Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Ɗanƙwallon Najeriya Abubakar Lawal ya rasu bayan faɗowa daga bene

    Rundunar 'yansanda ta ƙasar Uganda ta ce tana bincike game da mutuwar wani ɗanƙwallon ɗan Najeriya mai suna Abubakar Lawal, wanda ya faɗo daga saman ginin wani kantin sayar da kayayyaki.

    Lamarin ya faru ne a Kampala babban birnin ƙasar.

    Ɗanwasan mai shekara 29 ɗan asalin jihar Sokoto ne a arewacin Najeriya, wanda ɗanwasan gaba ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Vipers a Uganda.

    Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ta ce ya faɗo ne daga hawa na uku na ginin kantin Voicemall Shopping Arcade ranar Litinin.

    Ya kai wa wata ƙawarsa mai suna Omary Naima 'yar ƙasar Tanzania ziyara a rukunin ginin lokacin da abin ya faru.

  2. Amurka da Rasha sun haɗe wa Turawa kai game da yaƙin Ukraine

    Sauyin da aka gani daga gwamnatin Donald Trump ta Amurka game da yaƙin Ukraine ya fito ƙarara a ranar Litinin yayin da Amurkar da Rasha suka ɗauki matsaya ɗaya a taron Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

    Da farko ƙsashen biyu sun ƙi amincewa da wani daftarin ƙasashen Turai da ke yin tir da ayyukan Rasha kuma ya goyi bayan Ukraine, wanda babban zauren MDD ya amince da shi.

    Sai kuma suka amince da wanda Amurka ta gabatar a Kwamatin Tsaro, wanda ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin amma bai soki Rasha ba. Sai dai Birtaniya da Faransa sun ƙaurace wa kaɗa ƙuri'a a wannan ƙudirin.

    A makon nan shugabannin Faransa da Birtaniya za su gana da Shugaba Donald Trump - wanda tuni ya gana da Macron - yayin da batun tattaunawar zaman lafiya za ta mamaye ganawar.

  3. Za a iya kawo ƙarshen yaƙin Ukraine cikin makonni - Macron

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a iya cim ma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine cikin 'yan makonni masu zuwa.

    Ya fadi haka ne a kafar talbijin ta Fox News bayan ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House.

    "Mun yi aiki tukuri tare da Birtaniya, muna son gabatar da shirin Birtaniya da Faransa na aike dakaru ba wai domin su shiga sahun gaba a yakin ba, sai don tabbatar da zaman lafiya a iyakokin kasashen biyu," in ji Mista Macron.

    Ya nanata cewa shugabannin Turai a shirye suke su shiga batun tabbatar da tsaron Ukraine.

  4. Maraba

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Talata.

    Za mu kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Umar Mikail ne zai kawo rahotonnin bisa sa'idon Usman Minjibir.

    Ku biyo mu.