Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Taƙaitattu

  • An gano gawa biyu a Isra'ila bayan harin Iran kan wani gida
  • 'Za mu buɗe mashigar Hormuz idan jiragen sun amince su biya ɓarnar yaƙin
  • IRGC ta ce Amurka da Isra'ila sun kashe shugaban sashen leƙen asirinta'
  • Isra'ila ta ɗauki alhakin kisan shugaban leƙen asirin IGRC
  • Harin Iran ya kashe mutum huɗu a Haifa na Isra'ila
  • Isra'ila ta ce ta kai hari kan muhimmiyar cibiyar tace mai ta Iran

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An gano gawa biyu a Isra'ila bayan harin Iran kan wani gida

    Hukumomin Isra'ila sun ce an gano gawarwakin wasu mutum biyu a cikin ɓaraguzai, bayan wani harin makami mai linzami na Iran a kan wani gida a birnin Haifa na arewacin Isra'ilar.

    Har yanzu kuma ba a san inda wasu mutum biyu suke ba.

    Can a Iran ɗin kuwa kafofin yaɗa labaran Iran sun ce wani harin sama da aka kai kan wani gini da jama'a ke zama a ciki a babban birnin ƙasar, Tehran ya kashe mutum 13.

    Wasu ƙarin hare-haren da aka kai a babban birnin sun faɗa kan wata jami'a da kuma wani wajen rarraba iskar gas, abin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a birnin.

    Jami'an Iran sun ce hare-haren Amurka da Isra'ila a birnin Qom na tsakiyar ƙasar, sun kashe aƙalla mutum biyar.

  2. Iran ta ce mummunan ramuwar gayya za ta biyo idan Trump ya aiwatar da barazanarsa

    Iran ta yi gargaɗin cewa muddin Shugaba Trump, ya ci gaba tare da aiwatar da barazanarsa ta kai hari kan wuraren farar hula da suka hada da gadoji da tasoshin wutar lantarki, to shakka babu ramuwar-gayya da za ta yi za ta kasance mummunar gaske kuma ba ƙarama ba.

    Yau ne ya kamata ya zama ƙarshen wa'adin da Shugaba Trump ya ɗeba wa Iran ta buɗe mashigar Hormuz, ko ta fuskanci munanan hare-hare na lalata kayayyakinta da ba na soji ba - ciki har da tashoshin samar da lantarki.

    A ranar Lahadi ne, shugaban na Amurka ya kara sanya sabon wa'adi na zuwa gobe Talata, ga Iran ɗin ta sake buɗe mashigar.

    Kafofin yaɗa labarai na Amurka na cewa masu shiga tsakani - na can suna ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta tsawon kwana 45 - kodayake rahotanni na cewa ba lalle a samu nasarar hakan ba.

    A dalilin sabuwar barazanar ta Trump, farashin mai ya yi sama a Asia a yau Litinin, amma kuma kasuwannin hannun jari na nan yadda suke - ba su tashi ba, kuma ba su yi kasa ba.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-sate barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.