Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Tsananin sanyi ya kashe jarirai shida cikin mako biyu a Gaza - Jami'an lafiya

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce an kashe akalla jarirai sabbin haihuwa shida a cikin mako biyu da suka wuce saboda tsananin sanyin da ake fama da shi.

    Jami'an lafiya a Gaza sun shaida wa BBC cewar rashin abin dumama jiki ne ya haddasa mutuwar jariran yayin da Falasdinawa ke neman wajen fakewa daga azabar sanyin da ake fama da shi a yankin da suke zaune a cikin tantuna da gidajensu da aka lalata.

    Haka kuma jami'an lafiyar sun yi kira ga masu shiga tsakanin na kasa da kasa da su kara kaimi wajen ganin an tabbatar da samar da gidajen tafi da gidanka ga al'ummar ta Gaza.

    Har yanzu dai ana nuna rashin tabbas kan ko yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas za ta ci gaba da aiki.

  2. Birtaniya za ta ƙara yawan kuɗin da take kashewa a ɓangaren tsaro

    .

    Asalin hoton, PA Media

    Birtaniya za ta gaggauta kara yawan kudin da take kashewa a bangaren tsaro, kwanaki biyu kafin firaiminista Keir Starmer ya gana da shugaba Trump a Washington.

    Karin zai kai girman kashi biyu da rabi cikin 100 na karfin tattalin arzikin kasar na cikin gida zuwa nan da 2027.

    Wannan kudin za a cire shi ne daga kudaden da kasar ke taimaka wa kasashen ketare.

    Sir Keir, ya ce halin da ake ciki ne ya tursasa masa daukar matakin, kuma nan gaba ma za a ci gaba da kara yawan kudin da ake kashewa bangaren tsaron kasar.

    Amurka ta yaba wa matakin tana mai cewa kwakkwaran mataki ne, to amma kungiyoyin agaji sun yi allawadai da matakin.

  3. An cimma yarjejeniyar bai wa Amurka damar haƙar ma'adanan Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an gwamnatin Ukraine sun ce an cimma yarjejeniya tsakanin ƙasar da Amurka kan aikin haɗin gwiwa na haƙar albarkatun ƙasa a Ukraine.

    Babu cikakken bayani kan yarjejeniyar, amma rahotanni na cewa Amurka ta jingine wasu daga cikin buƙatunta masu tsauri da ta gabatar daga farko.

    Shugaban Donald Trump ya yi ta ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar kwasar ma'adanan ƙasa na Ukraine a matsayin ladan taimakon da Amurkar ta bai wa Ukraine game da yaƙin da take yi da Rasha.

    Tun farko Ukraine ta yi watsi da batun, sai dai yanzu babu tabbas kan ko Ukraine ɗin ta samu tabbaci na tsaro daga Amurka kamar yadda shugabanta Volodymyr Zelensky ya nace kai kafin ya amince da yarjejeniyar.

  4. Ana buƙatar dala biliyan 500 domin sake gina Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙididdigar baya-bayan nan da aka yi a kan yadda za a sake gina Ukraine bayan yaƙin da ƙasar ta fuskanta ta nuna cewa za a kashe fiye da dala biliyan 500.

    Hakan na nuna cewa an samu ƙarin kashi 7 cikin 100 a kan kididdigar da aka yi shekara ɗaya da ta wuce, inda aka shirya kashewa wuraren da suka fi lalacewa kuɗi mafi tsoka, kamar ɓangaren gidaje da makamashi da kuma ilimi.

    Firaiministan ƙasar Denys Shmyhal ya ce sake gina ƙasar zai zamo wata babbar dama ga kamfanonin nahiyar turai da kuma haɗin kan nahiyar.

  5. Syria ta yi allawadai da mamayar da Isra'ila ta yi wa wasu yankunan ƙasarta

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Syria ta yi allawadai da mamayar da Isra'ila ta yi wa wasu yankuna na kasarta, a yayin kammala taron tattaunawar da aka yi.

    Gwamnatin ta yi kira ga sojojin Isra'ila da su tattara nasu ya nasu su janye daga yankunan da suka mamaye kwanaki bayan hambarar da gwamnatin shugaba Assad a karshen watan Disamban bara.

    Kazalika mahalatta taron sun yi watsi da bukatar Isra'ila ta cewa ba za a tura sojojin Syria zuwa kudancin Damascus ba.

    Tun da farko a yayin bude taron, shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar, Ahmed al-Sharaa, ya yi alkwarin kafa kwamiti da zai duba tare da gano wadanda ke da hannu wajen cin zalin al'ummar Syria.

    Sannan ya ce fiye da watanni biyu ke nan suna aiki tukuru wajen gano wadanda suka aikata ayyukan cin zali a kan 'yan Syriya.

    Har ila yau kuma za su kafa kwamiti na musamman da zai gano waɗanda suka aikata hakan, sannan su hukunta su daidai da laifin da suka aikata.

  6. Sanata Natasha ta maka Akpabio a kotu kan zargin ɓata suna

    .

    Asalin hoton, XnatashaAkpoti

    Bayanan hoto, Natasha Akpoti

    Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar dattajai, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.

    Natsha ta shigar da karar ne gaban babbar kotun tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick.

    Ta nemi kotun tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

    Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya bayyana cewar kalaman da babban mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya wallafa a shafinsa na facebook.

    Barista Giwa ya yi zargin cewar kalaman ba komai ba ne illa, ɓata suna, da tsokanar fada, da ƙanskantar da ita a idon abokan aikinta, da sauran al'umma.

    Sanata Natasha ta bukaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansa daga wallafa duk wani rubutu na batanci a game da ita.

    A makon da ya gabata ne Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwarta kan yadda aka bai wa wani dan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar. Inda ta ki amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da shugaban majalisar dattawan.

    Tuni aka umarci kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.

  7. An yanke wa tsohon ɗan majalisa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Indiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Indiya, ta yanke wa wani fitaccen tsohon dan majalisar daurin rai da rai bayan samun shi da hannu a kisan wani mutum da ɗansa, a yayin zanga-zanga a shekarar 1984.

    Sajjan Kumar, na jam'iyyar Congress, an same shi da laifi tun a farkon watan da muke ciki, kan shirya kisa, yayin da ake wani rikicin yan daba da kisan Firaiministan kasar Indira Gandhi ya haifar.

    Kumar dai na zaune a gidan yari bayan yanke masa hukunci daurin rai da rai kan wani kisan na daban da aka yi masa tun 2018. An yanke masa hukucin ne kan zargin kitsa kona wajen Ibada na Sikah da ke Delhi.

    Iyalan mutane da yawa da suka jikkata sakamakon zanga-zangar sun dauki lokaci suna ta fafutukar ganin an yi wa iyalai da yan'uwansu adalci, yayin da suka yi ta fuskantar koma baya, saboda dalilai na siyasa, da rashin katabus daga bangaren yansanda.

  8. Duniyoyi bakwai za su yi jerin-gwano a sararin samaniya cikin wannan mako

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masana ilimin taurari sun tabbatar da cewar duniyoyi bakwai da suka hada da Mars, da Jupiter, da Uranus, da Venus, da Neptune, da Mercury, da Saturn za su bayyana ƙarara a sararin samaniya da yammacin ranakun wannan mako da muke ciki.

    Jerin gwanon wanda ake kira 'Faretin duniyoyi' abu ne da zai fito yadda kowa zai iya gani, kuma hakan zai zama shi ne lokaci na ƙarshe da duniyoyin bakwai za su yi wannan jerin gwano, inda sai nan da shekarar 2040 za a sake ganin hakan.

    Lokacin da za a iya ganin wannan jerin gwanon duniyoyin shi ne, lokacin da rana ta faɗi a ranakun Talata da Laraba, da Alhamis da kuma Juma'a.

    Duniyoyi hudu: Mercury, da Venus, da Jupiter, da Mars, za su fito karara a gan su da ido ba tare da amfani da wata na'ura ba. Sai dai zai yi wuya a iya ganin duniyar Saturn saboda za ta kasance ƙanƙanuwa a kan falaki. Haka ma tilas sai an yi amfani da na'urar tsinkayar taurari kafin a iya hango sauran duniyoyin biyu, wato Uranus da Neptune.

    Duniyoyin da ke falakin, na zagaya rana ne kwatankwacin yadda duniyarmu ke yi.

    Yayin da saurinsu da nisansu daga rana ya bambamta, akwai lokutan da akan gan su sun jera reras a sararin samaniyar duniya, lamarin da kan zama mai ban sha'awa duk kuwa da cewar akwai nisa sosai a tsakaninsu.

  9. Tattalin arziƙin Najeriya ya yi haɓɓakar ba-zata a ƙarshen 2024

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka a rubu'i na huɗu na shekarar 2024, haɓɓaka mafi sauri a cikin shekara uku, kamar yadda alƙaluma suka nuna a yau Talata.

    Arziƙin cikin gida na Najeriya ya haɓɓaka da kashi 3.84%, sama da kashi 3.46% da aka samu a rubu'i na uku na shekarar ta 2024.

    A rubu'i na biyu na shekarar ta 2024 tattalin arziƙin ya haɓɓaka ne da kashi 3.19% yayin da rubu'i na farko kuma ya haɓɓaka da kashi 2.98%.

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce ɓangaren tafiyar da ayyuka na tattalin arziƙin shi ne kan gaba wajen haɓɓaka, da kashi 5.7% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.

    A shekarar ta 2024 jimilla, tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka ne da kashi 3.40% idan aka kwatanta da kashi 2.74% a 2023.

    Duk da haka, haɓɓakar ba ta cimma alƙawarin da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɗauka na haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar da kashi 6% ba a shekarar ta 2024.

  10. Naira Marley bai da hannu a mutuwar Mohbad - Kotu

    ...

    Asalin hoton, FB/Multiple

    Kotun majistare da ke zama a Sabo, da ke unguwar Yaba a jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad.

    Mai shari'a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad.

    Haka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde.

    Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma'aikaciyar jinyar da ta kula da Mohbad gabanin mutuwarsa, wato Feyisayo Ogedengbe, da ɗaya daga cikin abokan marigayin, Ayobami Sadiq bisa tuhumar su da sakaci, wanda ya kai ga mutuwar matashin mawaƙin.

  11. Shugaban Koriya ta Kudu ya nemi afuwar al'ummar ƙasar

    Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da aka dakatar, Yoon Suk Yeol

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da aka dakatar, Yoon Suk Yeol ya roƙi afuwar al'ummar ƙasar bisa matakin da ya ɗauka a bara na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar mulkin soji a ƙasar.

    Lokacin da ya kammala bayanai a zama na ƙarshe na kwamitin da aka kafa na tsige shi, Mista Yoon ya ce yana neman afuwa kuma yana gode wa al'umma.

    A farkon zaman, lauyoyin Majalisar dokokin Koriya ta Kudu sun ce shaidu sun nuna cewa Mista Yoon ya take dokar kundin tsarin mulki saboda haka nan ya kamata a tsige shi.

    Wajibi ne sai baki ya zo ɗaya a tsakanin alƙalai takwas na kotun kare kundin tsarin mulkin ƙasar kafin a iya tabbatar da matakin tsige shi da majalisar dokoki ta yi, kuma ana sa ran yanke hukunci na ƙarshe ne a tsakiyar watan Maris mai shigowa.

  12. Ruwan sama mai ƙarfi ya kashe mutum 29 a Afghanistan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun bayyana cewa mutum 29 sun rasa rayukansu sanadiyyar wani mamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a ƙasar Afghanistan.

    Mutum 21 sun mutu ne a lardin Farah da ke yammacin ƙasar bayan mamakon ruwan ya haifar da ambaliya.

    Sai kuma mutum takwas waɗanda suka mutu a kudancin Kandahar sanadiyyar ruwan saman mai ƙarfin gaske, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

  13. Wasu sun yi murna da mutuwar mijina - Matar Mohbad

    Matar marigayi Mohbad, Wunmi Aloba
    Bayanan hoto, Matar marigayi Mohbad, Wunmi Aloba

    Wunmi Aloba, wadda ita ce matar tsohon mawaƙin nan na Najeriya, Ilerioluwa Oladimeji Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad ta ce ta yi baƙin cikin mutuwar mijin nata, kasancewar mutuwar tasa ta zama tamkar nasara ce ga wasu mutane.

    A tattaunawarta da BBC, Wunmi ta ce ta kuma ji zafin mutuwar ganin yadda mijin nata ya yi fafutikar ganin ya kasance a raye, amma duk da haka sai da ya mutu.

    Mohbad ya mutu ne a shekarar 2023, inda nan take aka binne shi, sai dai daga baya hukumomi sun tono gawar tasa domin yin bincike kan abin da ya yi sanadin mutuwar tasa.

    "Mijina ba mai magana ba ne sosai, na ji zafin mutuwarsa," in ji Wunmi.

    Ta ce mahaifin mawaƙin ya yanke hukuncin binne shi jim kaɗan bayan mutuwarsa.

    "Kowa ya yi ta roƙon shi cewa kada ya binne mijina amma ya ƙi ji, har ya kira mai binne gawa a cikin daren, sai mutumin ya ce masa ba ya yin jana'iza a cikin dare".

    Mutuwar Mohbad ta taɓa ran mutane da yawa a Najeriya, lamarin da ya haifar da kiraye-kirayen ganin an yi adalci bayan rahotannin da suka ɓulla kan cewa ya fuskanci hantara da cin zarafi, a matsayin shi na mawaƙin da ke aiki ƙarƙashin kamfanin waƙa na Marlian records.

  14. Ƙasashen Afirka sun naɗa sabbin wakilan wanzar da zaman lafiya a Kongo

    Olusegun Obasanjo
    Bayanan hoto, Cikin sababbin wakilan har da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

    Wani taron ƙoli na haɗin gwiwa tsakanin shugabannin ƙasashen gabashi da kudancin Afirka sun naɗa sabbin wakilai domin jagorantar sanya ido kan ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

    Wakilan sun haɗa da tsoffin shugabannin Kenya da Najeriya da Habasha (Uhuru Kenyatta da Olusegun Obasanjo da Hailemariam Desalegn).

    Muhimman batutuwan da za su mayar da hankali a zaman lafiyan da ake cigaba da kokarin tabbatarwa sun haɗa da aiwatar da tsagaita wuta cikin gaggawa da sake buɗe hanyoyin shigowa da kaya domin shigo da kayayyakin jinƙai.

    Za kuma suyi ƙoƙarin ƙwato filin jirgin sama da ke Goma, ɗaya daga cikin biranen da ƴan tawayen M23 da ke da goyon bayan Rwanda suka ƙwace.

  15. An kama ƴan China biyu da ake zargi da laifin leƙen asiri a Phillippines

    Masu bincike a Philippines sun kama wasu ƴan China biyu da suke zargin da laifin leƙen asiri.

    Ana zargin an kama su ne a lokacin da suke wucewa ta wasu wurare masu muhimmanci a babban birnin ƙasar Manila cikin wata mota da ke da na'urar sauraro.

    Wuraren da suka bi sun haɗa da fadar shugaban ƙasar da kuma hedikwatar ƴan sanda.

    Jam'i'an tattara bayanan sirri na Philippine sun ce motar na ɗauke da na'urar ISMI-catcher-- wata na'ura da ke iya naɗar bayanan yanar gizo daga wurin da ke kusa.

    Ana cigaba da zaman ɗar-ɗar tsakanin China da Philippine kan ruwan da ake dambarwa kansa da ke tekun kudancin China.

    A watan da ya gabata ma ƴan China shida aka kama da ake zargi suna leƙen asiri a lokuta daban daban.

  16. Shugaban Koriya ta Kudu ya nemi afuwar ƴan ƙasar kan ƙoƙarin sanya dokar soji

    Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Koriya ta Kudu wanda aka dakatar, Yoon Suk Yeol, ya nemi afuwar ƴan ƙasar kan ƙoƙarinsa na sanya dokar soji a shekarar da ta gabata.

    Da yake gudanar da jawabinsa na ƙarshe a zaman shari'ar neman tsige shi, Mista Yoon ya ba ƴan ƙasar haƙuri tare da miƙa godiyarsa a garesu.

    Tun da farko lauyoyin majalisar Koriya ta Kudu sun ce shaidu na nuna Mista Yoon ya saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasar kuma ya kamata a tsigesa.

    Wajibi ne alƙalai takwas na kotun tsarin mulkin su yanke hukuncin na ko sun amince da tsigewar da majalisar dokokin ta yi masa nan da watan Maris.

  17. Putin ya ce zai yi wa Amurka tayin haƙar ma'adanai a yankunan Ukraine

    Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce akwai yiwuwar zai iya bai wa Amurka damar haƙar ma'adanai a yankunan Ukraine da ta mamaye.

    Kalamam nasa na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi Ukraine ɗin ta bai wa ƙasarsa damar tono ma'adanan nata a madadin taimakon da take ba ta na soji.

    Cikin wata hira a kafar talabijin ranar Litinin, Putin ya ce a shirye yake ya bai wa Amurka "tayi" na albarkatun domin yin aiki tare, ciki har da haƙar ma'adanai a "sababbin yankunan Rasha".

    Tayin zai iya jawo ƙasashen biyu su haɗa gwiwa wajen haƙo ma'adanan alminiyan domin taimaka wa Amurka shawo kan hauhawar farashi, a cewarsa.

  18. Poland ta ce za ta tsaurara tsaron samaniya bayan harin Rasha a Ukraine

    Harin Rasha

    Asalin hoton, EPA

    An ji karar jiniyar ankararwa a mafi yawan yankunan kasar Ukraine, saboda hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai.

    Lamarin ya shafi zirga-zirgar jiragen sama a Poland mai maƙoftaka, kuma sojojin Poland sun ce za su ƙarfafa tsaro a iyakar yankinsu.

    Rahotanni sun bayyana cewa gidaje da dama sun lalace a birnin Kyiv na Ukraine, wata mace guda kuma ta samu rauni.

    Rasha ta ce ta lalata jirage marassa matuka na Ukraine 19 da tsakar dare.

  19. Muna da fetur ɗin da zai ishi Najeriya gaba ɗaya - Dangote

    Dangote

    Asalin hoton, @DangoteGroup

    Matatar man fetur ta Dangote ta ce tana da fetur mai yawa a lalitarta da zai ishi buƙatun Najeriya baki ɗaya, kamar yadda shugaban kamfanin Aliko Dangote ya bayyana.

    Da yake magana a ƙarshen mako, Dangote ya ce matatar na da mai sama da lita miliyan 500.

    Kalaman nasa na zuwa ne daidai lokacin da direbobin manyan motoci masu dakon mai ke yajin aiki a jihar Legas sakamakon abin da suka kira "cin zali" da 'yansanda ke yi musu a titunan birnin.

    "Yanzu da muke magana, muna da lita sama da rabin biliyan. Matatar na samar da albarkatu isassu kamar fetur, da dizel, da kalanzir domin amfanin 'yan Najeriya 100 bisa 100," in ji Dangote.

    Ya faɗa wa tawagar wakilai daga ƙasar Zambia cewa "da ma matatar an yi ta ne ba don Najeriya kawai ba, an yi ta ne domin amfanin Afirka baki ɗaya".

  20. Dalilin da ya sa muke yajin aiki a Legas - Direbobin manyan motoci

    Yajin aikin da direbobin tankar man fetur suka fara a Legas da kuma wasu sassan kasar ya haifar da fargabar ƙarancin mai da kuma katsewar karkokin sadarwa.

    Mambobin kungiyar direbobin manyan motocin haya ta Najeriya NATO sun dakatar da lodin mai tun daga ranakun Asabar da Lahadi, sakamakon zargin da suka yi cewa jami’an gwamnatin jihar Legas na cin zarafinsu a kan manyan hanyoyin jihar.

    Sai dai gwamnatin jihar Legas ta ce tana aiwatar da wani sabon tsari ne wanda ya dace da zamani don rage cunkoson ababen hawa.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman:

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku saurari rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman: