Mai rike da kofin nahiyar Turai, Sifaniya za ta kara da Saudiyya a gasar cin kofin duniya 2026 ranar Lahadi.
Wasa ne na bibiyu a cikin rukuni na takwas da za su kece raini a katafaren filin wasa da ke birnin Atlanta a Amurka.
Sifaniya, wadda ake kira La Roja tana kishirwar samun maki uku a wasan nan, bayan da ta kasa doke Cape Verde a karawar farko a rukunin.
Ita kuwa Saudiyya na sa ran kai wa zagayen gaba a karon farko tun bayan bajintar 1994 da ta yi a Amurka, idan ta yi kokari a fafatawar.
Dukkansu biyun suna da damar kai wa zagayen gaba daga karawar rukuni ko kuma a yi waje da su, kenan karawar nan tana da mahimmaci.
Bayan nan a kwai wasa na uku-uku a cikin rukuni da za su buga nan gaba, kenan dole kowacce tawaga ta sa kwazon da zai sa ta ci gaba da buga gasar kofin duniya da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Karawa da suka yi a baya a tsakaninsu
Wannan shi ne karo na biyu da tawagogin za su kara fuskantar juna a gasar cin kofin duniya a tsakaninsu.
Sun haɗu a gasar da Jamus ta gudanar a 2006, inda Sifaniya ta yi nasarar cin 1-0, kuma Juanito ne ya ci mata ƙwallon.
Abin da masu horarwa suka ce kafin fafatawar
"Dole ne mu gyara abubuwa da yawa. Ba wani yanayi mai tsanani muke ciki ba, amma dole ne mu yi nasara a wasan nan. Babu wata matsananciyar damuwa ko tashin hankali a tare da mu. Mun yi sa'ar samun tawaga mai fitattun ƴan wasa da suka goge sosai a fannin taka leda. Amma zan faɗi abu guda: ƴan wasanmu sun damu da halin da ake ciki tun daga wasan farko. Amma za su saka himma sosai, kuma za ku ga wani sabon salo daga gare su."
— Luis de la Fuente, kocin Spain
"Mun shirya tsaf kan fuskantar wannan wasan. Zangon farko a wasanmu na farko a cikin rukuni da Uruguay ya yi kyau, amma ban ji daɗin zango na biyu ba. Mun yi atisaye sosai kan inganta tsaron baya da raga, domin za mu fafata da tawaga mai riƙe ƙwallo sosai kuma ɗaya daga cikin mafi ƙyau a fannin taka leda a duniya, mai fitattun ƴan ƙwallo."
— Georgios Donis, kocin Saudi Arabia
Ƴan ƙwallon da ake sa ran fara wasan da su a fili
Unai Simon; Marcos Llorente, Cubarsi, Laporte, Cucurella; Rodri, Pedri; Lamine Yamal, Dani Olmo, Ferran Torres; Oyarzabal.
Al-Aqidi; Abdulhamid, Al-Tambakti, Al-Amri, kadesh; Al-Khaibari, Kanno, Al-Juwayr; Mandash, Al-Brikan, Salem Al-Dawsari
Filin wasa da ke birnin Atlanta da za a yi karawar
Filin wasa na Atlanta, wanda tsayinsa ya haura ƙafa 300, ana buɗe da kuma rufe samansa, irinsa na musamman na farko, yana da allon bidiyo mai zagayawa digiri 360, wanda shi ma irinsa na farko ne. An kuma yabawa filin a matsayin ɗaya daga cikin mafi kula da muhalli a duniya.
Ƙungiyar Atlanta United mai buga gasar ƙwallon kafar Amurka, Major League Soccer (MLS) da kuma Atlanta Falcons ta National Football League (NFL) sune suke amfani da filin a matsayin gida.
Tun bayan bude shi a shekarar 2017, filin ya karɓi baƙuncin manyan wasanni da taruka da bukukuwa da dama a Amurka, ciki har da MLS All-Star Game, wasan ƙarshe na College Football Play-off, Super Bowl LIII, FIFA Club World Cup, wasannin sada zumunta na duniya da dama, da kuma kaɗe-kaɗe daga manyan mawakan duniya.