƙƙoƙin ƴansanda da suka yi ritaya inda ya bayyana cewa tsaffin ƴan sandan sun cancanci su kasance cikin rayuwa mai inganci da kwanciyar hankali.

    Shugabar hukumar ta kuma yi wa Shugaba Tinubu ƙarin haske kan ƙoƙarin da ake yi na alkinta kuɗaɗen Fansho musamman la'akari da hauhawar farashi da ake fama da ita da kuma tsare-tsaren bijiro da tsarin ba da gudunmawar kuɗaɗen waje don bai wa ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje damar shiga tsarin na pensho.

  9. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama

    Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah (Hagu) da na muhalli, Murtala Mohammed (Dama)

    Asalin hoton, FB/Multiple

    Bayanan hoto, Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah (Hagu) da na muhalli, Murtala Mohammed (Dama)

    Ministan tsaron Ghana Dr Omane Boamah da na muhalli, Murtala Mohammed tare da wasu mutum shida sun rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a yau Laraba.

    Lamarin ya rutsa da ma'aikatan jirgin uku a hatsarin jirgin mai saukar ungulu wanda ya faru a yankin Ashanti.

    Shugaban ma'aikatan ƙasar Ghana Julius Debrah wanda ya yi jawabi ga al'ummar ƙasar ya umarci da a sassauto da tutoci domin nuna alhini.

    Tun da farko wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar da safiyar yau, ta nuna cewa an daina jin ɗuriyar jirgin - mai saukar ungulu - bayan katsewar sadarwarsa.

    Rahotonni sun ce mutanen da ke cikin jirgin sojin - mai lamba Z9 - na kan hanyarsu ta zuwa garin Obuasi mai arzikin ma'adinai domin halartar wani taro na ƙasa lokacin da hatsarin ya auku.

  10. Sunan Muhammad ya sake zama na ɗaya a Ingila da Wales

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
  11. Jirgin soji ya yi hatsari a Ghana

    Wani jirgi mai saukar ungulu da ke ɗauke da matuƙansa uku da fasinjoji biyar ya yi hatsari a yankin Ashanti na ƙasar Ghana da safiyar Laraba.

    Jirgin dai ya yi hatsarin ne bayan ya gaza tuntuɓar cibiyar da ke bibiyar jirgin.

    Hotuna da ake kyautata zaton na jirgin ne da ya kwalmaɗe suna ta yawo a soshiyal midiya.

    Akwai rahotanni da ke nuna cewa akwai jami'an gwamnati da ke cikin jirgin.

    Ana sa ran fadar shugaban ƙasar ta Ghana za ta yi wa ƴan jarida bayani dangane da abin da ke faruwa.

  12. Abin da ya sa aka ƙwace motar alfarma ta mawaƙin Ghana Shatta Wale

    Mawaƙin ya fusata kan yadda jami'an tsaro suka kai samame tare da bindigogi

    Asalin hoton, CHARLES NII ARMAH MENSAH/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Mawaƙin ya fusata kan yadda jami'an tsaro suka kai samame tare da bindigogi

    Hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati a Ghana ta ƙwace wata motar alfarma mallakin mawaƙin ƙasar Charles Nii rmah da aka fi sani da Shatta Wale.

    Hakan ya faru ne bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka da ma'aikatar shari'ar Amurka ta buƙaci hukumar ta Ghana ta ƙwace motar.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Talata, shugaban hukumar ya tabbatar wa BBC Pidgin cewa tuni suka ƙwace motar samfurin Lamborghini Urus da FBN ta ce an same ta ne ta hanyar aikata manyan laifuka.

    A cewar hukumar, sun alaƙanta wannan laifin ga wani ɗan Ghana Nana Kwabena Amuah wanda a yanzu haka yake tsare a gidan yarin Amurka bayan yanke masa hukuncin wata 86 saboda aikata miyagun laifukan da suka shafi kuɗi a Amurka.

    "Mun ƙwace motar daga hannun Charles Nii Armah da aka fi sani da Shatta Wale a gidansa da ke Trassaco a yayin wani samame."

    Sai dai mawaƙin ya nuna fushi kan yadda jami'an suka kai samamen tare da bindigogi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.

    Shatta Wale ya kuma zargi shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati da wuce gona da iri.

    Sai dai a martani da ya yi, hukumar ta ce "tsarin haka yake cewa jami'an bincike za su kasance da bindigogi a jikinsu a duk lokacin da suka kai samame."

    Hukumar ta ce mawaƙin ya roƙi jami'an da kada su yayata batun ƙwace motar tasa a shafukan sada zumunta saboda matsayinsa a ƙasar.

  13. Bajintar ɗaliban Najeriya a gasar Turanci ta nuna ingancin ilimin ƙasar - Tinubu

    Ƴanmatan Najeriya da suka haska a Birtaniya

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Bayanan hoto, Ƴanmatan Najeriya da suka haska a Birtaniya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya taya ƴanmatan nan uku da suka nuna bajinta a wata gasa ta TeenEagle da aka yi a Birtaniya.

    Ƴanmatan Nafisa Abdullahi mai shekara 17 ta haskaka a gasar Turanci yayin da Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15 ta fi kowa hazaƙa a muhawara da Hadiza Kashim Kalli ta lashe kyautar mafi fiƙira.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yaba wa matasan ƴan Najeriyar saboda bajintar da suka nuna a gasar .

    Ya kuma yaba wa makarantu da sauran cibiyoyin karatu inda ya ce irin waɗannan nasarori na bayyana yanayin ingancin da ilimi ke da shi a Najeriya.

    Shugaba Tinubu ya bayyana ilimi a matsayin tushen duk wani ci gaban ƙasa, abin da ya sa ma a cewarsa gwamnatinsa ke fifita ɓangaren tare da ganin ta kawar da duk wata matsala ta kuɗi da za ta hana ƴan ƙasar ci gaba da karatu ta hanysar tsarin tallafin karatu na NELFUND.

    Shugaban ƙasar ya kuma ƙarfafa wa Nafisa da Rukayya da Hadiza gwiwar mayar da hankali a karatu tare da yi masu fatan samun ƙarin nasarori a rayuwarsu.

  14. Abubuwa tara da kwamitin binciken kwamishinan Kano ya gano

    Ibrahim Namadi zaune kan kujera sanye da jar hula

    Asalin hoton, Ibrahim Namadi

    A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu, ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton bincikensa ga sakataren gwamnatin jihar.

    Wasu daga cikin manyan batutuwan da kwamitin ya gano sun haɗa da:

    • Kwamishinan ya amince ya tsaya wa mai lefin domin raɗin kansa a ranar 18 ga watan Yulin 2025.
    • Rantsuwa: Ibrahim Namadi ya yi rantsuwa kan belin a matsayinsa na kwamishina mai ci kuma ya yi alƙawarin cika dukkan sharuɗɗan beli har zuwa ƙarshen shari'ar.
    • Namadi ya fahimci cewa kwamishina kuma ɗan majalisar zartarwa na jiha ne kawai zai iya tsaya wa wani a harkar shari'ar bisa tanade-tanaden sharuɗɗan kotu.
    • Namadi bai yi takatsantsan ba: Kwamishinan bai yi takatsantsan ba kafin ya ɗauki wannan matsaya ta tsaya wa wani da ake zargi da laifi da ke fuskantar babbar tuhuma da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
    • Kwamishinan yana da cikakkiyar masaniyar haƙiƙanin girman tuhumar da ake yi wa mutumin da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
    • ‎Namadi ya saɓa dokokin gwamnatin Kano dangane da matsayarta da ke fili ta ƙyamar safarar ƙwaya da ta'ammali da ƙwayar da ɓata matasa da sauran laifuka da suka jiɓance su.
    • ‎Babu shaidar da ke nuna kwamishinan na da wata alaƙa da wanda ake tuhumar kafin yanzu.
    • ‎Kwamitin bai samu wata shaidar da ke nuna yin amfani da kuɗi ko wata kadara ba domin jan hankalin kwamishinan kafin ya aikata belin.
    • Kwamishinan bai ajiye ko kwabo ba na beli ciki kuwa har da naira 5,000,000 da ake magana akai. Wannan kawai yana ƙunshe ne a cikin takardar rantsuwar da wanda ake tuhumar ya rubuta.
  15. Motar agaji ta kashe Falasɗinawa 20 a Gaza - Hamas

    Wata uwa da ƴarta a Gaza

    Hukumar tsaron farar hula ta Hamas ta ce mutum ashirin aka kashe lokacin da wata babbar mota ta hantsila kan dandazon masu neman agajin abinci a Gaza.

    Zuwa yanzu dai ba a san abin da ya sa motar ta kife ba kusa da sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar yankin Falasɗinawa.

    Hamas ta zargi sojojin Isra'ila da tilastawa kwambar motocin agaji bi ta hanyoyin da ba su da tsaro don kai wa ga mutanen da ke fama da yunwa.

    Isra'ila dai ba ta ce komai ba kan batun.

    Hukumomin Jordan sun ce ƴan Isra'ila sun kai wa motocin agaji da ke kan hanyar zuwa Gaza hari yau Laraba - karo na biyu da hakan na faruwa ke nan cikin ƴan kwanaki.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an yi wa kusan motoci tara cikin 10 da ke shiga Gaza a watannin baya-bayan nan sata kafin su kai yankin.

  16. Matar MKO Abiola ta rasu tana da shekara 82

    Dr Doyinsola Hamidat Abiola

    Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya

    Bayanan hoto, Dr Doyinsola Hamidat Abiola

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa rasuwar mai ɗakin cif MKO Abiola, Dr Doyinsola Hamidat Abiola wadda ƴar jarida ce da ta yi fice.

    Sanarwar da aka fitar daga Fadar Shugaban na Najeriya ta ambato irin gudummawar da Doyin Abiola wadda ta rasu tana da shekara 82 ta bayar a fannoni da dama musamman a ɓangaren jarida da kuma samar da daidaito tsakanin jinsi.

    Sanarwar ta kuma yi magana kan rawar da ta taka wajen raya dimokraɗiyya inda ta yi riƙo da gaskiya da kuma ƙoƙarin samar da shugabanci na gari.

    A cewar sanarwar, shugaban ya bayyana kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da marigayiyar wadda ta samo asali daga irin dangantaka ta ƙut da ƙut da ke tsakaninsa da marigayi MKO Abiola.

    Ya ce ta bayar da gudummawa a zaɓen MKO inda bayan da aka soke zaɓen 12 ga watan Yuni da mai gidanta ya lashe, ta tashi tsaye wajen ganin an yi adalci.

    Ya ƙara da cewa ƴan Najeriya ba za su mance da Doyin Abiola ba saboda ƙwarewarta a fannin jarida da kuma yadda take jagorantar tallafawa mata da kuma ƙoƙarin bayar da gudunmuwa a fannin dimokraɗiya.

  17. Sojojin Sudan sun kashe mayaƙan RSF fiye da 100 a Kordofan

    Sojojin Sudn sun kashe fiye da mayaƙan RSF 100 tare da lalata motocinsu sama da 20 cikin kwana uku da sojojin suka shafe suna kai masu farmaki a yankuna da dama a Kordofan.

    Sojin yaƙin Sudan ne ya kai hare-haren a jiya Talata inda bayanai ke cewa hare-haren sun shafi birnin El-Obeid da Al-Khuwayi da Abu Zabad da El Nuhud a yammaci da arewacin Kordofan.

    Hare-haren sun faru ne bayan da RSF ta yi barazanar kai hari a ranar 3 ga Agusta kan El- Obeid, babban birnin jihar North Kordofan, yanki mai yawan sojoji da ke da dubban mutane da aka ɗaiɗaita daga wasu yankunan da ke maƙwabtaka.

  18. Kotu ta samu baƙi 21 da aikata laifukan intanet a Najeriya

    Wata kotu a Abuja ta samu baƙi 21 da aikata laifukan intanet inda kuma ta ci tarar kowannen su naira miliyan guda.

    Waɗanda aka samu da laifin na cikin ƴan ƙasar waje 109 daga ƙasashen China da Indonesiya da Brazil da Philippines da Vietnam da Thailand da aka yi holensu a 2024 kan zargin aikata laifuka shida.

    An kuma umarci masu laifin su 21 da su fice daga Najeriya cikin kwana shida yayin da ake ci gaba da shari'a kan wasu mutum 88 da ake zargi da aikata laifin zamba ta intanet.

  19. Mutum 19 sun mutu a hatsarin mota a Uganda

    An tabbatar da mutuwar mutum 19 a yammacin uganda bayan da wata babbar mota da suke ciki ta yi haɗari a ranar Talata da daddare a birnin Hoima mai arzikin mai, mai nisan kilomita 202 daga Kampala, babban birnin ƙasar.

    Kakakin ƴansanda a yankin Hakiza Julius ya shaida wa BBC cewa galibin waɗanda suka mutu ƴan kasuwa ne daga birnin Hoima kuma suna kan hanyarsu ta dawowa daga Lardin Buliisa, wani gari da ke yammacin Uganda.

    "Haɗari ne da nan take ya yi ajalin mutum 19 inda aka garzaya da wasu 13 zuwa asibitin Hoima inda suke samun kulawar likitoci. Mun kai gawawwakin zuwa ɗakin ajiye gawa." kamar yadda ya shaida wa BBC.

    A cewar ƴansanda da shaidu, babbar motar ba ta iya hawa kan wani ƙaramin tsauni ba inda ta gangara baya tare da murtsuke fasinjoji da kuma kashe wasu da ke cikin motar bayan da ta kife.

    Ƴan kasuwa a Uganda na yawan yin tafiye-tafiye domin sayar da hajarsu sai dai manyan motocin da a mafi yawan lokuta suka cike da fasinjoji har ma wasu a saman motocin na janyo fargaba a wajen jama'a da kuma hukumomi.

  20. Gwamnati ta yi hasashen samun ambaliya a jihohin Najeriya 19

    A shekarar 2024 an yi mummunar ambaliya a Borno

    Gwamnatin Najeriya ta yi hasashen za a shafe kwana biyar ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ka iya janyo afkuwar ambaliyar ruwa a sassan jihohi 19 da kuma wasu wurare 76 a ƙasar.

    Gargaɗin da aka fitar daga ma'aikatar muhalli ta ƙasar, ya buƙaci masu ruwa da tsaki da kuma mazauna yankunan da lamarin ka iya shafa da su ɗauki matakan kariya.

    Hakan na zuwa ne yayin da mummunar ambaliya ta afku a jihohin Ogun da Gombe yayin da wasu jihohin da suka haɗa da Legas da Filato da Anambra da Delta suma matsalar ta shafe su.

    A cewar sanarwar, ana hasashen yankunan za su samu mamakon ruwan sama a yankunan da zai iya haifar da ambaliya daga 5 zuwa 9 ga watan nan na Agusta.

    Jihohin da hasashen ya shafa sun haɗa da Akwa Ibom da Bauchi da Ebonyi da Cross River da Nasarawa da Benue da Kaduna da Katsina.

    Sauran jihohin sun haɗa da Kebbi da Kano da Neja da Filato da Taraba da Jigawa da Yobe da Zamfara da Sokoto da Borno da Gombe.

    Matsalar ambaliya a Najeriya ta zama ruwan dare kowace shekara wadda ke janyo asarar rayuka da salwantar dukiya mai yawa.

    A bara, jihohi 31 rahotanni suka bayyana sun yi fama da bala'in ambaliya da ta shafi mutum miliyan 1.2.