Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 7 ga watan Satumba, 2025.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Lahadi.

    Za mu kawo wasu sababbi gobe da safe.

  2. Mun shirya ƙaƙaba wa Rasha ƙarin takunkumai - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya aiwatar da zango na biyu na takunkumin da ya ƙaƙaba wa Rasha, amma bai fayyace yadda sabon zangon zai kasance ba.

    A ƴan kwanakin nan gwamnatinsa ta nuna alamun za ta ƙara matsa lamba kan Moscow saboda yaƙin da take yi da Ukraine.

    Bayan harin da Rasha ta kai jiya cikin dare a Kyiv, wakilin Mista Trump a Ukraine Keith Kellogg ya ce da alama Moscow ba ta fatan kawo ƙarshen yaƙin cikin diflomasiyya.

    Tun bayan komawar Trump kan mulki, Amurka ta riƙa jan ƙafa wajen ƙaƙaba wa Rasha takunkumi, ba kamar yadda ƙasashen Turai ke ɗaukar mataki a kan Moscow ba.

  3. Mummunan yanayi ya kashe mutum uku a sansanin gudun hijira na jihar Neja

    'Yan gudun hijira

    Asalin hoton, Nema

    Mutum uku sun mutu a sansanin 'yan gudun hijira da ke yankunan Shiroro da Munya a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

    Hussaini Alhassan ɗaya ne daga cikin masu kula da sansanin Gwada, kuma ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa mutanen sun mutu ne saboda ƙarancin kayayyakin kula da lafiya da kuma abinci.

    Bayanan sun fito ne a lokacin da ƙungiyar North South Power Foundation (NSPF) ta kai ziyara domin raba tallafin kayan abinci da suka kai darajar naira miliyan 30 a ranar Asabar.

    Alhassan ya ce akasarin 'yan gudun hijirar sun tsere ne daga garuruwan Kaore da Bassa saboda hare-haren 'yanfashin daji

    Shi ma wani jami'i a sansanin Kuta, Yusuf Kuta, ya tabbatar da mutuwar wata dattijuwa a sansanin, abin da ya sa suka zama uku.

  4. Isra'ila ta ce ta rusa dogon gini na uku a Birnin Gaza

    Birnin Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙara rusa wani babban gini a birnin Gaza bayan umarnin guje wa yankin da ta bai wa mazauna Gaza.

    Wannan ne dogon bene na uku da Isra'ilar ta rusa cikin kwan uku da ta faɗaɗa samame hare-hare.

    Wakilin BBC ya ce akwai dubban mutane da ke zaune a matsugunnan wucin-gadi a birnin Gaza, kuma rundunar sojin Isra'ila ta umarce su da gaggauta ficewa daga birnin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana kai harin nata ne kan maɓoyar mayaƙan Hamas, amma Falasɗinawa sun ce gine-gine ne da ƴan gudun hijira ke zaune.

  5. Ƙungiyar shugabannin Arewa ta nemi Tinubu ya sauya shugabannin sojin Najeriya

    Shugabannin sojin Najeriya

    Asalin hoton, Defense Headquaters

    Wata ƙungiyar shugabanni a arewacin Najeriya ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauya salon yaƙi da matsalar tsaro bayan harin da Boko Haram ta kai a jihar Borno.

    Ƙungiyar Northern Ethnic Nationality Forum ta siffanta lamarin da "bala'i" saboda yadda hare-haren masu iƙirarin jihadi ke hana ayyukan noma da kasuwanci, da kuma garkuwa da mutane da 'yanbindiga ke yi don neman kuɗin fansa.

    A ranar Asabar ne mayaƙan Boko Haram suka kashe sama da mutum 60 bayan harin da suka kai a jihar Borno.

    A yau Lahadi ne ƙungiyar ta nemi a naɗa sababbin shugabannin rundunar soja da kuma yi wa majalisar ministoci ta gwamnatin APC garambawul.

    Kazalika, sun nemi Shugaba Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a yankin domin yaƙi da matsalar tsaron da ta jawo kashe dubban mutane, musamman a yankin arewa maso yamma.

  6. Jirgi maras matuƙi na Houthi ya kai hari Isra'ila

    Mayaƙan Houthi

    Asalin hoton, EPA

    Hukumomi a Isra'ila sun ce wani jirgi maras matuƙi da aka aika daga Yemen ya kai hari kan filin jirgin sama na Ramon Airport a kudancin ƙasar.

    Sun ce harin ya lalata wurin jira na fasinjoji da kuma raunata aƙalla mutum biyu.

    An dakatar da tashi ko saukar jirage yayin da ma'aikatan agaji ke ci gaba da aiki sakamakon harin na yau Lahadi. Amma an ci gaba da ayyuka.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiniyar ankararwa ba ta kaɗa ba kafin harin kuma tana bincike game da hakan. Tun da farko, Isra'ila ta kakkaɓo wasu jiragen uku daga Yemen.

    'Yan ƙungiyar Houthi da ke Yemen sun ci alwashin ci gaba da kai wa Isra'ila hari a matsayin ramuwar gayya bayan kashe firaministan ƙungiyar Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi da ta Isra'ila ta yi a watan da ya gabata.

  7. 'Hamas na sako Isra'ilawa da ke hannun su yaƙin Gaza ya zo ƙarshe'

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan harkokin wajen Isra'ila, Gideon Saar ya ce za a iya kawo ƙarshen yaƙin Gaza a kwana ɗaya da zarar Hamas ta saki Isra'ilawan da take garkuwa da su.

    Saar ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da takwaransa na Denmark, inda ya ƙara da cewa ci gaba da garkuwa da mutanen ne babban ƙalubalen kawo ƙarshen yaƙin na Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga dukkan ɓangarorin.

    Ya ƙara da cewa samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu ba za ta magance matsalar ba, inda a cewarsa, hakan ƙara zai ƙara lalata tsaron Isra'ila ne.

    A nasa ɓangaren, Ambasadan Amurka a Isra'ila, Mike Huckabae ya shaida wa BBC amincewa da samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu tamkar nasara ce ga Hamas domin "a zuciyar su gani suke yi tamkar su ne suke samun nasara a wannan yaƙin."

    Ita dai Hamas ta ce za ta sako waɗanda take garkuwa da su ne idan Isra'ila ta dakatar da hare-harenta, sannan ta janye dakarunta daga Gaza.

  8. Ma'aikatan Najeriya na buƙatar ƙarin mafi ƙarancin albashi daga naira 70,000

    NLC

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya wato NLC ta ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta sake duba yiwuwar ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan ƙasar, domin a cewarta, naira 70,000 ya yi kaɗan a yanzu da tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare.

    A watan Yulin bara ne dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu a sabuwar dokar ƙara mafi ƙarancin albashi, inda ya ƙara ƙaramin albashi na ma'aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, duk da cewa wasu jihohin na biyan sama da haka.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito ƙungiyar na cewa hauhawar farashin kayayyakin buƙata a ƙasar ne ya sa mafi ƙarancin albashin naira 70,000 ba ya isar ma'aikacin ƙasar gudanar da abubuwan da suke buƙata na rayuwar yau da kullum, kamar yadda muƙaddashin babban sakataren NLC, Mr Benson Upah ya shaida wa NAN a ranar Lahadi a Abuja.

    "Maganar gaskiya naira 70,000 ya yi kaɗan a wannan yanayin na taɓarɓarewar arziki a Najeriya. Ma'aikata na fuskantar ƙalubale sosai, kuma idan gwamnati ba ta ɗauki matakin da ya dace ba, lallai ma'aikatan ƙasar za su shiga cikin damuwa sosai.

    "Tuni mun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya game da wannnan matsalar, kuma muna fata za ta yi abin da ya dace duba da irin yadda tattalin arzikin ƙasar yake ciki."

  9. An ceto mata biyu da jaririya daga ambaliyar ruwa a Kaduna

    Ambaliya

    Asalin hoton, Zubaida Umar

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta kai ɗauki kan waɗanda ambaliyar ta shafa a wasu garuruwan jihar Kaduna, inda ta samu nasarar ceto wasu waɗanda ambaliyar ta rutsa da su.

    A wata sanarwa da shugabar hukumar, Zubaida Umar ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce mamakon ruwan sama ne ya jawo ambaliyar, wadda ta shafi unguwannin da dama a cikin ƙwaryar Kaduna.

    "Ambaliyar ta samo asali ne daga mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Juma'a, kuma ta shafi aƙalla gidaje 163, waɗanda a ciki akwai aƙalla iyalai 533."

    Ta ce ƙananan hukumomin da ambaliyar ta shafa su ne Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da kuma ƙaramar hukumar Igabi duk a tsakiyar jihar.

    "Ruwan Kogin Kaduna ne ya yi sama sosai, sai ya yi ambaliya, har ruwansa ya mamala zuwa unguwannin Kabala Doki da layin Bachama da layin Kigo da layin Ramat da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali da wasu unguwannin."

    Ta ce shugaban hukumar na Kaduna, Suleiman Mohammed ne ya jagoranci aikin ceton na gaggawa tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin agajin gaggawa a jihar.

    Ta ce sun samu nasarar ceto mata biyu da wata jaririya daga ambaliyar, sannan ta ce za su ci gaba aiki tare da hukumomin jihar domin agazawa waɗanda lamarin ya shafa.

  10. DSS ta buƙaci X ya rufe shafin Sowore

    Sowore

    Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS ta buƙaci mahukuntar kafar X wato twitter da ta rufe shafin ɗan gwagwarmaya, kuma tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya, Omoyele Sowore.

    A wata takardar koke da hukumar da aike wa X, ta ce tana buƙatar a rufe shafin nasa a cikin awa 24.

    Wani mai suna B. Bamigboye ya rubuta a madaɗin shugaban hukumar, inda ta yi barazanar ɗaukar mataki idan ba a rufe shafin ba.

    Ta ce rubutun da Sowore ya yi game da shugaban ƙasar Bola Tinubu a ranar 25 ga watan Agusta zai iya jawo hargitsi a ƙasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. An gano dalilin haɗarin jirgin ƙasa da ya ci mutum 16 a Portugal

    Portugal

    Asalin hoton, EPA

    Wata sanarwar farko-farko a game da abin da ya haddasa hatsarin karamin jirgin kasan nan a Portugal ya gano cewa igiyar da ke hada taragunan biyu ta jirgin kasan ce ta tsinke.

    Mutum 16 ne suka rasa ransu bayan da jirgin ya yi hadari a Lisbon a ranar Laraba. Ofishin da ke kula da harkokin sufuri a Portuugal ya ce sai da aka tabbatar da lafiyar karamin jirgin kasan da safiyar ranar da abin zai faru kuma komai lafiya lau babu wata matsala, to amma ba a san abin da ya janyo hadarin ba.

    Sanarwar ta ce babu wani tabbaci akan abin da aka gano a game da musabbabin hadarin karamin jirgin kasan.

    Wakiliyar BBC ta ce a yanzu haka ana gudanar da bincike da dama inda kamfanin da ke kula da jirgin da kuma Ofishin da ke kula da harkokin sufuri a Lisbon ke na su binciken don gano abin da ya janyo hadarin karamin jirgin kasan

  12. An sako direbobin mota shida da aka yi garkuwa da su a Senegal

    BINDIGA

    Asalin hoton, Getty Images

    An sako direbobin manyan motocin nan 6 'yan kasar Senegal da ake zargi masu ikirarin jihadi a Mali na tsare da su a cewar kungiyar direbobi ta Mali.

    Rahotanni sun ce kungiyar masu kaifin kishin Islama da ke da alaka da al ka'ida ne suka kama direbobin ne a ranar Alhamis din data gabata bayan da suka rufe wata hanya a yammacin Mali.

    Kungiyar ta sanar da rufe hanyoyi biyu a yankin arewacin Malin da nufin hana shigar da mai cikin Mali daga Senagal.

    Mazauna garuruwan da hanyoyin suka ratsa sun kasance cikin fargaba saboda suna ganin rufe hanyoyin zai janyo musu fuskantar karancin abubuwan bukatun yau da kullum.

  13. Dubban mutane sun yi zanga-zangar adawa da ƙarfafa dokokin shige da fice a Amurka

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a Chicago inda suke nuna kin amincewa da barazanar da shugaba Trump ya yi ta karfafa harkokin shige da fice da kuma kai jami'an tsaro na kasa zuwa birnin.

    A ranar Asabar, shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta wani hotonsa da aka hada da komfuta ya juyawa jirgi mai saukar ungulu baya sannan kuma ga wuta na ci a Chicago sannan kuma ya rubuta cewa ina jin dadin mayar da mutane garuruwansu na asali da sanyin safiya.

    Cikin sakon nasa ya kuma ce nan ba da jimawa ba wannan birni zai gano abin da ya sa ake kiran ma'aikatar yaki da sunanta.

    Tuni gwamnan jihar Illinois JB Pritzker ya zargi Mr Trump da yi wa birnin barazanar yaki yana mai cewa wannan kalamai na sa ba abin wasa bane.

  14. Zulum ya jajanta wa iyalan waɗanda Boko Haram ta kashe a Borno

    Borno State

    Asalin hoton, Borno State

    Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Darajamal da ke ƙaramar hukumar Bama domin jajanta wa ƴan'uwan aƙalla mutum 63 da ƴan Boko Haram suka kashe a daren Juma'a.

    Daga cikin waɗanda aka kashe ɗin har da sojoji biyar da fararen hula 58 daga cikin waɗanda suka koma garin bayan ɗaukar tsawon lokaci suna gudun hijira.

    A zantawarsa da menama labarai, gwamnan ya ce, "mun zo ne domin jajanta muku bisa abin da ya faru a Darajamal, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane da dama. Lamarin nan abin takaici ne. Watanni kaɗan da suka gabata ne mutanen garin nan suka koma gidajen su, har sun ci gaba da gudanar da ayyukan su, amma kwatsam sai aka kai musu wannan hari na Boko Haram," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Gwamnan ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum 63, "ciki har da farareb hula da sojoji."

  15. Harin Rasha ya yi ajalin wata mata da ɗanta a Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Ukraine State Emergency Service

    An samu fashewar abubuwa da dama a Kyiv, babban birnin Ukraine bayan Rasha ta kai hare-haren makamai linzami a ƙasar.

    An hango wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniyar birnin sannan kuma an dauke wuta.

    Magajin Garin birnin Vitaly Kiltschko, ya ce an kashe wata mata da danta a harin.

    Cikin dare Rasha ta yi amfani da jirage marassa matuka inda ta kai hare hare a wasu sassa na Ukraine ciki har da yankunan da ke kusa da iyakar kasar da Poland.

  16. Isra'ilawa sun buƙaci Trump ya matsa wa Netanyahu lamba kan tsagaita wuta a Gaza

    Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Trump ya bayyana damuwa kan yiwuwar kasancewar wasu daga cikin Isra'ilawan da har yanzu Hamas ke tsare da su a Gaza a raye, a yayin da dubban Isra'ilawa suka yi gangami a Tel Aviv a daren jiya Asabar.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi kira ga shugaba Trump din akan ya matsa wa Firaiminista Netanyahu lamba wajen ceto mutanen ta hanyar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Mr Trump ya ce Amurka na tattauna sosai da Hamas domin sako ragowar mutanen baki daya, to amma ya ce an shaida masa cewa ba akwai wadanda suka mutu a cikinsu.

    Isra'ila ta ce mayakan Hamas na rike da mutane kusan 50, to amma mutum 20 ne kadai ake ganin suna raye.

    Wakilin BBC ya ce Isra'ial ta sake nanata cewa dole ne ta kwace ikon Gaza domin ta murkushe Hamas da kuma kubutar da mutanen da suka rage a tsare a hannun Hamas din.

  17. Budewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Lahadi, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya Asabar wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.