Lebanon ta ce wani harin jirgi maras matuƙi da Isra'ila ta kai ƙasar ya kashe mutum biyu
Ma'aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyu sun mutu bayan harin da Isra'ila ta kai da jirgi maras matuƙi a kudancin ƙasar.
Mutanen biyu dai na tuka keke a lokacin da harin ya faɗa kansu a kusa da garin Taybeh.
Sojin Isra'ila sun ce jirgin yaƙinsu sun kai hari wasu gine-gine da sukai amanna mayaƙan ƙungiyar Hezbollah da Iran ke mara wa baya na amfani da su a ƙauyen Odaisseh, kusa da iyakar ƙasashen biyu.
Shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrullah ya maida martani da cewa maƙiyan ƙungiyarsa su dakaci martanin da ya kira 'mai tsair' da za su mayar.
Ya ƙara da cewa duk wanda ya taɓa ƙungiyar to ba za su ƙyale shi ba.
Ƙungiyar Hezbollah da sojin Isra'ila, na kai wa juna hari tun bayan kisan kwamandansu da jagoran siyasar Hamas Isma'il Hanniyeh.
An rantsar da Kagame karo na huɗu a shugancin Rwanda
Asalin hoton, Getty Images
Shuagaban ƙasar Rwanda Paul Kagame ya sha rantsuwa a matsayin shugaban ƙasar karo na huɗu.
Mista Kagame ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan da ya gabata da fiye da kashi 99 cikin 100 a takarar da aka haramta wa mafiya wayan 'yan adawa tsayawa.
'Yan ƙasar na yabonsa wajen taimakawa don daidaita zaman lafiyar ƙasar, amma masu rajin kare haƙƙin bil'adama suna sukarsa kan take 'yancin ɗan'adam da taimaka wa rikicin da ake yi a gabashin Kongo.
An gudanar da bikin rantsuwar cikin shagulgula tare da harbin bindigogi domin girmamawa, a taron da mafi yawan shugabannin Afirka suka halarta.
To sai dai makusancin makwabcinsa, shugaban Kongo, Felix Tshisekedi bai halarci bikin rantsuwar ba.
Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da takun saƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, kan rikicin gabashin Kongo, inda 'yan tawayen M23 ke cin karensu babu babbaka.
Kongo dai ta jima ta zargin Rwanda ta taimaka wa 'yan tawayen, zargin da Kigalin ta sha musantawa.
Dakarun Ukraine sun kutsa cikin Rasha da nisana kilomita 30
Asalin hoton, Getty Images
Mazauna yankin Sumy da ke arewacin Ukraine, na ci gaba da ganin tankokin yaki, da makamai da motoci masu sulke na nufar hanyar yankin Kursk da ke Rasha, a rana ta shida da fara kai hare-haren da Ukraine ke yi a cikin Rasha.
Dukkan motocin an yi musu zane da launin fari, yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da gwabza faɗa.
Ma'aikatar tsaron Moscos ta ce sojin Ukraine sun yi arangama da dakarun ƙasar a nisan kilomita 30 a cikin ƙasarsu.
Rasha dai na ci gaba da jajircewa da maida martanin hare-haren makamai mazu linzami da ake kai musu a yankin Sumy.
Duka kasashen biyu na ci gaba da kwashe dubban fararen hula da ke zaune iyakokinsu.
A ɓangare guda kuma, Rasha ta fara ɗakar matakan kare cibiyar makamashi da ke Kursk ta hanyar kewaye ta, wadda ɗaya ce daga cikin manyan cibiyoyi uku da ƙasar ke da su.
Isra'ila ta rufe kafar yaɗa labaran Lebanon
Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Isra'ila ta amince da matakin rufe kafar yaɗa labaran Lebanon ta al Mayadeen a cikin Isra'ila.
Matakin na zuwa ne bayan gaggauta yi wa dokokin ƙasar gyaran fuska, da suka bai wa ƙasar damar rufe kafofin yaɗa labaran ƙasashen wajen da aka yi amanna suna cutar da tsaron ƙasar.
Lamarin na zuwa ne bayan 'yan jaridar kafar yaɗa labaran al Mayadeen suka yi zargin cewa Isra'ilar da kanta ta shirya harin roka kan tsaunukan tuddan Golan da ya kashe Isra'ilawa a watan da ya gabata.
Tun da farko dai Isra'ila ta ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Hezbolla da ke samun goyon bayan Iran.
To sai dai Ƙungiyar ta musanta zargin tare da nesanta kanta daga harin.
Shugaban Iran ya sanya sunan mace cikin ƙunshin ministocinsa
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Mata da dama sun fito a lokacin zaɓen da nufin samun sauyi a salon shugaban ƙasar
Sabon shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya ayyana mace da mutumin da ke ɗasawa da ƙasashen Yamma a cikin ƙunshin ministocin gwamnatinsa.
A ranar Lahadi ne shugaban ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar sunayen mutum 19 domin ta amince da su a amatsayin ministocin ƙasar.
Mutumin da ke ɗasawa da ƙasashen Yamman da ake ganin zai zama sabon ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi, ya yi fice wajen hulda da ƙasashen Yamma.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma yarjejeniyar nukiliya takanin Iran da ƙasashen Yamma a shekarar 2015.
Ita kuwa Farzaneh Sadegh, wadda ake ganin za ka jagoranci ma'aikatar kula da birane da titunan ƙasar, za ta zama mace ta biyu da ta taɓa riƙe muƙamin minista a ƙasar tun bayan juyin-juya halin ƙasar a shekarar 1979.
Aƙalla mutum 30 sun nutse bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto
Asalin hoton, Getty Images
Mutum guda ya mutu yayin da fiye da 30 suka nutse bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutane a kife a kogin Dundaye a ƙaramar hukumar Wamakko da ke jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi da safe, lokacin da mutanen suka shiga kwale-kwalen domin zuwa gonakinsu.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA mai lura da jahohin Sokoto da Kebbi da Zamfara,Aliyu Shehu-Kafindangiya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin, inda ya ce jami'an hukumar da gwanayen ninƙaya a ruwa na ƙoƙarin ceto sauran fasinjojin da ba a gani ba.
''Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:00 na safe, kuma mun zo da jami’anmu da kuma gwanayen nutso a ruwa domin a san yadda za a ceto waɗannan mutanen da ke cikin ruwa, yanzu dai an fiddo gawa guda kuma an wuce da shi gida domin a yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada'', in ji jami'in hukumar NEMA, Aliyu Shehu-Kafindangi.
Matuƙin kwale-kwale wanda shi kaɗai ne da ya tsira, ya shaida wa BBC cewa suna kan hanyarsu ne daga garin na Dundaye zuwa fadama domin aikin shinkafa lokacin da lamarin ya faru.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji aƙalla 20 ya kife a jihar Jigawa, lamarin da ya janyo mutuwar aƙalla mutum 15.
Hatsarin kwale-kwale a Najeriya, wani abu ne da ke neman zama babban bala'i, wanda masana ke dangantawa da rashin ingancin jiragen da kuma ƙazamin lodi da ake yi wa kwale-kwalen.
An ƙirƙiro manhajar waya domin rage kisan mutane da giwaye ke yi a India
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a jihar Assam ta kasar India sun kirkiro wata manhaja da za a rika amfani da ita ta wayar salula domin rage yadda giwayen daji ke kashe mutane.
Manhajar mai suna Haati, za ta rika aikawa da sako ne na gargadi da mutane a duk lokacin da wani garken giwaye ya tunkaro su, domin mutum ya yi sauri ya kauce daga hanyar.
Assam na daya daga cikin jihohin da suke da giwaye masu yawan gaske a India, kuma hakan ya sa ake yawan samun mace-macen mutane da giwaye saboda haduwar da suke yi.
Masu rajin kare muhalli da namun dawa, sun ce giwaye na fada sosai yanzu a jihar ta Assam saboda, muhallinsu na ta raguwa, mutane na cinye musu muhallin.
A india, mutanen da giwaye suka kashe sun kai kusan 1,701 daga 2020 zuwa 2024, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna kamar yadda jaridar Hindustan Times ta ruwaito a watan Maris.
Wata kungiya mai rajin kare muhalli da dabbobi, Aaranyak, ita ce ta kirkiro manhajar a arewa maso gabashin kasar ta India.
Manhajar tana kuma dauke da wani shafi wanda mutane da 'yan uwan wadanda giwayen suka illata ko halaka, za su iya neman diyya daga gwamnati.
Haka kuma kungiyar ta samar da wani karamin littafi a kan yin kadanga mai amfani da hasken rana wadda za ta iya kora ko hana giwaye zuwa kusa da wuri.
Kungiyar kare namun daji ta WWF, ta ce giwaye irin na yankin Asia ba su fi dubu 50 yanzu a dazuka. Haka kuma kungiyar ta yi kiyasin cewa kusan iyalai rabin miliyan a kasar ta India na fama da matsalar giwaye masu bata amfanin gona a duk shekara.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya zargi Iran da yi masa kutse
Asalin hoton, Reuters
Kwamitin yaƙin neman zaɓen tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an yi masa kutse a cikin bayanansa na cikin gida, kuma ya nuna alamun jami'an Iran ne ke yin hakan.
Shafin jaridar intanet ta Politico da ke Amurka, a jiya Asabar ya bayar da rahoton cewa an aika masa wasu takardun yaƙin neman zaɓe ciki har da takardun bincike na cikin gida da kwamitin yaƙin neman zaɓen na Trump ya yi a kan mataimakin Trump ɗin a zaɓen da za a yi, Sanatan Ohio, JD Vance.
Wani mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen ya gaya wa BBC cewa :“An samu waɗannan takardu ne ta haramtacciyar hanya daga wasu kafofi na ƙasar waje, da ke gaba da Amurka, da nufin katsa-landan a zaɓen 2024.''
Jaridar Politico ta ce ta tabbatar da sahihancin takardun. Sai dai kuma BBC ba ta tabbatar da sahihancin iƙirarin ba.
Sai dai kwamitin yaƙin neman zaɓen bai bayar da cikakken bayani ko wata sheda da ke tabbatar da takardun da aka yi satar fitar da su ba ga masu kutse na Iran ko kuma gwamnatin Iran.
Ko a lokacin zaɓen shugaban Amurka na 2020 kamfanin Microsoft ya fitar da irin wannan rahoton, da cewa masu kutse na Iran na harin yaƙin neman zaɓe na shugaban ƙasa.
Kamfanin ya ma ƙara da cewa masu kutsen na Iran sun yi haka a kai-a kai aƙalla a zaɓe uku na shugaban ƙasa a Amurka.
Haka su ma jami'an tsaron Amurka sun yi gargaɗin cewa Iran na shirin hallaka Donald Trump, to amma wannan ba shi da alaka da harin da aka kai masa a watan da ya wuce a Pennsylvania.
Kuma a ranar Talata ma'aikatar shari'a ta Amurka ta tuhumi wani ɗan Pakistan da ake zargi yana da alaƙa da Iran da shirin kashe jami'an Amurka, wanda a iya cewa har ma da shugaban ƙasar.
BBC ta tuntuɓi jami'an Iran domin jin ta bakinsu.
Kotu ta tura shugabannin zanga-zangar Katsina gidan yari wata ɗaya
Asalin hoton, Usman Rafukka
Wata kotu a jihar Katsina ta tura 7 daga cikin jagororin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar, gidan yari tsawon wata ɗaya.
Wani makusancin biyu daga cikin jagororin ya shead wa BBC cewa, a ranar Juma'a 9 ga watan Agusta 2024, rundunar 'yansanda ta jihar ta gurfanar da Kwamared Habibu Ruma da Kwamared Kabir Shehu 'Yanɗaki da kuma wasu mutum biyar a gaban kotun majistare a birnin Katsina, inda ta tuhume su da laifukan da suka haɗa da tarzoma da sata da kuma ɓarnata kayan gwamnati.
Bayan an karanta musu laifukan da ake tuhumarsu da su, ''sai kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 11 ga wata mai zuwa, Satumba, 2024 tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare mutanen bakwai a gidan kaso, zaman waƙafi.
A Najeriya an gudanar da zanga-zanga ta gama-gari daga ranar 1 ga watan Agusta, 2024 zuwa 10 ga watan na Agusta 2024, saboda matsaloli da suke addabar ƙasar, waɗanda suka haɗa da tsadar rayuwa da rashin tsaro musammana a arewacin da neman shugabanci na gari.
Sai dai yayin da zanga-zangar ta kasance cikin lumana a wasu jihohin, a wasu kuwa ta rikiɗe ta zama tarzoma inda aka riƙa sace-sace da ɓarnata kayan gwamnati da na 'yan kasuwa da ɗaiɗaikum mutane.
Tarzomar ta kuma yi sanadin kashe mutane da jikkata wasu da dama.
Ana bikin rantsar da Shugaba Kagame na Rwanda wa'adi na huɗu
Asalin hoton, EPA
A yau Lahadi ne za a rantsar da shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame a karo na huɗu, na wa'adin wasu shekara biyar.
Ya samu nasarar zaɓen da aka gudanar a watan da ya gabata da kashi 99 cikin ɗari na ƙuru'un da aka kaɗa.
Kodaya ke bai fuskanci wata hamayya mai ƙarfi ba sakamakon hana manyan jagororin hamayyar ƙasar takara.
Wakilin BBC ya ce ana yabon Kagame da samar da zaman lafiya a Rwanda tun bayan kisan ƙare-dangi na 1994.
To amma kuma ana zarginsa da take haƙƙin ƴan hamayya da kuma rura wutar rikici a maƙwabciyar ƙasar Jamhuriyar Dumokuraɗiyyar Kongo.
Za a gudanar da taron rantsuwar ne a filin wasa na Amahoro da ke babban birnin ƙasar Kigali.
An gano dukkanin gawarwaki 62 na haɗarin jirgin sama na Brazil
Asalin hoton, EPA
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Brazil ta gano dukkan gawarwakin mutanen da jirgin sama ya yi haɗari da su a kusa da birnin São Paulo, a ranar Juma'a.
Dukkan mutum sittin da biyu da ke cikin jirgin sun rasu, daga cikinsu akwai wata tawagar likitoci da ɗaliban jami'a da wasu iyalai uku da ke ƙoƙarin komawa gida daga wata ƙasa.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jirgin ya rikito daga sama zuwa ƙasa tare da kamawa da wuta.
Jirgin ya fado ne a wata unguwa da jama'a ke zaune, to amma ba wanda ya ji rauni a wajen da ya fado, sai dai jami'ai sun ce gida daya ya lalace.
Hukumomi sun ce gawarwakin - 34 na maza ne sai kuma 28 mata - kuma an kai su dakin ajiye gawarwaki na 'yansanda a birnin na São Paulo, inda za a yi kokarin gano su tare da mika su ga iyalansu.
Tuni an riga an gane gawar matukin jirgin da ta mataimakinsa.
Iyalai da 'yan uwan mutanen za su je domin taimakawa wajen gane gawarwakin.
Ana ci gaba da bincikin dalilin da ya haddasa hadarin.
Amurka ta yi Allah-wadarai da harin da Isra'ila ta kashe farar hula a Gaza
Asalin hoton, OTHERS
Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris ta yi Allah-wadai a mamadin fadar White House da kashe fararen hula a Gaza sakamakon mummunan hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a jiya Asabar.
Ms Harris, wadda ita ce kuma ƴar takarar shugabar ƙasa a Jam'iyar Democrats a zaɓen da za a yi a watan Nuwamba, ta ce wannan karon ma an sake kashe fararen hula masu yawa, ta kuma sake nanata kira da a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da sako waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.
Ta ce Isra'ila na da damar kai wa Hamas hari amman ta yi ammanar cewa yana da matuƙar muhimmaci a kiyaye rayukan fararen hula.
Mutum sama da 70 harin na Isra'ila ya kashe a ginin makarantar inda Falasɗinawa da ke gudun hijira suka fake, kamar yadda darektan wani asibiti ya gaya wa BBC.
Kakakin sojin Isra'ila ya ce, makarantar al-Taba’een da aka kai harin na zaman wata cibiya ta aikin soji ta Hamas da kungiyar Islamic Jihad, zargin da Hamas ta musanta.
Rasha na kai hare-haren ramuwar gayya Ukraine
Asalin hoton, Reuters
Rasha ta kai hare-haren jirage marasa matuƙa cikin dare a yanki biyar na Ukraine,ciki har da babban birnin ƙasar Kyiv.
Hakan na zuwa ne a rana ta shida da dakarun Ukraine din ke ci gaba da faɗaɗa sumamensu ta ƙasa a yammacin Rasha.
Zuwa yanzu babu bayanin mutanen da aka kashe ko kuma ɓarnar da hare-haren suka yi.
Wakilin BBC ya ce ana fargabar cewa Rasha za ta mayar da martanin harin bazata da Ukraine ta kai mata a yankin Kursk a cikin kwanakin nan.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya fito a karon farko ya furta cewa sojojin kasarsa na kai hare-hare a yankin Kursk da ke yammacin Rasha.
Buɗewa
Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke
kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran
sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi.
Ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan kasancewa da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.
A yi jimirin
kasancewa da mu.
Mu fara da wannan karin maganar - Duk mai aiken yaro wata rana tare za su