Da alama kiran Firaiministan Isra’ila Benjamin
Netanyahu ya yi wa ƴan Lebanon na su haɗa kai su yi wa ƴan Hezbollah bore bai samu
karɓuwa ba a wajen mutanen ƙasar.
Netanyahu ya yi wannan kiran ne, inda ya ce ko dai
su musu bore, ko kuma ya ƙara zafafa luguden wuta a ƙasar.
A cewarsa, “Kirista da
Musulmi Sunni da Shia da Druze, dukkanku kuna shan wahala a sanadiyar yaƙin Hezbollah
da Isra’ila. Ku tashi tsaye ku tseratar da ƙasarku.”
Amma a yankunan Shia da Sunni da
Kirista a Beirut a ranar Laraba, da alama sun yi kunnen uwar shegu da wannan
maganar.
“Mun ji maganarsa, amma ai babu
wanda zai yi amfani da maganar Netanyahu,” in ji Yusuf Habbal mai shekara 31 a
daidai lokacin da yake ci gaba da sana’arsa a shagonsa da ke Tariq El jdideh da
ƴan Sunni suka fi yawa.
“Babu wanda ya ce Netanyahu ya
mamaye Falasɗinu, babu wanda ya ce ya mamaye Lebanon, Isra’ila ce take assasa
yaƙin.”
Sai dai duk da haka Habbal da sauran ƴan Sunni “ba su amince da abubuwan
da Hezbollah take yi ba,” in ji shi.
Shi ma wani mai suna Mohammed
Khair mai shekara 43 da BBC ta riska ana masa aski a Tariq El jdideh ya ce, “babu
wanda zai juya wa Hezbollah baya a nan saboda maganar Netanyahu.”
A yankin Achirafieh, inda mafi yawan Kirista ne a Beirut, wani mai suna
Antoine mai shekara 75 da BBC ta riska yana shan sigari cewa ya yi, “Netanyahu
firaiministan Isra’ila ne, ba na Lebanon ba. Ya ji da mutanensa ba mu ba.”
Ita ma Maya Habib mai shekara 35 ta ce, “Kowa ya san Isra’ila da ƙarya.”
Fadi Ali Kiryani mai shekara
52 ya ce, “ko da Lebanon za ta fi Gaza rugujewa, za mu ci gaba da goyon bayan
Hezbollah.”