Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/04/2025

Wannnan Shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ministocin Najeriya da Nijar sun tattauna a birnin Yamai

    Ministocin harkokin wajen Najeriya da Nijar sun gudanar da wata tattaunawa ta musamman kan al'amura da dama da suka shafi harkokin tsaro da tattalin arziki a kan iyakokin ƙasashen biyu.

    Hakan dai na zuwa ne bayan da Najeriya ta sake sabunta kiraye-kirayen neman a saki hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, wanda ke tsare a fadar shugaban ƙasar da ke Yamai.

    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya tattauna da ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare, a ziyara ta biyu da wani babban jami'in Najeriya ya kai tun bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar a 2023, bayan Janar Christopher Musa, babban hafsan tsaron Najeriya ya ziyarci Nijar a watan Agustan bara,

    ''Tattaunawar ta gudana ne cikin yanayi mai cike da mutuntawa ta kuma bayar da damar yin nazari mai zurfi kan ƙalubalen da ƙasashen biyu ke fuskanta," in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da ministocin biyu suka fitar.

    A ɓangaren tattalin arziki, ministocin sun tattauna kan aikin layin dogo da zai haɗa garuruwan Kano da Katsina na Najeriya zuwa Maradi a Nijar, wanda za a buɗe a shekarar 2026.

    Har ila yau, sun tattauna batun gina babbar hanyar Trans-Sahara, da shirin bututun iskar gas da za a yi a yankin Sahara, da kuma batutuwan da suka shafi haraji.

    Nijar da Burkina Faso da Mali sun fice daga ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka a farkon wannan shekara, inda suka zargi ƙungiyar ECOWAS da gazawa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

    Dukkanin ƙasashen uku dai na ƙarƙashin jagorancin sojoji ne, kuma suna fuskantar munanan hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

  2. Kotun Amurka ta samu tsohon sojan Gambia da laifin azabtar da mutane

    Wata kotu a Amurka ta samu wani tsohon sojan Gambia da laifin hannu a laifukan azabtarwa da aka aikata a lokacin da Yahya Jammeh ke kan karagar mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka.

    An samu Michael Sang Correa da laifin haɗa baki domin azabtar da waɗanda ake zargin abokan adawa ne a lokacin da yake aiki ƙarƙashin rundunar soji da aka fi sani da "Junglers".

    Hakan ya biyo bayan shari'ar da aka shafe mako guda ana yi a birnin Denver da ke jihar Colorado, a ƙarƙashin wata doka da ba kasafai ake amfani da ita ba wadda ke hukunta laifukan da aka aikata a wajen Amurka.

    An fara tsare Correa ne a Amurka a shekarar 2019 bayan ya wuce wa’adin bizar zamansa a ƙasar, shekaru uku bayan ya koma Denver inda rahotanni ke cewa yana aikin leburanci.

    An tuhumi Correa mai shekara 46 a 2020 da laifin azabtarwa da kuma haɗa baki wajen azabtar da aƙalla mutane shida a Gambia.

    Shi ne mutum na farko wanda ba ɗan Amurka ba ne da aka samu da laifin azabtarwa a wata kotun tarayya wanda ake zargin ya aikata laifukan a ƙasashen waje, a cewar ma’aikatar shari’a.

    Sau biyu kawai aka taɓa amfani da dokar tun lokacin da aka kafa ta a 1994 amma duka shari'o'in da suka gabata sun shafi ƴan kasar Amurka ne.

  3. Buɗewa

    Masu bibiyar mu, barka da wannan safiya ta Alhamis.

    A yau ma za mu kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su X da Facebook da Instagram da YouTube domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku shiga shafinmu na WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu.

    Ku kasance tare da mu.