Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Everton na fatan siyan Jack Grealish na Manchester City a kan kasa da fam miliyan 50, Manchester United, Liverpool da Chelsea na zawarcin Adam Wharton na Crystal Palace, yayin da Fulham ke tunanin makomar Harry Wilson.

    Everton na fatan za ta iya siyan dan wasan Ingila Jack Grealish daga Manchester City kan kudi kasa da fan miliyan 50 bayan ɗanwasan ya kammala buga mata a matsayin aro. (Telegraph)

    Manchester United na daya daga cikin kungiyoyin da ke duba yiwuwar siyan dan wasan tsakiyar Crystal Palace Adam Wharton a watan Janairu, inda Liverpool da Chelsea ke zawarcin dan wasan na Ingila mai shekara 21. (Caughtoffside)

    Chelsea ta yi kokarin sayen dan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 25, kafin ya koma Tottenham a bazara, amma ta kasa shawo kan West Ham ta amince ta ba ta wani dan wasanta sannan ta kara mata da kudi. (Fabrizio Romano)

  2. Jadawalin wasannin mako na huɗu a Premier ta Najeriya, Najeriyan Premier League

    • Abia Warriors da Katsina United
    • Bayelsa United da Enyimba
    • Kano Pillars da Enugu Rangers International
    • Kun Khalifat da El Kanemi Warriors
    • Nasarawa United da Wikki Tourists
    • Plateau United da Remo Stars
    • Rivers United da Shooting Stars
    • Warri Wolves da Kwara United
    • Ikorodu City da Barau FC
  3. Zan mayar da Forest kan ganiya - Postecoglou

    Ange Postecoglou ya ce ba zai wani ɓata lokaci ba wajen mayar da Nottingham Forest kan ganiya, ya bayyana hakan ne bayan wasan da Arsenal ta doke su 3-0 a wasan mako na huɗu a Premier League ranar Asabar.

    Martin Zubimendi ne ya zura biyu a raga da kuma Viktor Gyokeres - hakan ya sa Gunners ta samu maki uku, bayan da a mako na uku ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Liverpool.

    Postecoglou ya koma horar da Premier League bayan kwana 99 da Tottenham ta kore shi, wanda ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a Forest.

    Forest ta kori Nuna, wanda ya kai ƙungiyar mataki na bakwai a kakar da wuce, sakamakon rashin jituwa tsakaninsa da shugaba, Evangelos Marinakis.

  4. Da ƙyar idan Yamal zai buga wa Barcelona wasa da Newcastle

    Watakila Lamine Yamal bai zai buga wa Barcelona Champions League ba da za ta kara da Newcastle United, kuma Hansi Flick ya caccaki Sifaniya kan matakan da ta dauka kan matashin mai shekara 18.

    Yamal ya buga wa Sifaniya wasan da ta doke Bulgaria 3-0 da caskara Turkiya 6-0 a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Yamal bai halarci atisayen Barcelona ba ranar Asabar, saboda jinya, kenan ba zai yi wasan da za ta fuskanci Valencia ba ranar Lahadi a Laliga, daga nan Barcelona za ta kece da Newcastle United a wasan farko a cikin rukuni a Champions League a makon gobe.

  5. Wasu sakamakon Premier League mako na huɗu ranar Asabar

  6. Real Madrid ta cinye dukkkan wasa huɗu da fara La Liga ta bana

    Real Madrid ta je ta yi nasara a kan Real Sociedad da cin 2-1 a wasan mako na huɗu a Laliga da suka kara ranar Asabar.

    Kylian Mbappe ne ya fara ci wa Real Madrid ƙwallo, sannan Arda Guller ya kara na biyu.

    Daga baya Mikel Oyarzabal ya zare ɗaya a bugun fenariti, sai dai Real ta karasa wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dean Huijsen jan kati tun a minti na 32 da taka leda.

    Kenan Real Madrid ta lashe dukkan wasa huɗu da fata La Liga ta kakar nan.

    A makon gobe ne Real Madrid za ta karɓi bakuncin Marseille a wasan farko a rukuni a Champions League, bayan nan ta fafata da Espanyol a Santiago Bernabeu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

  7. Borussia Dortmund na iya kokarin siyan dan wasan bayan Argentina Aaron Anselmino, mai shekara 20, na dindindin idan ya taka rawar gani a Chelsea, inda ya je aro. (Bild German)

    Dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Sam Mather, mai shekara 21, yana tattaunawa domin ya koma kungiyar Kayserispor ta Turkiyya. (Manchester Evening News)

    Chelsea, da Everton da Brighton duk sun yi bincike a bazara kan dan wasan Barcelona kuma na tsakiyar Spain Marc Bernal mai shekaru 18. (Mundo Deportivo)

    Chelsea na sha'awar sayen dan wasan Juventus da Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, amma za ta biya £86m (€100m). (Fichajes Spanish)

    Fulham za ta nemi kudi don siyan dan wasan tsakiya Harry Wilson a watan Janairu don gujewa rasa dan wasan Wales mai shekara 28 kyauta a bazara. (Football Insider)

    Babban jami'in kwallon kafa na Nottingham Forest Ross Wilson zai bar aikinsa a City Ground don zama darektan wasanni na uku a Newcastle cikin shekaru uku. (paper I)

  8. Arsenal ta haɗa maki uku a kan Nottingham Forest, Arsenal 3-0 Nottingaham Forest

    Arsenal ta doke Nottingham Forest 3-0 a wasan mako na huɗu a Premier League ranar Asabar a Emirates.

    Martin Zubimendi ne ya fara cin ƙwallo tun kan hutu, kuma na farko a Arsenal, inda sabon koci, Ange Postecoglou ya yi rashin nasara a wasan farko da jan ragamar Forest, wanda ya maye gurbin Nuna Espirito Santo.

    Tsohon kociyan Tottenham, bai taɓa yin nasara ba a kan Mikel Arteta a wasa huɗun da suka fuskanci juna, inda ya sha kashi karo uku da canjaras ɗaya.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, sabon ɗan wasan Gunners, Viktor Gyokeres ya kara na biyu, sannan Zubimenti ya ci na uku kuma na biyu a fafatawar.

    A makon gobe Gunners za ta ziyarci Athletic Bilbao a Champions League wasan farko a cikin rukuni, sannan ta karbi bakuncin Manchester City a Premier League.

  9. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.