Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 06/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mika'il, Aisha Babangida, Khalifa Dokaji da Ahmad Bawage

  1. An miƙa wa Amurka daftarin sasanta DR Congo da Rwanda

    Mai bai wa shugaban Amurka, Donald Trump shawara na musamman kan harkokin Afrika, Massad Boulos, ya tabbatar da karɓar daftarin sasanta ƙasashen DR Congo da Rwanda bayan rsaka hannu kan sharuɗa a tsakaninsu a birnin Washington ranar 25 ga Afrilu.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a jiya, Boulos ya ce: “Na karɓi daftarin sasantawa ɗauke da shawarwarin zaman lafiya daga DRC da Rwanda. Wannan muhimmin mataki ne wajen cika alƙawuran da aka ɗauka a Sanarwar Ka’idoji, kuma ina sa ran ƙasashen biyu za su ci gaba da jajircewa don ganin an samu zaman lafiya.”

    Ministan harkokin wajen Rwanda, Olivier Nduhungirehe, ya bayyana cewa har yanzu ba a haɗa ra’ayoyin ƙasashen biyu gaba ɗaya ba, amma ya nuna fatan cewa yarjejeniyar ƙarshe za a iya sanya hannu akanta a fadar White House nan da watan Yuni.

    Hukumomin DR Congo ba su fitar da wata sanarwa ba kan takardun, sai dai Shugaba Félix Tshisekedi ya musanta zargin cewa ya sayar da dukiyar ma’adinan ƙasar don samun goyon bayan Amurka a yaƙi da mayaƙan M23 da ake zargin Rwanda na goyon baya gare su.

  2. Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma'aikata

    Kungiyar ƙananan likitoci a Najeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, bayan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan birnin na FCT ta yi.

    An yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da kungiyar likitocin ta gudanar a asibitin Asokoro ranar Litinin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito.

    Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma "rashin imani", yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu.

    Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa.

    Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wike bai ɗauki mataki cikin kwanaki uku ba za su shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani tare da rufe duk asibitocin Abuja.

  3. Nijar ta soke yarjejeniyar tattara bayanan sirri tsakaninta da Rasha da Turkiyya

    Gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar tattara bayanan sirri tsakaninta da ƙasashen Rasha da Turkiyya.

    Gwamnatin sojin ta ce ta yi hakan ne saboda rashin gamsuwa da irin ingancin fasahar na'urori da dabarun aikin da waɗannan ƙasashe suka ba ta, kamar yadda shafin intanet na LSI-Africa mai zaman kansa ya ruwaito.

    Rahoton ya kuma ce wata sabuwar yarjejeniya tsakanin Nijar ɗin da wani kamfani na Maroko da ke da ƙwarewa a aikin tattara bayanan sirri ta hanyar latironi ta katse bayan da gano kamfanin na da alaƙa da wani kamfanin Faransa.

    Nijar ta katse hulɗa da ƙasashen Yamma tare da ƙulla ƙawance da ƙasashen Rasha da Turkiyya ne tun bayan juyin mulkin da Janar Abdirahmane Tchiani ya jagoranta a watan Yulin 2024.

  4. Ɗalibai miliyan 1.5 ne cikin 1.95 suka samu maki ƙasa da 200 a jarabawar Jamb

    Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun kasa kai maki 200 daga cikin maki 400.

    A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, JAMB ta ce dalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, ɗalibai miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.

    Binciken sakamakon ya nuna cewa ƙalilan ne suka samu maki mafi girma wato ɗalibai a Jimillance, ɗalibai 12,414 ne kacal suka samu maki 300 sama.

    A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.

    Rukunin da ya fi yawan dalibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu dalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 kenan. Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.

    Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 suka kasa kai maki 100 gaba ɗaya.

  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Talata.

    Shafin zai kawo rahotonni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana.

    Aisha Babangida ce za ta kawo muku rahotonni har zuwa ƙarfe 3:00 na rana bisa kulawar Umar Mika'il.