Labarai da dumi-dumi, Iran ta ce aƙalla mutum 430 aka kashe tun fara yaƙi
Aƙalla mutum 430 ne aka kashe, sannan an jikkata 3,500 a Iran tun soma yaƙi da Isra'ila ranar 13 ga watan Yuni, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar - kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nour ya ruwaito.
Wannan ne sabon bayani da hukumomi suka fitar cikin kwanaki a Iran na alkaluman waɗanda suka mutu.
A baya, ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana a ranar Lahadi cewa aƙalla mutum 224 ne aka kashe, yayin da wata ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta saka alkaluman zuwa 657 a ranar Juma'a.