Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi da Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. 'Harin Iran ya katse wutar lantarki ga dubban Isra'ilawa'

    Kimanin mutum 8,000 ne suka fama da rashin wutar lantarki a sanadiyar hare-haren Iran a cikin Isra'ila, kamar yadda ministan makamashin ƙasar ya bayyana.

    Eli Cohen ya ce hukumomi "sun yi shirin fuskantar wannan matsalar tun farko," sannan ya ƙara da cewa za su tabbatar lantarki ta samu cikin awa uku.

    Tun da farko, hukumar wutar lantarki ta Isra'ila IEC ta sanar da cewa harin ya ɓarnata mata wasu kadarori masu muhimmanci a kudancin ƙasar, wanda hakan ya yi sanadiyar ɗaukewar lantarki a wasu yankunan ƙasar.

    “IEC ta tura wakilanta zuwa wasu yankunan domin gyara lantarkin nan ba da jimawa ba."

  2. Waɗanda suka tsira daga kisan Filato sun bayyana yadda sojoji suka cece su

    Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga kisan da aka yi wa wasu da za su je biki a Filato sun bayyana wa jaridar Daily Trust yadda aka kai musu hari a lokacin da suke tafiya zuwa bikin aure.

    Ibrahim Umar, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, ya ce suna kan hanyarsu ne daga Zariya zuwa Qua’an Pan domin bikin ɗan uwansa. A cikin motar akwai mahaifin ango, kawunsa da kuma ƙaninsa. Duk da cewa sun bayyana wa maharan cewa ba 'yan yankin ba ne, kuma suna ɗauke da goro da kyaututtukan biki, sai ya ce, “ba su saurare mu ba – suka kashe ƴanuwanmu.”

    Ya bayyana cewa mahaifi da ƙanin ango da kuma kawunsa duk an kashe su a harin.

    Angon, wanda asalinsa daga Zariya ne kuma malami ne a wata makaranta a yankin, ya hadu da matar da zai aura a lokacin da yake koyarwa, sannan suka amince su yi aure. Ibrahim ya ce sun bayyana wa maharan cewa ba mazauna yankin ba ne, daga Jihar Kaduna suka taho domin halartar biki, amma ba su yarda ba “Dukkanmu dangin juna ne, daga ƙauye ɗaya muka fito,” in ji shi.

    Ibrahim ya ce da ba don sojojin da ke kusa da inda lamarin ya faru sun hanzarta zuwa ba, da abin zai fi muni. “Sojojin sun iso da wuri kuma suka cece mu. In ba don hakan ba, da labarin zai canza,” in ji shi.

    Wani, wanda shi ma ya tsira daga harin, Sa’adu Abdullahi, ya bayyana cewa sun yi ɓatan hanya ne suka shiga wani ƙauye ba da gangan ba. Bayan sun tsaya domin tambayar hanya, sai kwatsam aka fara kai musu hari.

    Duk da cewa sun shaida wa mutanen cewa suna kan hanyar zuwa biki ne, hakan bai sa aka kyale su ba.

  3. Jami'an Iran na tattaunawa da Shugaba Putin na Rasha

    Ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara Rasha tare da rakiyar wasu jami'an gwamnatin ƙasarsa, inda ya je domin ganawa ta musamman da Shugaban Ƙasar Vladimir Putin.

    Abbas Araghchi ya yaba wa shugaban na Rasha, wanda ya ce tarihi ba zai manta da shi ba bisa jajircewar da ya nuna wajen fitowa fili ya yi Allah-wadai da harin Amurka a cibiyar nukiliyar Iran.

    Ministan ya zargi Amurka da yi wa dokokin duniya da yarjejeniyar makamin nukiliya ta Non-Proliferation Treaty (NPT) karan tsaye ta hanyar ɗaukar matakin kai harin.

    Yayin wani taro da ministan harkokin wajen Iran a birnin Moscow, Mr Putin ya ce babu wata hujja da za a bayar, domin goyon bayan hare-haren.

    Ya kuma bayar da tabbacin cewa Rasha na ƙoƙari domin taimakawa jama'ar Iran.

    Wakilin BBC ya ce ''Amma yarjejeniyar da ke tsakanin Rasha da Iran ba ta haɗa da tallafin aikin soji ba, don haka da wuya Kremlin ta iya bai wa Tehran duk wani tallafi mai alaƙa da aikin soji.''

  4. 'Matsaloli sun yi wa Yammacin Afirka ɗaurin goro'

    Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da suka yi wani taro a Najeriya sun ce yankin na fuskantar barazanar ta'addanci da sauyin yanayi da juyin mulkin soja da kuma talauci.

    Taron Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ta ECOWAS wanda aka kammala jiya Lahadi ya yi gargadi kan matsalolin masu hatsari.

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce rashin tabbacin siyasa da safarar makamai ba bisa ƙa'ida ba, da kuma laifukan da suka shafi kasashe da dama na nufin lokaci ya yi da za a sake gyara tsarin tsaro na haɗin gwiwa a yankin.

    Kungiyar dai ta fuskanci babban ƙalubale a farkon wannan shekara bayan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soja a halin yanzu suka fice daga cikinta, inda suka kafa nasu ƙawancen ƙasashen.

  5. Mutum tara sun mutu a Kyiv a wani sabon harin sama da Rasha ta kai

    Aƙalla mutum Tara ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin da Rasha ta kai da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa a daren jiya a yankin Kyiv, in ji ministan harkokin cikin gida na Ukraine, Ihor Klymenko

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta, Ihor Klymenko ya bayyana cewa an kai harin ne kan unguwannin zama da asibitoci da kuma wuraren motsa jiki.

    Shugaban birnin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya ce aƙalla mutum shida daga cikin waɗɗanda suka mutu suna cikin wani gini mai hawa da yawa a birnin, inda ya ƙara da cewa mutum 19 sun jikkata a cikin birnin.

    A ‘yan makonnin nan, Rasha na ƙara kaimi wajen kai hare-haren sama a kan biranen Ukraine.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce a shafin X cewa zai je birnin London domin tattauna rikicin a ranar Litinin.

    Rundunar sojin saman Ukraine ta ce a sabon harin da aka kai, Rasha ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙi guda 352 da makamai masu linzami 16, wanda suka nufi yankin Kyiv.

    An ruwaito tashin gobara a wurare da dama a faɗin babban birnin.

  6. Za a iya sauya gwamnati a Iran idan ba ta yi abin da ya dace ba - Trump

    Donald Trump ya yi wasu kalamai da ke nuni da yiwuwar samun sauyin shugabanci a Iran.

    Shugaban na Amurka ya ce duk da cewa ba daidai ba ne a siyasance a yi amfani da kalmar sauya gwamnati, amma idan har gwamnatin Iran mai ci ba ta iya - abin da ya kira sake mai do da martabar Iran - to me zai hana a samu sauyi.

    Kalaman mista Trump sun ci karo da na jami'an gwamnatinsa waɗanda tun bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ,su ke ta nanata cewa Amurka ba ta da muradin tsige shugabannin Iran.

    Akwai dakarun Amurka guda dubu arba'in a sansanoni daban daban da ke yankin gabas ta tsakiya wanda halin yanzu ke cikin shirin ko ta kwana yayin da Amurka ke tsammanin martani daga Iran.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gargaɗi Amurkawa da ke fadin duniya da su yi taka tsan-tsan a duk inda suke

  7. Iran ta yi barazanar mayar wa Amurka da martani mai tsanani

    Wasu manyan hafsoshin sojan Iran sun yi barazanar mayar wa Amurka da martani mai tsanani kan hare-haren da ta kai.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun saki wani bidiyo da ke nuna babban kwamandan sojojin ƙasar, Amir Hatami, yana magana da wasu manyan hafsoshi a cikin wani dakin tsare-tsare.

    A cikin bidiyon, Hatami ya ce duk lokacin da Amurka ta aikata “laifuka” kan Iran a baya, sai ta samu martani mai tsanani, kuma wannan karon ma hakan zai faru.

    A wani ɓangare kuma, babban hafsan hafsoshin sojan Iran, Abdolrahim Mousavi, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce Amurka ta buɗe ƙofar daukar “kowanne irin mataki” kan dakarun ta. Ya ƙara da cewa Iran “ba za ta taɓa ja da baya ba.”

  8. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Litinin.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.