Sai da safe
Nan za mu dakata da rahotonni a wannan shafi, kafin mu zo da wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabta da kuma sauran sassan duniya na ranar Juma'a 24 ga watan Oktoba, 2025.
Habiba Adamu, Haruna Kakangi, da Umar Mikail
Nan za mu dakata da rahotonni a wannan shafi, kafin mu zo da wasu sababbi gobe da safe.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar 'yansandan ƙasa da ƙasa ta Interpol ta ce ta kama mutum 11 da ta kira manyan 'yanta'adda a Najeriya, a wani samame da ya shafi ƙasashen Afirka da dama.
Kamen wani ɓangare ne na Operation Catalyst, wanda ya farmaki masu ɗaukar nauyin ta'addanci da kuma laifukan da suka shafi hakan a ƙasashen Afirka shida.
A cewar Interpol, an gudanar da samamen na wata uku tsakanin watan Yuli da Satumba na 2025, inda aka yi nasarar kama mutum 83 da kuma gano 160 da ake nema.
Ƙasashen da suka taimaka wa shirin sun ƙunshi Najeriya, da Angola, da Kamaru, da Kenya, da Namibia, da Sudan ta Kudu.
Interpol ta tabbatar da kama mutum 11 a Najeriya, ciki har da manyan mambobi na ƙungiyoyin 'yanbindiga.

Asalin hoton, EPA
Ƙasashe fiye da 20 da ke taimaka wa Ukraine sun yi alƙawarin "daina sayen man fetur da gas ɗin Rasha" a matsayin wani ɓangare na matsa wa Shugaba Vladmir Putin dakatar da yaƙi a Ukraine ɗin.
"Muna so katse hanyoyin samun kuɗi na Rasha," kamar yadda Firaministan Birtaniya Kei Starmer ya bayyana bayan karɓar baƙuncin taron ƙasashen da ke da aniyar taimaka wa Ukraine a yau Juma'a.
A kwanan nan Birtaniya da Amurka suka saka wa manyan kamfanonin mai na Rasha takunkumi, yayin da Tarayyar Turai ta tunkari ɓangaren iskar gas na Rashar.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda ya halarci taron a Landan, matsa wa Rasha ce kaɗai hanyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin.
Amma ba a bayar da wata sanarwar bai wa Ukraine ɗin makamai masu cin dogon zango ba, waɗanda Shugaba Zelensky ke nema domin kai hare-hare tsakiyar Rasha.

Asalin hoton, Defense Headquaters
A yau Juma'a ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tuɓe Hafsan Hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, da sauran hafsoshin tsaron ƙasar.
Shugaban ya ce ya yi hakan ne domin "ƙyautata tsaron ƙasa".
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, Tinubu ya yi musu fatan alkairi tare da bayyana sunayen sabbin hafsoshin da za su maye gurbin waɗanda aka sauke ɗin.
Sunayen sabbin hafsoshin tsaro:
Ku karanta cikakken bayani kan sababbin jami'an tsaron a nan: Su wane ne sabbin hafsoshin tsaron da Tinubu ya naɗa?

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya ɗauki matakain sauya hafsohin tsaron ƙasar, yana mai gode wa tsofaffin manyan jami'an tsaron da ya sauke.
Wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne saboda "ƙyautata tsaron ƙasa"
"Na amince da sauya shugabancin rundunar tsaro domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya," in ji shi.
"Ina gode wa Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin tsaron da suka gabata saboda hidima da sadaukarwar da suka yi, kuma ina neman sababbin shugabannin da su kyautata ƙwarewar aiki, da ankararwa, da haɗin kai a tsakanin sojojinmu."
Sauyin shugabannin rundunar sojin na zuwa ne a lokaci da ake ci gaba da raɗe-raɗi game da shirin juyin mulki da aka ce wasu sojoji sun tsara, zargin da rundunar sojin ta musanta.
Sunayen sabbin hafsoshin tsaro:

Asalin hoton, Reuters
An cire Najeriya da Afirka ta Kudu daga jerin kasashen da aka fi saka wa ido saboda yawan aikata zamba da kuma halasta kuɗaɗen haram a duniya.
Ƙungiyar kula da irin waɗannan laifuka ta Financial Action Task Force (FATF) mai hedikwata a Faransa ta bayar da sanarwar cire ƙasashen biyu mafiya girman tattalin arziki a Afirka yau Juma'a bayan taronta.
Ta kuma cire ƙasashen Burkina Faso da Mozambique daga jerin nata na ƙasashen da take bayar da shawarar tsaurara saka ido a kan su saboda ayyukan masu damfara da halasta kuɗin haram.
A shekarar 2023 ne aka saka Najeriya da Afika ta Kudu ciki jerin, kuma FATF ta ce Najeriya ta ƙarfafa wa hukumomi gwiwar yin aiki tare.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matakin a matsayin "gagarumin cigaba a yunƙurin Najeriya na gyaran tattalin arziki da kuma inganta ayyukan ma'aikatun gwamnati".

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni a kafafen yaɗa labarai na Amurka da Rasha sun ce wakili na musamman a fannin tattalin arziki na Moscow ya isa birnin Washington domin tattaunawa da jami'an gwamnatin Donald Trump.
Ziyarar da Kirill Dmitriev ya kai na zuwa ne kwana biyu bayan Shugaba Trump ya ƙaƙaba takunkumai kan manyan kamfanonin mai biyu na Rasha.
A ziyarar da ya kai a watan Afrilu, Mista Dmitriev ya kasance jami'i daga Rasha na farko da ya kai ziyara Washington tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Ziyarar wadda a lokacin ne ya tattauna da Steve Witkoff, ta kasance alama ce da ke nuna dangantakar kasashen ta fara inganta.

Asalin hoton, Pete Hegseth on X
Sakataren tsaro na Amurka, Pete Hegseth ya sanar da cewa ƙasar ta ƙara kai wani hari kan wani jirgin ruwan da ake zargin na masu safarar miyagun ƙwayoyi ne, a ranar Juma'a.
An kai harin ne kan jirgin a tekun Caribbean, kan wasu gungun masu safarar da Hegseth ya bayyana da 'Tren de Aragua' masu aikata manyan laifuka.
Hegseth ya ce "maza shida masu ta'addancin miyagun ƙwayoyi" na cikin jirgin kuma duk an kashe su.
Amurka ta kai hare-hare kan jiragen ruwa a yankin, a matakin da shugaba Donald Trump ya bayyana a matsayin yunƙurin kawo ƙarshen safarar miyagun ƙwayoyi.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Mutanen ƙasar Guinea sun fara bayyana matuƙar mamaki kan sanarwar da ta ce sai ƴantakarar shugabancin ƙasar sun biya miliyan 875 kuɗin ƙasar ($100,000; £75,000) don tsayawa takara a zaɓen da za ayi a watan Disamba, wanda zai kai ga miƙa mulki ga farar hula.
Ƙasar ta kasance ƙarƙashin mulkin soji tun bayan da kanal Mamady Doumbouya ya yi juyin mulki a shekarar 2021.
Kuma za a yi zaɓen ne ƙarkashin wani sabon kundin tsarin mulki da ya bai wa Doumbouya damar tsayawa takarar shugabancin ƙasar – duk da cewa bai fito ya bayyana aniyarsa ba.
Ko da yake a baya an samu kuɗaɗen da ake biya har sun kai miliyan 800 na kuɗin ƙasar, wasu masu sharhi sun yi fatan ganin an rage saboda a baiwa ƙarin mutane damar tsayawa a zaɓen mai cike da tarihi.

Asalin hoton, PDP
A Najeriya, wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na shiyyar arewa maso yammacin ƙasar, sun yi watsi da matakin da gwamnoni suka dauƙa na tsayar da Tanimu Turaki a matsayin ɗan takararsu a babban taron da jam’iyyar za ta yi a watan gobe.
Uwar jam’iyyar ta PDP ta amince da miƙawa shiyyar muƙamin shugabancin jam’iyyar, amma da sharaɗin sai an tuntuɓi masu ruwa da tsaki a yankin.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Sokoto, Muhammad Bello Aliyu na cikin shugabannin da suka yi fatali da matakin da gwamnonin suka ɗauka.
Saboda a cewarsa, ba a basu damar zama su tattauna ba, gabannin tsayar da Turaki.
Sai dai wasu na ganin tamkar sun kwarewa jam'iyyar baya ne saboda a gabansu aka zaɓe shi, amma daga baya suke nuna ƙin amincewa.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta daɗe tana fuskantar rigingimu na cikin gida, lamarin da wasu ke ganin ya taimaka wajen ficewar wasu gwamnoninta zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance da sakataren harkokin wajen ƙasar, Marco Rubio sun yi suka ga yunƙurin majalisar dokokin Isra'ila na karɓe Gaɓar Yamma da kogin Jordan da ta mamaye.
A ranar Laraba ne ƴan siyasa masu tsananin ra'ayin riƙau suka bayar da amincewa a matakin farko kan wani ƙudurin dokar Isra'ila a kan yankin, wanda Falasɗinawa ke fatan zai zama wani ɓangare na ƙasarsu mai cin gashin kanta.
A ƙarshen ziyarsa zuwa Isra'ila Vance ya bayyana cewa "Idan wani neman suna na siyasa ne, wannan babbar wauta ce kuma kamar wani cin mutunci ne a gare ni." Inda ya ƙara da cewa "Isra'ila ba zata karɓe Gaɓar Yamma da kogin Jordan ba. Manufar gwamnatin Trump ita ce Isra'ila ba zata karɓe Gaɓar Yamma da kogin Jordan ba."
Shi ma Rubio ya yi irin wannan gargaɗi kafin ya tafi Isra'ailar na cewa karɓe yankin barazana ce ga shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Sai dai Firaiministan Isra'ilar ya bayyana yunƙurin a matsayin "tsokana daga ƴan adawa don janyo saɓani."
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Benjamin Netanyahu ta jaddada cewa jam'iyyarsa ta Likud mai ra'ayin riƙau da ƙawarta ta ultra-Orthodox ba su kada ƙuri'a a kan ƙudurin ba, " sai dai wani ɗan jam'iyyar Lukud guda da ke jin haushin cire shi da aka yi daga shugabancin wani kwamiti a majalisar. "
Inda ya ce ba tare da amincewar jam'iyyar Lukud da ƙawarta ba, babu inda ƙudurin zai je.

Ba a ci gaba da shari'ar jagorar ƴan tawayen Bifra, Nnamdi Kanu ba kamar yadda aka shirya yi a ranar Juma'a.
Kanu wanda ke kare kansa ya shiada wa babbar kotun tarayyar da ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriya cewa, bai samu takardun ƙarar ba, don haka yana ɓuƙatar lokaci.
Wanda ake tuhumar ya kuma buƙaci kotun da ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun dinga bari ana ganinsa a kullum, saɓanin ranaku uku, litinin, laraba da juma'a da ake ganinsa a yanzu.
"Mai shari'a ina da masu bayar da shaida 23 da zasu zo daga ƙasashen duniya domin shari'ar, don haka ina buƙatar lokaci," In ji Kanu.
An ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar Litinin mai zuwa.
A ranar Alhamis ne Nnamdi Kanu ya sallami duka lauyoyin da ke kare shi, inda ya sanar da kotun cewa zai ci gaba da kare kansa.

Asalin hoton, Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images
Yayin da babban zaɓe ke ƙaratowa a Tanzania, zabiya sun shiga fargaba kan irin hare-haren da ake kai musu saboda tsafe-tsafen da ake dangantawa da zaɓe a ƙasar.
Wata wadda ta rasa hannuwa biyu sakamakon irin wannan hari, Mariamu Stanford, ta ce a lokacin da aka shiga yanayin siyasa, ya kan zo mata da fargaba da barazanar sake ganin abun da ya faru da ita a baya.
Akwai waɗanda suka yi imanin cewa wasu sassan jikin zabiya bayar da ƙarfin iko ko arziki, batun da ba gaskiya ba ne, amma yana ci gaba da sanadin kisan zabiya da kuma tozarta kaburbura.
Aƙalla an kai hare-hare 200 kan zabiya a shekarun bayan-bayan nan, lamarin da ya tilasta wa iyalai tserewa ko kuma ɓuya.

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya isa birnin London ranar Juma'a, domin ganawa da ƙawancen ƙasashen da suka yi alƙawarin tabbatar da zaman lafiya a ƙasarsa, idan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Firaiministan Burtaniya, Keir Starmer tare da Zelensky za su ɗauki baƙuncin sakatare janar na ƙungiyar NATO, Mark Rutte, Firaiministan Denmark, Mette Frederiksen da Firaiministan Netherlands, Dick Schoof da kuma shugaban Faransa, Emmanuel Macron waɗanda za su shiga taron ta intanet.
Shugabannin za su tattauna yadda za a ƙara matsin lamba a kan Rasha ta hanyar sanya mata takunkumai, sannan a ƙarfafa tsaron Ukraine ta amfani da kadarorin Rashar da aka hanata taɓawa.
Taron zai kuma duba yiwuwar ƙarawa Ukraine makamai masu dogon zango.

Asalin hoton, Joseph Ayo Babalola University
Sabon shugaban hukumar zaɓen Najeriya, (INEC), Joash Amupitan, ya yi alƙawarin kare dokokin zaɓe da na ƙundin tsarin mulkin ƙasar.
Amupitan ya ƙara da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bashi umarnin cewa ya tabbatar da an yi zaɓe mai inganci a faɗin ƙasar.
Amupitan wanda ya bayyana hakan bayan rantsar da shi a ranar Alhamis a Abuja, ya ce “ ba wannan kaɗai zan tabbatar ba, zan kuma yi tafiya da masu ruwa da tsaki, domin duk yadda ake ganin nasara ba zata samu ba sai an buƙaci masu ruwa da tsaki.”
Sabon shugaban shi ne jagorar hukumar zaɓen ƙasar na shida tun bayan komawar ƙasar turbar dimokradiyya a shekarar 1999.

Asalin hoton, AFP
A ɗaki guda, ba na'urori da kayan aikin gano ƙwayoyin halitta na DNA, kuma ba wuri mai sanyi na ajiye gawawwaki, tawagar masana masu binciken ƙwaƙwaf a asibitin Nasser da ke Gaza na fuskantar ƙalubale.
Isra'ila ta dawo da gawawwakin Falasɗinawa 195 a kwanaki 11 da suka wuce, a musayar da suka yi da gawawwaki 13 na mutanen da aka yi garkuwa da su, a ƙarƙashin yarjejeniyar da shugaba Donald Trump ya taimaka aka cimma.
Wasu hotunan da hukumomin lafiya na Gaza suka fitar, sun nuna wasu gawawwakin sun fara ruɓewa, wasu sanye da kaya, wasu sai kanfai, wasu kuma da raunuka da dama a jikinsu.
Haka kuma da yawa daga cikin gawawwakin hannuwansu a ɗaure ta bayansu, kuma likitocin sun ce wasu gawawwakin an kawo su da idanuwansu a ɗaure da ƙyalle, ko kuma an ɗaure musu wuya.
Sai dai tawagar ƙwararru masu binciken ƙwaƙaf da ke asibitin Nasser, suna aiki ba tare da kayan da ake buƙata ba, wurin gano ko an azaftar da muzguna wa mamatan, sannan wurin gano ainihin gwawwakin su waye.
Shugaban sashen, Dr Ahmed Dheir, ya ce babban ƙalubalen shi ne na rashin waje mai ƙanƙara da za su adana gawawwakin.
Gawawwakin sun isa Gaza sun yi ƙanƙara sosai, kuma sai sun ɗauki kwanaki kafin su saki, abin da zai kawar da duk wata dama ta gano ko su waye ta hanyar haƙoransu da kuma gano musabbabin mutuwarsu.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan takarar jam'iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya shaida wa BBC cewa a shirye yake ya kare abin da ya bayyana "nasara ƙarara" da ya samu.
Yayin da al'ummar ƙasar ke ci gaba da dakon sakamakon zaɓen da za a bayyana a ranar Litinin mai zuwa, Bakary, wanda shi ma tsohon jami'in gwamnatin Paul Biya ne, ya ce zai amince ne kawai da sakamako na gaskiya.
Wannan kalami nasa dai zai ƙara rura wutar zaman ɗarɗar da ake yi a ƙasar ta yankin tsakiyar Afirka.
Tun daga farkon makon nan ne mutane, musamman magoya bayan Bakary suka riƙa fita kan tituna domin yin gangamin kira ga gwamnati ta tabbatar ta fitar da sakamako daidai da zaɓin al'umma.
A baya an tsara cewa za a bayyana sakamakon zaɓen ne ranar Alhamis, sai dai wata sanarwa daga gwamnati ta ce an ɗage bayyana sakamakon zuwa ranar Litinin ɗin mako mai zuwa.
Wasu alkalumman da kafofin yada labaran kasar suka ruwaito sun nuna cewa akwai yiyuwar shugaba Paul Biya ne zai zarce kan mulkinsa na shekara 43.

Yau Juma'a ce rana ta farko da jagoran ƙungiyar ƴan awaren Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, zai fara kare kansa a gaban kotu bisa tuhumar da hukumomin Najeriya suke masa, waɗanda suka jiɓanci tunzura haifar da husuma da cin amanar ƙasa.
Hakan ya biyo bayan korar lauyoyinsa da ya yi, a zaman babbar kotun tarayyar da ke Abuja a ranar Alhamis.
Jagoran lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu, Kanu Agabi (SAN) bayan janyewarsu, ya shaida wa manema labarai cewa, jagoran ƴan awaren na da ƴancin kare kansa.
Ko da yake babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa Nnamdi Kanu ya kori lauyoyin nasa, amma kotun ta amince ya fara kare kansa daga zaman na jiya.
Lauyoyin sun yi masa fatan alheri.
Gwamnatin Najeriya ce ta shigar da ƙarar, kuma cikin tuhume-tuhumen da ake masa sun haɗa da na ta'addanci.
Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Juma'a daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.