Wanda ake zargi da kisan Bondi ya bayyana a kotun majistare a karon farko
Mutumin da ake zargi da kai harin wurin shakatawar nan na bakin ruwa da ake kira Bondi Beach a Ostraliya Naveed Akram, ya bayyana ta hanyar bidiyo a wata kotun majistare a karon farko.
Yana fuskantar tuhume-tuhume hamsin da tara kan kisan gillar da ake zargin ya yi wa wasu Yahudawa a birnin Sydney, sama da watanni biyu da suka gabata.
Mutane 15 ne suka mutu, wasu da dama kuma sun jikkata yayin harin.
'Yan sanda sun kashe mahaifinsa Sajid Akram a lokacin wani hare harbe.
A wajen kotun, lauyansa ya ce lokaci bai yi ba da za a iya cewa wanda yake karewa zai amsa laifinsa. Za a ci gaba da sauraron karar a watan Afrilu.