Harin jiragen sama marasa matuƙa ya lalata tashar wutar lantarki a Sudan
Kamfanin wutar lantarkin ƙasar Sudan ya ce harin jiragen sama marasa matuƙa da dakarun RSF suka kai ya lalata tashar wutar lantarki a birnin El-Obeid da ke tsakiyar kudu maso tsakiyan Sudan, wanda rundunar sojin ƙasar ke kula da shi.
Wannan lamarin dai ya ya janyo rashin wutar lantarki mafi girma a faɗin yankin.
El-Obeid ta kasance ita ce babban birnin jihar Kordofan ta Arewa, ita ce sabon fagen daga a rikicin da ya daɗe tsakanin sojojin ƙasar da RSF.
Rundunar sojin ƙasar ta sanar a karshen watan da ya gabata cewa ta sake karɓar wasu birane da ke kudu da El-Obeid daga hannun RSF, wadda ta kaddamar da yunkurin mamaye manyan wurare a Kordofan.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da halin jin kai ke ƙara tabarbarewa yayin da yaƙin da aka daɗe ana fama da ita ke ci gaba da haddasa wahala ga fararen hula inda wasu kuma ke tserewa.
Fiye da fararen hula 100 ne suka rasa rayukansu a hare-haren jiragen sama mara matuƙa, yayin da dubban mutane suka tsere a faɗin Kordofan tun farkon Disamba 2025.
Dukkan ɓangarorin da ke yaƙi da juna na kallon Kordofan a matsayin muhimmin wuri na gwada ƙwanji don raba ikon ƙasar, saboda inda jihar take. Jihar na matsayin hanyar zuwa Yammacin Darfur, inda RSF ke da ƙarfi.