Ƙungiyar likitoci ta zargi RSF da kisan kiyashi a El Fasher ta Sudan
Ƙungiyar likitoci a Sudan ta zargi mayaƙan RSF da aikata kisan kiyashi akan fararen hula a yayin da suke ci gaba da lugudan wuta a El Fasher, ɗaya daga cikin biranen dake Darfur wanda kuma basa iko da shi.
Ƙungiyar ta ce mutane 24 sun mutu a wani hari da suka kai tsakiyar wata kasuwa da ke yankin.
Babu wani tabbaci a hukumance a game da hakan, to amma ana yawan zargin mayaƙan na RSF da zafafan hare-hare a yayin da suke ƙarfafa kawanyar da suka yi wa yankin.
Fiye da shekara guda kenan mayaƙan RSF na yi wa El Fasher kawanya kuma a tsawon wannan lokaci mayaƙan na aikata laifukan yaƙi sosai a yankin.
A ƙarshen makonnan an kashe wasu mata da yara a yayin da suke ƙoƙarin barin birnin.