Bankwana
Masu bibiyar shafin kai tsaye na BBC Hausa, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 07/09/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Masu bibiyar shafin kai tsaye na BBC Hausa, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Asabar.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, FT
Shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, CIA, ya ce akwai yuwuwar cewa Rasha ta shirya amfani da makaman nukiliya a shekarar farko ta yakinta da Ukraine.
William Burns ya bayyana cewa sanin haka ya sa ya aika wa gwamnatin Rasha, gargadin abin da zai iya biyo baya.
Shugaban ya fadi hakan ne a wani taro a London, tare da takwaransa na Birtaniya , Richard Moore.
Shi kuwa shugaban hukumar leken asirin ta Birtaniya, M16, ya jaddada muhimmancin ci gaba da taimaka wa Ukraine ne a yakin, inda ya bayyana take-taken hukumomin leken asiri na Rasha a baya-bayan da cewa abin ya wuce hankali.

Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga Sudan sun ce ɗaruruwan iyalai na yin ƙaura daga wani gari dake kusa da Khartoum babban birnin ƙasar, bayan yaƙi ya ƙazanta tsakanin rundunar soji da mayaƙan RSF.
Faɗan ya fi ƙamari ne a wata barikin soji a Bahri, inda mayaƙan RSF ke ƙoƙarin ƙwace iko, amma abin ya shafi gidajen mutane.
A ranar Juma'a, ƙwararru a Majalisar Dinkin Duniya suka buƙaci a gaggauta tura dakarun ƙasashen duniya domin bayar da kariya ga fararen hula a Sudan.
Mutane fiye da miliyan goma suka guda daga gidajensu tun da aka fara yaƙin a watan Afirelun bara.

Asalin hoton, EPA
Mutane aƙalla huɗu ne suka mutu, wasu da dama kuma suka samu rauni a Vietnam, inda guguwar Typhoon Yagi ta yi ɓarna a arewacin ƙasar.
Masunta da dama sun ɓace a cikin teku.
Guguwar ta tumɓuke bishiyoyi da dama, kuma ta kwashe kwanon gidaje da dama, yayin da ake gargaɗin mutane da su ci gaba da zama a cikin gida.
Birnin Haiphong ne guguwar tafi yin ɓarna, inda tituna suka cika da ɓaraguzan abubuwan da guguwar ta kwaso.
A baya ma guguwar Yagi ta yi ɓarna a tsibirin Hainan, inda mutum huɗu suka mutu, kuma wasu dubu ɗari takwas suka faɗa cikin rashin hasken lantarki.
A bana dai ita ce guguwa mafi muni a nahiyar Asiya.

Asalin hoton, EPA
Hukumomin Falasɗinu sun yi allawadai da muzgunawar da ake yi wa Falasdinawa a gidan yarin Megiddo na Isra'ila, bayan wani bidiyo da jaridar Haaretz ta Isra'ilan ta wallafa a shafinta na Intanet.
Bidiyon ya nuna wani jami'in tsaron Isra'ila sanye da kayan sulke yana tsaye, yayin da wani kare ke yin haushi a kan gomman fursunoni da ke kwance, fuskokinsu na kallon ƙasa, wasun su a tuɓe
Hukumar gidan yarin Isra'ila ta shaidawa jaridar Haaretz cewa ana gudanar da hakan lokaci zuwa lokaci a gidan yarin.
Shugaban ƙungiyar Falasɗinawa fursunoni, Abdullah al-Zughary, ya ce suna fuskantar muzgunawa sosai a gidajen yarin Isra'ila.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar Human Rights Watch ta buƙaci hukumomi a jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo su gudanar da bincike kan fasa gidan yarin Kinshaha wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 129.
Ministan cikin gidan ƙasar ya ce an yiwa fursunonin mata da yawa fyaɗe a lokacin yamutsin.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ɗin ta koka da yadda aka kashe har fursunoni 24 da harbin bindiga, tana mai cewa gidan yarin Makala, kamar sauran da ke sassan Congo yana ɗauke da fursunoni da yawan su ya zarce ƙa'ida.
Human Rights Watch ta ce ya kamata gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin samar da tsaro a gidajen yari.
Ta kuma nemi a yi tanadin kariya ga fursunoni mata daga duk wani na'in cin zarafi.

Asalin hoton, EPA
Hukumomin Kenya sun ce za a fara gwajin ƙwayar halitta ta DNA ranar Litinin domin tantance gawarwakin ɗalibai 18 da suka mutu a gobarar da ta tashi a wata makarantar furamare a birnin Nairobi.
Iyaye da dama na cikin halin ɗimauta sakamakon rashin ganin 'ya'yansu bayan gobarar.
Mataimakin shugaban ƙasar, Rigathi Gachagua ya ce kawo yanzu ba a iya gano ɗalibai 70 ba, bayan faruwar lamarin.
To amma yayin da yake jawabi ga manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura ya bayar da mabambantan alƙaluma.
''Abin da muka tabbatar shi ne ɗalibai 18 sun mutu. Kuma yara 156 ne ke kwance a ɗakin kwanan ɗaliban lokacin da wutar ta tashi. Don haka akwai ɗaliban da har yanzu ba a gani ba. Ba za ka iya cewa 20 ko 30 ko 40 ko ma 70 ba, saboda hakan ka iya zama kuskure,'' in ji shi.
Iyalai da dangin ɗaliban - waɗanda suka yi sansani a makaranta suna jiran labarin 'ya'yan nasu - sun buƙaci amsa daga hukumomin ƙasar.
Jami'an gwamnati sun yi kira ga waɗanda suka taimaka a aikin ceton su dawo da yaran da suka kuɓutar domin taimakawa wajen tantance duka yara.
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta kafa kwamitin gano yaran tare da kwantar wa waɗanda lamarin ya shafa hankula

Asalin hoton, Getty Images
'Yar wasan Najeriya, Flora Ugwunwa ta lashe lambar azurfa a gasar jifan mashi ta mata a gasar wasannin nakasassu ta Paralympic 2024 da ke gudana a birnin Paris.
Ugwunwa ta ƙare a mataki na biyu bayan da jifanta ya kai mita 19.26, bayan na Nurkhon Kurbanova, 'yar Uzbekistan da jifanta ya kai mita 21.12.
Nasarar Ugwunwa ya sa Najeriya ta samu lambar yabo ta farko a ɓangaren jifan mashi na mata, wanda kuma shi ne lambar yabo ta huɗu da Najeriya ta samu kawo yanzu a gasar.
'Yar wasan mai shekara 40 ta ci gaba da haskawa fagen wasanin, inda awo yanzu ta lashe lambobin yabo uku a jere a gasar nakasassu ta Paralympic, (bayan da ta lashe zinare biyu a Rio da Tokyo sai kuma yanzu ta samu azurfa a Paris)
Sauran 'yan wasan Najeriya da suka samu lambobi a gasar kawo yanzu sun ne Onyinyechi Mark da Eniola Bolaji sai kuma Esther Nworgu.

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Faransa na gudanar da jerin zanga-zanga a faɗin ƙasar, domin nuna adawarsu da naɗin sabon firaminsitan ƙasar, Michel Barnier, mai ra'ayin 'yan mazan jiya, bayan zaɓen da ba a kammala ba - wanda masu ra'ayin kawo sauyi suka samu kujeru masu yawa a majalisar dokokin ƙasar.
Ana sa ran gudanar da zanga-zangar a wurare fiye da 100 a faɗin ƙasar a yau Asabar, inda tuni mutane suka fantsama titunan biranen Bordeaux da Nice da kuma Le Mans.
Ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar da jam'iyyar masu ra'ayin kawo sauyi - wadda shugaba Macron ya yi watsi da 'yan takarta - ne suka kira zanga-zangar.
Mista Barnier - wanda tsohon wakilin Faransa ne a yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai - ya ce a shirye yake ya kafa gwamnatin haɗaka da 'yan siyasa daga sauran jam'iyyu ciki har da ta masu ra'ayin kawo sauyi.
Kawo yanzu ana gudanar da zanga-zanga a wurare daban-daban kusan 130 da ke wajen birnin Paris, ciki har da biranen Marseille da Lyon.

Asalin hoton, International Solidarity Movement
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gudanar da ''cikakken bincike'' kan kisan da aka yi wa wata Ba'amurkiya 'yar asalin Turkiya a Gabar Yama da kogin Jordan da aka mamaye.
Kafofin yaɗa labaran yankin sun ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun harɓe, Aysenur Ezgi Eygi, mai shekara 26 a garin Beita da ke kuda da Nablus, lokacin da take cikin zanga-zangar mako-mako da ake yi domin nuna adawa da faɗaɗa gine-ginen Yahudawa a yankin.
Rundunar sojin Isra'la ta ce tana "bincike kan rahotonni da ke cewa an kashe 'yar ƙasar waje sakamakon harbin da dakarunta suka yi a yankin".
Wani ganau a wurin ya shaida wa BBC cewa ya ji ƙarar harbi har sau biyu kan masu zanga-zangar.
Danginta sun ce wani bidiyo ya nuna ta mutu ne sakamakon harbin harsashi da wani sojan Isra'ila ya yi mata, tare da kiran Amurka ta gudanar da bincike.
Tuni dai Amurkan ta buƙaci Isra'ila ta bincike lamarin.
Kakakin majalisar tsaron Amurka, Sean Savett, ya ce ya ''kaɗu matuƙa kan mutuwar matashiyar Ba'amurkiyar''.

Asalin hoton, NNPCL/X
Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya musanta zargin da ya ce ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC ta yi masa na yi wa matatar mai ta Dangote maƙarƙashiya.
MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Dangoten sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPCL ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar.
To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Asabar, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote.
''Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta rage farashi domin samun ciniki a kasuwa'', in ji sanarwar.
Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin rafashi kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa.
Kamfanin NNPCL, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita.
''NNPCL ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPCL ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,'' in ji sanarwa.
Kamfanin ya kuma ce babu ta yadda zai yi maƙarƙashiya ga kasuwancin da ya zuba hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa

Asalin hoton, Ajuri Ngalale/Facebook
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya sanar da ajiye aikinsa 'na wucin gadi'
Cikin wata sanarwa da mista Ngelale ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a ranar Juma'a ya miƙa takarda zuwa ga shugaban ma'aikata na fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila domin sanar da shi aniyarsa ta tafiya hutun da bai san lokacin ƙarewarsa ba, don mayar da hankali kan rashin lafiyar wasu iyalansa da bai bayyana ba.
''Na yi hakan ne domin samun isasshen hutun da zai ba ni damar mayar da hankalina kan matsalolin rashin lafiya da a yanzu haka iyalaina ke fuskanta'', in ji Ngelale.
Mista Ngelale ya kuma ce ya jingine duka sauran muƙaman da yake riƙe, da suka haɗar da wakilin Shugaban ƙasa na musammman kan sauyin yanayi da kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan inganta muhalli.
''Na ɗauki wannan mataki ne bayan shafe kwanaki ina tuntuɓar iyalai da dangi kan yanayin rashin lafiya da ake fuskanta a gidanmu'', in ji shi.
Daga ƙarshe ya ce yana sa ran dawowa domin ci gaba da aikinsa, idan lokaci da rabo sun ba shi damar hakan.
Dubban masu zanga-zanga sun fantsama kan tittunan jihar Manipur da ke arewa maso gabashin Indiya.
Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki 'yan tawaye na kai musu hare-haren bam da rokoki.
Ɗalibai sanye da kayan makaranta da ƙungiyoyin mata da sauran al'umma sun fito kwai da ƙwarƙwatansu ɗauke da alluna da tutoci suna alla-wadai da waɗannan hare-hare da sukayi sanadin mutuwar mutane akalla uku a ƙasa da mako guda.
Ko a jiya Juma'a sai da aka kashe wani malamin addini, bayan harba makamin roka kan rufin gidansa.

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri ne domin gina ƙasar tare da samar mata ingantaccen ci gaba.
Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar 'yan asalin Najeriya mazauna China, a birnin Beijing, Shugaba Tinubu ya ce an ƙara farashin man fetur ne a ƙasar, domin samar wa Najeriya ingantaccen ci gaba.
''Za ku ji a 'yan kwanakin nan ana ta magana game da ƙarin kuɗin man fetur, amma magana ta gaskiya za mu iya gina ƙasarmu? Mu samu tituna masu kyau kamar yadda muka gani a nan (China), mu samu tsayayyiyar wutar lantarki da ruwan sha, kuma kun dai ga yadda makarantunsu ke da kyau a nan'', in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa ''idan muna son cimma waɗannan abubuwa sai mun ɗauki matakai masu tsauri domin samun hanyar da za ta kai mu ga ciyar da ƙasarmu gaba''.
Shugaban ƙasar ya ce ba a samun kowane irin ci gaba cikin sauƙi ko kuma a ɓagas.
“Idan kana son ka samu komai a kyauta, to zai zame maka mai wahalar samu ko ka jima ba ka same shi ba”, in ji shugaban na Najeriya.
''Kalli tituna masu kyau da inganci a nan, ina so na kwaikwayi irin waɗannan ayyuka a Najeriya, ina son gyara makarantun 'ya'yanmu, bana son ganin ɗalibanmu suna zama a azuzuwan da suka lalace, ina son gayar tsarin koyarwa'', in ji shi.
A ranar Talata ne dai babban kamfanin mai na asar NNPCL ya sanar da ƙarin kuɗin man fetur zuwa naira 855, dangane da inda mutum ke zaune a ƙasar, lamarin da ya ya janyo wa gwamnatin ƙasar suka daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane.

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Algeria na kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana a yau Asabar.
Shugaban ƙasar mai ci, Abdelmadjid Tebboune - da ke neman wa'adin mulki na biyu - ya samu karɓuwa tsakanin al'ummar ƙasar, lamarin da ke ƙara ba shi ƙwarin gwiwwa a zaɓen.
Mista Tebboune na fuskantar hamayya daga Abdelaali Hassani mai matsakaicin ra'ayi, da kuma ɗan takarar jami'iyyar socialist, Youcef Aouchiche.
Kusan 'yan ƙasar miliyan 24 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na yau
Masu sharhi sun ce 'yan takarar sun mayar da hankali a yaƙin neman zaɓensu kan matasa - waɗanda kusan su ne rabin al'ummar Algeria - da alkawarta inganta rayuwarsu da rage dogaro kan albarkatun mai.

Asalin hoton, AFP
An ayyana zaman makoki na kwanaki uku a Kenya, bayan mutuwar dalibai 17 a wata mummunar gobara a makaranta.
Shugaban ƙasat, William Ruto, ya ce za a gudanar da binciken kan yadda wannan lamari ya auku, kuma duk waɗanda aka samu da laifin sakacin aukuwar gobarar za su fuskanci shari'a.
Iyaye da dama na cikin zullumi da fargabar ko ɗaliban da ake cewa ba a gani ba akwai 'ya'yansu a ciki.
Daliban 17 suka kone kurmus - ta yadda ma ba za a iya gane su ba - a gobarar da ta tashi ranar Juma'a a makarantar da ke tsakiyar gundumar Nyeri a birnin Nairobi.
Sama da mutane 2,000 ne suka yi kokarin ceto yaran, waɗanda galibinsu suka shige karkashin gadajen kwanansu a lokacin gobarar.
'Yan sanda sun ce sai an yi amfani da gwajin ƙwayoyin halitta na DNA wajen tantace gawarwakin waɗanda suka mutu.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Asabar.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki ta fuskar labarai.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.