Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/10/2025.
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni na cewa an ji wata fashewa mai karfi da kuma musayar wuta a kusa da wani gidan yari mai tsaron gaske da ke Mogadishu babban birnin Somalia.
Ana iya ganin hayaƙi na tashi ta kan gidan yarin na Godka Jilicow, wanda ke kusa da fadar shugaban kasar da ke gabashin Afirka.
Wakilin BBC ya ce da wuya a iya sanin ko akwai waɗanda lamarin ya rutsa da su domin an rufe dukkanin titunan zuwa wajen.
Gidan yarinn da hukumar tattara bayanan sirri ta kasar ta Somaliya ke gudanarwa, yana dauke da ruƙaƙƙun masu aikata miyagun laifi da wadanda ake zargi da zama 'yanbindiga.
Kungiyar Al-Shabab mai ikirarin jihadi ta ce ita ta kai harin, wadda ke ci gaba da kama wurare bayan a baya dakarun gwamnati suka rage karsashin mayakanta.

Asalin hoton, Reuters
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce matsi Hamas ta ji a difilomasiyyance da kuma ƙarfin soja kafin ta amince da sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su a Gaza.
Netanyahu ya kuma ce ƙungiyar za ta zubar da makamanta a matsayin tanadin yarjejeniyar zaman lafiya.
"A mataki na biyu, za a karɓe makaman Hamas sannan a fitar da dukkan makamai daga Gaza - ko dai ta laluma ko kuma da ƙarfin tsiya, amma lallai za a cimma hakan," in ji shi cikin wani jawabi da ya yi babu daɗewa.

Asalin hoton, Reuters
Kafofin yada labarai na Masar sun ce Isra'ila da Hamas na shirin gudanar da tattaunawa da ba ta gaba da gaba ba ranar Lahadi da kuma jibi Litinin a Alƙahira babban birnin ƙasar.
Shirin na zuwa ne bayan Hamas din ta amince da wasu sassan daftarin zaman lafiya da Shugaba Trump na Amurka ya gabatar.
Kafar Al-Qahera News wadda ke da kusanci da hukumar leken asiri ta Masar, ta ce tawagogin biyu za su tattauna kan sharuɗɗan musayar dukkanin 'yan Isra'ila da suka rage a hannun Hamas da kuma fursunoni.
Jami'an fadar gwamnatin Amurka ma sun ce sirikin Trump, Jared Kushner, da jakadan shugaban na musamman Steve Witkoff za su je Masar ɗin domin tattaunawar, amma ba su bayar da cikakken bayani ba.
Tun da farko, Hamas ta ce za ta saki dukkanin ragowar 'yan Isra'ila da take garkuwa da su, amma ta bukaci ƙarin tattaunawa kan wasu batutuwan.
A halin da ake ciki kuma, Isra'ilar ta ci gaba da ruwan bamabamai a Gaza duk da kiran da Shugaba Trump ya yi mata na ta daina.

Asalin hoton, @GEJonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce an sauya wa kalaman da ya yi kan marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ma'ana game da Boko Haram, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.
Yayin bikin ƙaddamar da littafin da tsohon babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor ya rubuta, Jonathan ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa sanar da tsohon shugaban a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da take so ya shiga tsakani a tattaunawarta da gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Jonathan.
Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, ya musanta iƙirarin yana mai cewa wani ɓangare ne na ƙungiyar ya sanar da batun "wanda Buhari kansa bai san da shi ba".
Wata sanarwa da mai magana da yawun Jonathan ya fitar ta ce ya faɗi hakan ne kawai domin ya nuna irin dabarun da ƙungiyar ta dinga amfani da su a lokacin.
"Jonathan bai yi kalaman ba domin ya nuna cewa Buhari yana da wata alaƙa da Boko Haram, ko kuma yana goyon bayan su," in ji sanarwar da Ikechukwu Eze ya fitar a yammacin yau Asabar.

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 66 cikin awa 24 da suka gabata, wanda hakan ya sa jimillar adadin Falasɗinawa da ta kashe suka kai 67,074.
Ma'aikatar ta kuma ce akwai wasu 265 da aka kai asibiti da raunuka a fadin Gaza a wannan lokacin.
Adadi mai yawa na Falasɗinawa na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai saboda rashin kayan aikin ceto su, a cewar sanarwar da ma'aikatar lafiyar ta fitar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce har yanzu tana kaiwa da kawowa a Birnin Gaza tare da gargaɗin Falasɗinawa cewa ya yi wuri su fara komawa birnin a yanzu.
Tun da farko Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare a yankin bayan ƙungiyar Hamas ta bayyana amincewa ɓangarorin daftarin zaman lafiya da ya gabatar a yammacin Juma'a.
Amma ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra'ilar sun ci gaba da sauka cikin dare.
Hamas ta amince ta saki dukkan Isra'ilawan da take tsare da su amma kuma ta buƙaci a tattauna kan wasu ƙudirorin - ciki har da batun zubar da makamanta.
Rahotonni daga Isra'ila na cewa hukumomi sun fara shirin karɓar mutanen da za a sako.

Asalin hoton, Reuters
Za a koma teburin tattaunawa domin ci gaba da lalubo hanyoyi kawo ƙarshen yaƙin Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas.
Za a ci gaba da tattaunawa ne a ƙasar Masar nan da wasu kwanaki masu zuwa, lamarin da ke zuwa kwanaki kaɗan bayan Hamas ta amince da sharaɗin Trump na sakin dukkan waɗanda ta yi garkuwa da su a Isra'ila.
Sai dai Ira'ila na ci gaba da kai hare-hare a wasu sassa na Gaza, duk da ta ce ta rage luguden na wuta da take yi saboda buƙatar da Trump ya bayyana ta a dakata.
Ma'aikatar Hamas ta ce an kashe aƙalla mutum 60 a cikin kwana ɗaya a zirin a daidai lokacin da ake maganar tsagaita wuta.
A nata ɓangaren, Isra'ila ta ce duk da cewa tana shirye-shiryen fara tattaunawa, "akwai buƙatar kawar da duk wata barazana."

Asalin hoton, Dangote Industries/Facebook
Rukunin kamfanoni na Dangote ya ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin takin zamani na Dangote Gode Fertilizer a ƙasar Habasha.
Shugaban rukunin kamfanonin, Alhaji Aliko Dangote ne ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gina kamfanin mai suna Dangote Gode Fertiliser Plant wanda za a garin Gode da ke ƙasar Habasha.
Daga cikin waɗanda suka samu halartar ƙaddamar da fara aikin, akwai Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban kamfanin man fetur na MRS, Sayyu Dantata da shugaban rukunin kamfanonin NGX, Umaru Kwairanga da shugaban kamfanin hannun zuba jari na Habasha, Biru Taye.

Asalin hoton, Garba Shehu
Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari ya musanta maganar da tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ya yi cewa Boko Haram ta taɓa zaɓar marigayin a matsayin wakili domin tattauna sasanci da gwamnatin tarayya.
Garba Shehu ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya yi kira ga Jonathan da ya guji amfani da sunan maigidansa domin neman mulki a zaɓen 2027.
"Da Muhammad Yusuf ko Abubakar Shekau, babu wani tsohon shugaban Boko Haram da ya taɓa zaɓar Muhammadu Buhari a matsayin wakili domin shiga tsakaninsu a tattauna sasanci da gwamnatin tarayya. Maimakon haka ma, Shekau ya sha yi wa Buhari barazana, har ta kai marigayi Buhari ya tsallake rijiya da baya a wani harin Boko Haram a shekarar 2014 a Kaduna."
Garba Shehu ya ce ko a yaƙin zaɓe, marigayin ya mayar da hankali kan yaƙi da Boko Haram da tabbatar da tsaro a Najeriya.
"Buhari ba shi da masaniya a kan batun da aka riƙa yaɗawa cewa wai shi ne zai wakilci ƙungiyar domin tattaunawa. Haka kuma a wata sanarwa da babban sakataren Jam'iyyar CPC na lokacin, Buba Galadima ya fitar, ya ce Buhari ba shi da masaniya kan batun."
Garba Shehu ya ce abin da ya faru a lokacin shi ne wani tsagin Boko Haram "waɗanda wataƙila maƙiya Boko Buhari suka ɗauki nauyi ne a ƙarƙashin wani mai suna Abu Mohammed Ibn Abdulaziz suka gudanar da taro suka ce wai suna so Buhari da mariygayi Bukar Abba Ibrahim da tsohon ministan fetur na farko a Najeriya Shettima Ali Monguno da wasu dattawan yankin ne suke so su wakilce su a wajen tattauna sasanci da gwamnatin tarayya."
Garbe Shehu ya ce ko a lokacin shugaban Boko Haram na lokacin Abubakar Shekau ya fito ya ƙaryata maganar, inda ya ce Abdulaziz ba shi da izinin magana a madadin ƙungiyar.

Asalin hoton, Reuters
Wani alkali a birnin New York na kasar Amurka ya yanke wa fitaccen mawakin gambarar nan na kasar Sean 'Diddy' Combs, hukuncin daurin shekaru hudu da wata biyu a gidan kaso.
Alkalin ya ce ya ci zarafin wasu tsoffin yan matansa biyu wadanda suka bada shaidar ya ci zarafinsu, sannan kotun ta kuma ci tarar mawakin dala dubu dari biyar.
Tunda farko Diddy ya ce ya dauki alhakin abun da ya faru, harma ya kira dabi'un na sa a matsayin masu kyama.
Ya kuma nemi afuwar wadanda ya ci zarafinsu da kuma iyalansa. Duk da haka lauyoyinsa sun ce yana shirin daukaka kara kan hukuncin shekara hudun.

Asalin hoton, EPA
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin mai shiga tsakani domin tattaunawa da gwamnatin tarayya a zamanin mulkinsa.
Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Juma'a a wajen ƙaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum“, wanda tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ya rubuta a Abuja.
Ya ce, a lokacin an fara yunƙurin tattaunawa ne da Boko Haram domin ganin ko za a samu sulhu, su daina yaƙin da suke yi.
"An kafa kwamiti ne a lokacin, sai Boko Haram ta zaɓi Buhari a matsayin wakilinsu domin tattaunawa da gwamnatin," in ji Jonathan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Jonathan ya ce, "tunda dai har suka zaɓe shi a matsayin wakili, to sai na yi tunanin da zarar ya hau mulki, zai kawo ƙarshen matsalar, amma abin mamaki har yanzu ana fama da matsalar ta Boko Haram."

Asalin hoton, Reuters
Filin tashi da saukar jiragen sama na Munich da ke kudancin Jamus ya dakatar da aiki a dare na biyu a jere, bayan da aka samu kutsen wasu sabbin jirage marasa matuka na Rasha.
An soke tashin jirage masu shigowa da masu fita a yammacin jiya Juma'a, lamarin da ya shafi fasinjoji sama da dubu shida.
Wakiliyar BBC ta ce cikin wata sanarwa, hukumar kula da filin jirgin ta ce an dakatar da tashi da saukar jiragen saman ne har nan da abun da hali ya yi, da zummar gudun abun da ka je ya zo.
A baya-bayan nan dai an dauki irin wannan mataki a Denmark da Norway da kuma Poland saboda kutsen jirage marasa matukan. Moscow ta musanta hannu.

Asalin hoton, Office of the Press Secretary, Government House Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto ya kai ziyarar jaje wajen al'ummar ƙananan hukumomin Sabon Birni da Isa da ke gabashin Sokoto domin jajanta musu kan hare-haren ƴanbindiga.
A ziyarar, gwamnan ya ba ƴangudun hijirar yankin naira miliyan 293 da buhun shinkafa 1,540 da sauran kayayyakin buƙata domin rage musu raɗaɗin da ma rage musu zafin zama a sansanin gudun hijira.
A ziyarar, Gwamna Ahmed Aliyu ya jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa, inda ya ce suna ƙoƙarin gaske domin magance matsalar.
A ƙaramar hukumar Isa, gwamnan ya ba iyalan mutum 65 da aka kashe naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, da kuma naira 250,000 da buhun shinkafa uku ga duk wanda ya ji rauni a harin.
Haka kuma gwamnan ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 20 da buhun shinkafa 1,200 ga sansanin gudun hijira a yankin.
A ƙaramar hukumar Sabon Birni, Gwamna Aliyu ya ba iyalan waɗanda suka rasu guda 61 naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, da kuma gudunmuwar naira miliyan 20 da buhun shinkafa 1,200 ga sansanin gudun hijira a yankin.
Gwamnan ya ce za su yi doka na musamman domin hukunci mai tsanani kan mau kwarmata bayanai ga ƴanbindiga, "masu kwarmata bayani ba su da gindin zama a jiharmu," in ji shi, kamar yadda mai magana a yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana.
A game da tsaro, gwamnan ya ce sun ba jami'an tsaro motocin sintiri guda 180, sannan suna bayar da alawus ga dakarun da ke kan gaba wajen daƙile matsalar tsaro.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na nuna cewa hukumomi a Iran sun ce an kashe wasu mutane shida da aka samu da laifin ta'addanci da alaka da Isra'ila.
Ma’aikatar shari’a ta kasar ta ce mutanen mambobi ne na wata kungiyar ‘yan ta’adda ta ‘yan aware da suka yi ikirarin kashe jami’an tsaro hudu tare da kai harin bam a lardin Khuzestan da ke yammacin kasar.
Mahukunta sun ce an dauki matakin ne bayan cika dukkan ka'idojin shari'a.
Iran da Isra'ila sun gwabza yaki na tsawon kwanaki goma sha biyu a watan Yuni.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana rage kai hare-haren d take kai wa Gaza bayan umarnin shugaba Trump na daina kai hari nan take.
A cikin wata sanarwa da ofishin firaministan kasar ya fitar, ya ce tuni aka fara shirin karbar mutanen da Hamas ke rike da su.
Shugaba Trump ya umarci Isra'ila ta dakatar da hare haren na ta ne, bayan martanin Hamas ga yarjejeniyar da ya gabatar mata, don kubutar da mutanen da take rike da su, da kuma kawo karshin yakin baki daya.
A wani bidiyo da ya saki, Mista Trump ya ce za a yi wa dukkan bangarorin adalci. Hamas ta yi maraba da umarnin da shugaban ya ba wa Isra'ila na tsayar da hare harenta.
Wakilin BBC ya ce ta kuma nuna alamun amince da bukatar mika yankin ga wani kwamitin kwararru na musamman na Falasdinawa domin ci gaba da gudanar da yankin.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar.
Yau ma za mu ci gaba da kawo muku muhimman labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Ku kaance tare da mu.